Sashe 74
Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kun gama aikinku kun cika wa'adinku,ina me sanar daku cewa,kowa a yanzun yana da 'yancin komawa qasarsa.....ni muhammad haisam zanci gaba da daukar nauyin aikin a wuyana da dukkan iyawata da qoqarina......dole wasan zai sauya salo,zai kuma zuwa wani YAQI na daban,bawai binciken me laifi ba.....zan sadaukar da numfashina ga qasata,zan bada rayuwata ga qasata......You're good to go
You're free to leave
All set!
You all did an amazing job,perfect score!.i owe you one!.....well done!!!" Ya furta yana daga hannunsa alamun jinjina a garesu gaba daya,wani siririn murmushi na qarfafa gwiwa a garesu gaba daya yana fita daga saman fuskarsa.
Kamar anyi ruwa an dauke haka kowa a cikinsu ya kasa magana,ya kuma kasa cewa komai,musamman omar da yakejin wani abu yana tsargawa ta cikin jininsa da zuciyarsa. Yana son ya gaya masa labarin sakin akhnan diya ga sultane wanda yayi waliccin aurenta,yana jin kamar nauyin zaiwa zuciyarsa yawa. Ya sani faduwa a wannan aikin wani abune da zai ma haisam din wahalan dauka,sai kuma gashi dukkanin alamu suna nunawa cewa BA'A BANZA AKA HAIFESHI A MATSAYIN YARIMA BA,BA'A BANZA YA FITA DAGA JINI ABBA JIFAR BA.......ba kuma a banza yake dauke da kalar wannan nauyin ba.
Baya ya basu yana fuskantar widow.......bayason ya matsantawa kowa aiki dashi......bayaso suji nauyin idanunsa suyi masa kara,baya kuma so kuma ya shiga hurumin rayuwarsu na matsa musu ci gaba da rayuwa cikin agadez. Daren jiya duka baiyi bacci ba ko sau daya,baccin da har yanzu yakejinsa cikin idanunsa,amma sai yakejin bai samu lokaci da zai kwanta ba.
Ya qarasa qarar da daren jiya ne wajen yin sallah da tarin addu'oin da suka bashi cikakkiyar nutsuwa a yau din. Ya tsaya gaban ubangijin kowa yana damqa amanar kansa da kansa a hannunsa da kuma neman jagoranci daga gareshi. Salon sirrintattun addu'oin daya saba yi a duk sanda wani abu ya cakude masa ko ya shige masa duhu,wanda kuma yake da cikakken alaqa me kyau da Allah,don ko sau daya ubangiji bai taba kunyatashi ba. Yanaji a ransa zaiyi komai da dukka numfashinsa......yana kuma jin zai fuskanci komai da sadaukarwa.
Hannunsa yaji an riqo ta baya,tun kafin ya juyo kuma yasan omar ne,sai ya tsinci omar din yana fadin.
"Ina tare dakai a dukkanin abinda ka shirya zakayi......a iya adadin kwanaki watanni ko shekarun da zaka kwashe a agadez.....har sai mun cimma nasara" Yayi maganar yana dora hannunsa saman na haisam.
Kafin haisam din yace komai abdii ya matso ya aza hannunsa saman na omari dake kan na haisam din,ya kuma sake maimaita abinda omar ya fadi. Ya daga idanunsa da sauri zaiyi magana salawi ya biyo baya,basu barshi yace komai ba har sai da dukkanin wanda ke gurin ya dora hannunsa saman nasa yana masa mubaya'a da dukkan gaskiyarsa da zuciyarsa.
Wani irin abu yaji yana ratsashi,bawai don yafi kowa ba amma Allah ya mallaka masa amincin wadannna mutane dukkaninsu lokaci guda?,sai ya rasa me zaice,ya wara hannuwansa iya yadda zai iya yana rungumesu,zuciyarsa tayi wani rauni,ya rasa da wacce kalma zai nuna girman karbar amincinsu da yayi.
