Sashe 1
Luu Luu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 02///PAGE 03*
_________________________
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________
Hadimai hudu ne ke kula da bakin qofar,wasu irin tsayyayun mutane da yanayin jikinsu kawai zai gaya maka alamun qarfi me yawa a tattare dasu,suna tsaye kyam,tahowarsa kuma ya sanya biyu daga cikinsu matsawa suka buda masa qofar suna rusunar da kawunansu qasa gami da buda masa hanya sosai.
Cikin nutsuwar shin nan yayi sallama a nutse cikin tsarrarren library din. Tun a ranar farko da bincikensa ya fada ga library din yaga tsarinta ya masa,zai kuma dace da yanayin nutsatstsen karatu.
"Wa'alaikumussalam warahmatullah" Sultane dake zaune saman daya daga cikin lafiyayyun tausasan kujerun zama da aka zuba a gurin ya amsa,fuskarsa yana gauraya da murmushi.
"Maraba da sheikh muhammad" Sultane ya sake fadi yana gyara zamansa sosai,ya dubi nannie dake zaune daura dashi.
Ta jima cikin library din suna tattaunawa da sultane din,wanda duka akan abinda ya shafi auren akhnan ne. Tun daga wancan ranar daya gaya mata kada ta sake tuntubar akhnan din,sai bata sake neman nata ba,bata kuma sake magana akan komai ba. Ta sani tunda har sultane yayi magana akai akwai wani dalilin nasa. Mahaifinta ne,ya fita sanin d'iyarshi,tasan tabbas akwai dalilin da ya sanya yace kada ta sake bari maganan ya shiga tsakaninta da alkhnan.
"Ga yaro na Fatimatou" Sultane ya furta yana murmushi gami da miqa hannuwa haisam dake takowa gurin.
Murmushi nannie ta saki tana duban haisam din. Ba ranar da zama zai hadata da sultane bai bata labarin haisam ba,mamaki take kullum na yadda ya shiga ranshi haka farat daya,to amma itama a yau nata mamakin ya ragu duba daya data masa. Akwai wani irin cikakken nutsuwa da kamun kai tattare da shi,uwa uba tana hangen kwarjini me yawa a tare dashi da wani irin haske da ita kanta batasan na meye ba.
"Ba shakka,yau naga muhammad haisam" Ta fadi tana girgiza kai har yanzu idanunta a kansa sanda yake zama daura sultane din.
Cikin girmamawa suka gaisa da sultane,ya juya akalar gaisuwar tasa ga nannie wadda shekarunta suka kusa na nanay dinsa.
Cikin kulawa sa wata qaunar haisam din ta amsa masa. Godiya ta masa me yawa game da kula da karatunsu falaak da kuma amincewa ya zama mashawarci ga sultane din,sannan ta miqe.
"Bari na bawa uba da d'ansa guri ko?" Tayi maganan tan dariya gami da gyara lullubinta.
Murmushi sultane yayi,yakanji kamar duk wani matsala na rashin samun magajin d'a namiji ta yaye masa a duk sanda ya tuna da haisam,a duk sanda haisam yake gefansa.
"A fito lafiya" Ta sake fadi tana rusunawa sultane din cikin nuna girmamawar data saba gareshi tun daga quruciya kawo yanzu.
"Allah yasa" Ya amsa mata shima cikin kulawa.
Shuru gurin ya danyi bayan ficewar nannie,sai ya gyara zamansa sultane din yana matso da farantin dake cike da kayan marmari gaban haisam din.
"Allah yasa ba ayyukanka na katse maka ba......baka kwana da sanin zan nemeka ba ka tashi da hakan" Kai ya girgiza a nutse,fuskarsa adan sake ba yadda ta saba kasancewa ba.
"Ba wani damuwa a cikin hakan".
"Bismillah mana" Sultane ya fada yana masa nuni da fruit din. Baice masa komai ba,ya miqa hannu ya dauki fruit din,ya riqe a hannunsa ba tare da yaci ba.
Ya lura kaman akwai maganar da sultane din yakeso yayi dashi,amma kuma kamar tana masa nauyin fadi,wannan ya sanyashi ya gyara zamansa kadan yana fadin.
"Ina fatan ba wani matsala ko damuwa bace?". Murmushi ya kuma saki yana girgiza kai.
"Ko daya......shawara ce nake da buqatarta" Sai ya miqe ya zauna sosai.
"Gami da bayi maza da mata dake cikin gidan nan.......akwai hade haden auren da nake buqata nayi.....inason shawara kan zamansu a cikin gidan,dukkaninsu sun balaga sunkai munzali,morsa safiyya tana aiwatar da wannan tsarin ga hadiman bangarenta". Kai haisam ya jinjina,kima da darajar sultane tana qaruwa a idanunsa. Gefe guda matar daya ambata din,ya yabawa girman hasashenta da hankalinta. Mace kamar ita har tayi wannan tunanin,ta kuma dinga aiwatarwa da dukka qwarin gwiwarta da qoqarinta?. Sunan nata sai ya maida tunaninsa baya,kamar dai itace wadda ta sanya oustaze Ousmane kawoshi a madadinsa......sannan kamar itace mace ta biyu a gurin sultane din indai bai manta ba,indai kuma lissafinsa ya bashi daidai.
