Sashe 38
Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A idanun me kallonsa,da kuma idanun wadanda suka dauki shekaru suna rayuwa tare da ita. Tura hoton yayi cikin sirrintacciyar system dinsa,sannan ya aikashi zuwa ga sashen bincike na can qasar yayi dan gajeran bayani a qasan hoton.
★★Tsaye take cikin qawataccen lambun nata da takan wanzu a cikine a duk sanda take cikin nishadi da walwala.irin wannan. Yanayin yana taimaka mata qwarai,yana sake inganta mata nishadinta.
Tun bayan da sultane ya fita zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na agadez,zama kadan tayi taga mabuqata sannan ta kebe kanta cikin qasaitaccen lambun nata.
Tun tsakanin jiya zuwa yau din bata bawa kanta sukuni ba,shirye shirye kawai takeyi na irin uwar dukiyar da za'a narkar wajen tsarawa akhnan din komai na aure a zahiri,yayin da a badini aikin ya zame mata biyu,shirya almaz da kuma shirya dukiyar auren da take sanya ran za'a gabatar da ita bayan almaz yazo sun gana da akhnan kamar yadda al'ada ta tanadar. Lefen auren da za'a kawo da kuma yadda bikin zai kasance,wanda ta tsara gudanar da komai bayan daurin aure gudun wanzuwa ko gilmawar wata matsala,kuma ta tsara komai ya kasance a haka ne don kashe bakin tsanya.
Duk da wadannan damarmakin data samu tana jin wani susa cikin ranta idan ta tuna yadda sultane yake sake jaddadawa haisam kula da nauye nauyen da yake ganin da haisam din kawai suka dace,saidai wani sashe na zuciyarta yana bata tabbacin bai isa ya hana faruwar komai ba,bai kuma isa ya sanya komai ya faru ba. Ta gani sun kebe da sultane a gurin,sunyi maganganun da har yanzu suke gilmamata da tsananin kwadayin son jin meye da meye sultane ya gayawa haisam din a kebe?.
A yanzun da take gurin,tana waya da amintacciyarta ne dake mata siyayya da order na duka wasu kayan qyale qyalen alfarma na buqatar rayuwa,daidai lokacin data hangi tahowar yalwa da sassarfa hannunta dauke da wata takarda fara.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
[1/20, 20:09] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 34*
Idanunta akan yalwa,amma hankalinta yana kan wayar da takeyi,saidai zuwan yalwan bai hanata yin wayarta ba,har zuwa sanda ta kammala wayar da cewa.
"Ki lissafa dukka adadin da kudin ya kama,zan tura miki,a tsara komai yadda ya dace,yadda kuma zai qayatar".
"An gama ranki ya dade" Ta amsa mata cikin girmamawa sannan ta yanke wayar tana jiyeta saman doguwar takardar daje gabanta data sanya sabeera tayi list din komai.
"Ya ake ciki?" Ta tambayi yalwa tana dubanta a tsanake. Kasa magana yalwa din tayi,sai miqa mata doguwar takardar tayi tana komawa mazauninta ta zauna. Kamar ba zata karba ba,sai ta sanya hannu a qasaice ta karba,ta bude takardar tana dubawa cikin tattara hankalinta guri daya.
saidai tun batayi nisa ba hankalin nata ya dagu sosai,ta tsuke girarta tana duban jerin sabbin dokokin masarautar AGADEZ.
Tarin mamaki ne ya soma yankowa yana lullubeta,wasu irin tsare tsare da dokokin da tunda aka kafa masarautar bata taba ganin shigensu ba. A fusace ta dangwarar da takardar,ta daga idanunta cikin wani irin yanayi na fusata tana duban yalwa.
"Uban waye ya zartar da sabbin dokoki da hukunce hukunce irin wannan,ba masaniyata?,ba yarjewata?,ba kuma neman ta baki na kaman yadda aka saba?". Qasa yalwa tayi da kanta,tana iya hango kwantaccen fushi saman fuskar mammina din,wani irin wutar fushi data jima bataga kamarta ba.