*BAYAN AWA DAYA*
*SULTANE*
Tun bayan kammala wayarsa da mammina yakejin wani irin shuru cikin kansa. Tun bayan da suka gama wayar data isar da saqon da takeson isarwa yakejin komai ya dauke masa wuta. Wani abune da bai taba tunanin zai faru ba,wani abune da iya hasashensa ko lissafin rayuwarsa bai taba qiyasta zai faru ga gudan jininsa ba. SAKI irin wannan wulaqantaccen saki?. Cikin kwanaki uku kacal da daurin auren?. Da wanne idanu zai kalli duniya?,da wanne idanu zai jama'arsa?.
A yanzun da yake zaune gaban ka'aba bayan ya kammala dawafi na musamman da yayi saboda akhnan din.....ya gaza tantance laifin waye?. Laifinta ne bisa bijirewa dukkanin zabin da yayi mata wanda yake da tabbas a kansa?,laifinta ne na rashin daukan zabinsa da muhimmanci ta zabi fifita nata zabin akan nasa?. Ko Laifinsa ne?. Shin laifinsa ne daya barta da zabinta?,laifinsa ne daya kauda kai daga dukkan al'amuranta?,ya kauda kai daga zurfafa bincike akan mutumin data kawo tana so ta aura?.
Idanunsa kan dakin Allah......yayin da zuciyarsa ta cika da wani irin yaqini da kyautatawa Allah zato. Sawun mutane masu yin dawafi ya ragu sosai daga cunkusonsa na al'ada,wannan ya bashi damar ganin ka'aba sosai daga inda yake zaunen.
Idanunsa ya lumshe a hankali na tsahon wasu mintuna,yana son tuna me ya kamata yayi?,yanason tuna me ya kamata ya aiwatar. Kamar an rada masa sunan haisam ya fado a ransa,sai ya fara laluben wayarsa.
Ya tabbatar shi kadai zaiyi magana dashi yaji dadi a ransa,yana kyautata zaton baiji maganar ba tunda bayajin dadi kwana biyun shi yasa bai kirashi ba. Yanajin dadin magana dashi,yana jin nutsuwar magana da haisam sosai,wani lokaci idan yana bayyana damuwarsa a gabansa ko a tare dashi,yakanji irin yanayin nan da d'a yakeji a sanda yake magana da mahaifiyarsa.
*HAISAM*
Idanun omar a kansa sanda yake takowa inda yake zaunen. Cikin wata qaramar rumfa dake ta bayan gidan daura da wani garden dake dauke da wasu nau'ikan shuke shuke dake bada iska me kyau daya banbamta da iskar da gidan yake kadawa.
Yayi relax cikin rocking chair yana lilawa a hankali,idanunsa a lumshe suke abinda yake alamtawa omar cewa ya lula ne duniyar tunani.
Motsin da yaji ya sanyashi bude idanunsa kadan,ganin omar din kuma ya sanyashi bude idanun nasa gaba daya ya tashi ya zauna sosai cikin kujerar.
"Ina maleek ya shiga ne?". Kafada omar ya daga yana neman wajen zama.
" Tun sanda yaga zamu zauna meeting ya fita,kuma har yanzu bai dawo ba......hussam ne yaketa kirana yanaso na hadaka dashi........issue ne na company,order din daya saka daga India ta iso........sannan yace watanni uku suka rage a fidda sabon scents,suna buqatar hankalinka a wajen" Qaramin tsaki haisam din yaja yana shirin komawa cikin kujerar.
"Ka fada masa idan bazai iya handling komai ba ya zauna ya zubawa company din ido" Yana qarasa fada ya maida idanunsa ya lumshe. Murmushi omar ya saki......haisam yana wasa da kasuwancin da Allah yayi.masa wata irin daukaka dashi kansa baiyi zato ba. Yana mamakin yadda yake fifita aikin security services akan kasuwancin da kowacce rana wasu irin mahaukatan kudi suke saukewa a account dinsa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Kaf kamfanin turaruka dake duniya a yanzu ba wanda yake daukakar nasa da karbuwarsa,amma ya tattara komai ya aza akan hussam.
"Man.....yaron nan fa yana qoqari".