"Allah ya huci zuciyarki,ya baki yawan rai.....sheikh muhammad haisam ne" Yalwa ta fadi cikin kwantar da murya.
Madaukakin mamaki da kuma fargaba ne suka hadu gaba daya suka cakude mata,tayi ciki ciki da idanunta tana duban yalwa da wani irin tsini da kaifi cikin idanunta.
"Sheikh muhammad haisam?" Ta maimaita sunan kamar yau ne rana ta farko data taba jin sunan. Kai ta girgiza sosai
"Qwarai kuwa.... Don dama a taron da aka gabatar jiya an bada sanarwar samun sabbin dokoki cikin gidan nan saboda yanayi na tsaro,da kuma qarin sabbin masu tsaron cikin gida da kuma kowacce qofa" .
Wani irin zazzafan gumi taji yana karyo mata tashin farko. Kokwanto da kuma zargi me girma yana samun sabon mazauni a ranta game dashi. Ta yaya zai halicci wani tarnaqi a daidai sanda take ganin akwai space me girma da komai zai faru ya qare kafin dawowar sultane?. Sati biyun da sultane zai fara yi a france,da wata daya da zaiyi a madeena tana ganin sun isa ta aiwatar da komai. Tana sanya ran a sanda zaya dawo ma ya samu akhnan din da tsarabar jikansa.
Wanne irin mutum ne shi da hankalinsa zaikai ga shiryawa da tsara abubuwa irin wadannan a daidai wannan lokacin?. Hannu ta sanya ta sake dauko takardar tana sake dubata daga farkonta zuwa qarshe,saidai still ta kasa samun nutsuwa jira takai ga rubutun qarshe dake qasan takardar,saboda tunaninta dake yamutsewa.
Jikin kowacce doka akwai qalubale me tarin yawa.......a jikin kowacce doka akwai tasgaro da matsaloli da zasu iya cin karo da kowanne muradi nata.
"Me kike tsoro?,me kuma kike jira da zaki zauna yaro qarami irin wannan ya fara wasa da hankalinki?.......WAYESHI?". Tambayar da tayi mata tsaiwar mashi kenan cikin tsakiyar zuciyarta,yayin da zuciyarta ta kasu sassa daban daban akan haisam.
Tun daga sanda ta fara ganinsa zuwa yau takeji wani abu na daban a kansa wanda bata taba jin irinsa akan kowanne mutum ba........wani yanayi hali da dabi'u take hanga tattare dashi da suka sha banban dana kowacce baqo dake zaune yana rayuwa cikin gidan......me yasa lokaci daya wani baqo zata dinga jinsa na daban cikin gidan?,me yasa zai samu wani irin power da koda wadanda suka shekara ashirin basu da ita?.
"Ki tura saqona izuwa sashensa......a shaida masa kome yakeyi yazo inason ganinsa!.....sannan a nemomin tamim..... Amma zan ganshi ne bayan na gama ganawa da wancan yaron"
"An gama.....cikar muradanki sune farincikinmu" Ta fada tana miqewa da dukka karsashinta don cika umarninta.
"Yalwa" Ta kirata a qasaice ba tare data kalleta ba,saita amsa mata a ladabce.
"Raina yana tsananin bace,banason in zauna jira,don banaso yazo ya ruskeni a sanda zuciyata ta fara sassauta......sa'annan daga yau zuwa wayewar garin gobe.....kowa dake cikin gidannan inaso yaji a jikinsa,yasan kuma MIJIN GIMBIYA AKHNAN zaizo don ganawa da ita,inaso ayi gagarumin shirin da ba'a taba yiwa mazajen baya ba a kanta"
"An gama......an aiwatar kamar yadda kika ce ranki ya dade" Saita juya da sassarfa tana barin shiyyar.
Idanunta ta runtse tana jin zafi a ranta,zuciyarta na cika da d'ar d'ar......gabanta na wani irin bahaguwar faduwa a duk sanda zuciyarta ta raya mata. KADA KOWANNE GIRMAN IKO YA KOMA HANNUNSA.