" Kada ma yayi.....namiji ne ai,dama kuma shi namiji ai ba'a sanshi da hutu ba....banda ragonci me ya sani?,company uku kawai amma ya kasa riqesu gaba daya sai qwaya daya?,dayanma komai sai anyi guiding nasa?" Ya fadi yana bude manyan idanunsa da suka rusuna a yau din kan fuskar omar.
Wannan kwarjinin nasu ne ya motsa,ya kuma daki omar din,sai kawai ya kauda idanunsa daga kan haisam din yana lalubar wayarsa don bawa hussam mafita. Shi kansa yasan a yanzu haisam din bazai saurareshi ba.
"Fata dai kawai idan ka kammala branch dinka dake dubai ka nemi wani ka bawa....kada ka hada masa zafi" Yayi maganan yana danna kiran hussam,daidai sanda kiran suitane ke shigowa wayar hasaim,abinda ya sanya omari tashi yana waya da hussam din ya barwa haisam gurin.
"Assalamu alaikum warahmatullah" Muryar sultane ta bayyana cikin wayar,muryar dake cike da wani irin dattako da kawaici,muryar data saukar da wani irin tausayin sultane din me nauyin gaske a zuciyar haisam.
zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (700) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
09166221261
KO
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 500*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
09166221261
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 700 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
09166221261
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
[2/5, 20:38] +234 903 555 3736: 💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 66*
"Wa'alaikumussalam warahmatullah,barka da warhaka" Haisam ya amsa masa cikin matuqar girmamawa,girmamawar data daukar da murmushi duk da tarin zafin dake ratsa zuciyar sultane din.
"Barka kade haisam,ina fatan ban shiga huruminka ba kirana kuma bai takuraka ba" Maganan saita masa nauyi,don da gaske zuwa yanzu yana yiwa sultane wani kallo na tausayi,kallo kuma na girmamawa.
"Ina fata yarona yana lafiya".
" Alhamdulillah,ina fatana kana cikin aminci da nutsuwa" Haisam din ya maida masa. Idanunsa ya lumshe,yaja wani numfashi can qasa,tambayar nutsuwarsa da haisam din yayi sai yakejin kamar ya fama masa wani tabo ne dake danqare qasan zuciyarsa.
"Ina cikin aminci,amma nutsuwa tayi nesa da zuciyata haisam". Magana sai ta yiwa haisam wani iri,fargaba kadan taso kama zuciyarsa amma ya daidaita yanayinsa.
"Ina fata kana cikin agadez?" Kai haisam ya jinjina masa kamar yana a gabansa.
"Ina nan ranka ya dade.....ina riqe da amanar al'ummarka"
"Ma sha Allah.....naji dadin hakan" Sultane ya furta a nutse,saidai qasan ransa yana jin nauyin furta maganar da alamu ke sake gaya masa haisam baisan da ita ba. Yanayin shurun sultane bai masa kama da amintaccen shuru ga wanda ya gama magana ba,wannan ya sake sanyashi tattara hankalinsa a kansa.
"Labari ya riskeni a daren nan haisam.....auren akhnan ya qare....mijin data aura kwanaki uku baya ya saketa". Da sauri ya runtse idanunsa yana jin zuciyarsa tana wani irin harbawa. Maganar ta shammaceshi ta kuma zo masa a bazata sosai. Harshensa da zuciyarsa yaji sunyi nauyi,mamaki yana sake cika kwanyarsa.
Wanne irin baqon al'amari ne wannan?,ya akayi baisan da lamarin ba a matsayinsa na waliyyinta?,shi ya kamata sultane yaji daga bakinsa bawai shi yaji daga bakin sultane ba. Wani irin nauyin sultane yaji ya saukar masa,sai yaji gaba daya kaman laifi yana laftuwa a kansa,sai yaji kamar shurun da sultane yayi yana bashi qofa ko dama na kare kansa,sai yaji kaman ya gaza da riqe wannan amanar ta wannan bangaren,sai yaji kamar ya gaza a aikin da sultane ya bashi.