Duk da bata fita cikin mutane ba taba kebance a nan ita kadai,amma wani irin kunya ce take saukar mata. Tana ji kamar ma kowa ya soma fahimtar abubuwa sun fara fita daga ikonta. Abubuwa da yawa cikin tsukin nan suna fara barin da'irarta......saboda wani malami da baisan kan duniya ba ballanta girma da qarfin iko na gidan sarauta ba?.
Da qyar ta yiwa kanta saiti ta koma ta zauna tana jiran isowarsa,bataso yazo ya same ta a tsaye ballantana har ya fahimci daga mata hankali lamarin yayi,ta fesar da iska daga bakinta tana duban hanyar cike da qaguwa.
_____Tun daga nesa kana iya hangen yadda farar jubah din jikinsa ta zame masa wani irin ado me daukan hankali,hular daya sanya saman kansa ga rufe tsakiyar kanne kawai saboda laushi da santsin sumarsa.
Qafarsa daya kan daya ya dorata,hannunsa dauke da littafin fataawan nisaaa yana dubawa a hankali. Zaman ya masa dadi,duk da cewa ya zauna dinne don yayi charge din kansa da shurunsa. Ba kasafai ya fiya son hayaniya ba,yana ji tana hawan masa kaine a yawancin lokuta. Ko a yanzu abdii na zaune a gefansa,kuma tun dazun abdii din ke satar kallonsa. Yasan magana ce a bakinsa,amma shurunsa da tsumewarsa suka sanya abdii jan baki yayi gum.
Duka duka bai rufe awa daya da kammala zama tsakaninsa da wazirin sultane ba,wanda a yanzu yake a mazaunin mataimakinsa cikin fadar. Ya fahimci akwai abubuwa masu yawa,ya kuma karanci matsaloli ne masu yawa lullube da masarautar sama da katangun da masarautar ke dasu.
A nutse ya qaraso cikin girmamawa. Yaron gidansa da aka sake bashi saddam ya qaraso cikin girmamawa yana rusunawa.
"Barka da warhaka" Saddam din ya furta yana rusunawa cikin girmamawa tamkar zaikai har qasa,saidai bai qarasa kaiwa qasan ba saboda tuni haisam din ya hanasu yi masa haka.
A nutse ya sauke qafarsa daya qasa yana rufe littafin hannunsa,gami da sanya yatsa daya a tsakiya. Da kai ya amsawa sadam yana lumshe idanu gami da budesu,can cikin kansa yana jin hayaniya ta soma masa yawa. Yana shawarar qarshen satin ya wuce personal gidansa koda kwana daya ne yayi,ya gaji da yadda kwanyarsa take tattaro dukka matsalolin masarautar tana shirin dora masa,duk da yadda yake qoqarin barranta kansa da dukkan wata damuwa da ba ta aikinsa ba.
"Sarkin gida ne ya iso da saqon kira daga giwa mammina.......tana buqatar ganinka yanzu yanzu" Kadan ya zubawa saddam idanu,yayin da abdii ya saki abinda yakeyi ya zubawa saddam din idanu shima.
Har cikin rai da zuciyarsa yana mamakin yadda suke ma haisam din karan tsaye,yadda suke isar masa da umarni?,amma wani lokaci idan ya tuna HAR YANZU BASUSAN WAYESHI BA sai yaji zuciyarsa ta sassauta,ba kuma hakan yana hanashi jin haushi ba gami da jin kamar ya sanar musu waye haisam din da suke rayuwa dashi?,saidai koda yaushe idanun haisam din dama kallonsa a kansa na gargadi ne da tuna masa doka da qa'idar da yake kai.
Wani lokaci yakan cilla tunaninsa baya,yakan tuna irin girma da nauyin matsayin haisam din cikin Ethiopia,amma gashi yau cikin qasar agadez ya zabi yayi rayuwa a matsayin wani gama garin malami ba tare da kowa yasan nasa girman matsayin ba.