Tunaninsa da fatansa dukka masu kyau ne,yana da tsananin hangen nasa da kuma qoqarin kare haqqin musulunci,sai ya maida apple din inda ya daukota ya hade tafukan hannunsa guri guda.
"Akwai tarin kuskure da sabawa addini akan ajiye bayi ko hadimai ko 'yan aiki maza da mata cikin gida ba tare da aurar dasu ba ko kuma duba buqatunsu na dan adam ba.......akwai tarin tuhumar cikar nagartar dukkan wanda ya aikata wannan....." Kai sosai sultane ya girgiza cikin gamsuwa.
"Abu mafi kyau shine......a basu dama kowa ya zabi wanda yakeso,a kuma aurar dasu kaman yadda musulunci ya tanada"
"In sha Allah" Sultane ya fadi yana jinjina kai,zuciyarsa girman haisam da qaunarsa suna sake samun gurin zama.
Yana yiwa mutanensa da yawa kwarjini,kwarjinin da ya sanya malaman dake tare dashi ba kowanne lokaci suke bashi shawarar da zata dace da shinda ya kamata ayi ba. Yafi buqatar jin gaskiya a bakunansu fiye da su gaya masa abinda rai da zuciyarsa sukeson ji,amma ba kasafai suke iyayin hakan ba,saidai ya hango wannan qualities din tattare da haisam din.
Shuru ya sake wanzuwa a tsakani,har yanzu haisam yana ganin akwai wani magana ta daban da sultane yakeso yayi cikin idanu da bakinsa......sai ya sauke idanunsa yana maidawa ga littattafan dake gefansa cikin nazarin wadanne iri ne.
★A hankali ta hadiye tea na qarshe data kurba,ta kuma dire cup din saman table din tana jin yadda wata kasala da mutuwar jiki take saukar mata lokaci guda. Idonta ta lumshe sannan ta budesu lokaci guda,a hankali ta dafa table din ta miqe ta fara sauka daga gurin tana jin yadda kasalar take bin jikinta.
Ta alaqanta hakan da yunwar data tarawa cikinta na kwana da kwanaki,yanzun kuma ruwan zafin da tasha ne qila yake sauka a jikinta yana sake mata gabobinta. Wayar hannunta ta daga tana duban lokaci,bata manta ba mammina nason ganinta,kuma kiran mammina din abune me matuqar muhimmanci a gareta. Tana buqatar taje,don tana neman duk wani hanya da dabara da zai sanya sultane ya janye daga qudurinsa,banda haka a yanayin kasalar da takeji ba abinda take buqata irin ta koma samanta ta kwanta ta huta,ta kuma qara bacci,ta tabbatar awa daya zuwa biyu zata tashi fresh.
Saman takeso ta koma,amma sai taji ba zata iya hawa stairs din ba,don haka ta matsa na'urar dake kusa da ita,ba jimawa birra ta qaraso a gaggauce.
"Zan fita gurin mammina.......shiga ki samomin abu mafi kusa dake da zan lullube kaina" Ta qarasa maganan a kasalance. Cikin girmamawa ta amsa ta kuma haura saman da azama,ba jimawa ta sauko da wata Riga.
Gabanta a hude yake,tana zubi da alkyabba don hade take da hular da zaka saye kanka dama fuskarta gaba daya,tana da dogon hannu bata da nauyi kwata kwata,saidai ita tsahonta gaba dayanshi bai qarasa har qasa ba.
Baya kawai ta juyawa birra din,ita kuma ta qaraso cikin girmamawa da kulawa ta zira mata,akhnan din ta sanya hannu ta rufa hular a kanta sannna ta fara tattaki don ficewa daga sassan.
"Zan iya yi miki rakiya?" Birra ya fada tana sadda kanta qasa,kai kawai akhnan din ta kada mata alamun bata buqata sannan taci gaba da takawa tana ficewa.
Iska sosai ta zuqa sanda ta fara takawa a farfajiyar da zata zame mata kamar ragin hanya,yadda zata bulle sassan mammina ta hanyar mahadar data hada library din sultane da kuma shiyyar mammina din.
Tanason hanyar,saboda tafiya a hanyar yana tuna mata abubuwa masu yawan gaske,tafiya a hanyar yana tuna mata rayuwarta a France,lokacin karatunta da wasu lokuta takejin kewar da takan sanyata siyan ticket ta koma qasan tasha iska na satittika sannan ta dawo. Hanya ce da ba wani zirga zirgar mutane,duk wanda ka gani a area din amitacce ne,sannan kuma akwai abinda ya kaishi ta gurin. Library din sultane ne kawai a gurin,sai dakunan ajiyar kayayyaki na musamman na sultane mammina da morsa safiyya,sai akayi masa gurin hutawa kebantaccce,da kuma hanyoyin da zasu iya sadashi da hanyar da zata bulla dashi sassan kowacce cikin matan nasa.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
A hankali take takawa da salon tafiyar nan tana me matuqar jan hankali,saidai a yau din tafiyar ta kasance da wani irin yauqi saboda kasalar dake ci gaba da saukar mata,har tana jin kamar qafafunta ma sundan fara nauyi,hakanan wayar hannunta taji dama ta barta a sassanta bata fito da ita ba. Ba kowa kuma ta gurin ballantana ta bashi wayar ya maida mata,hakanan dai tayi ta maza taci gaba da riqon wayar a hannunta tana kuma ratsa guri..
"Idan ba damuwa ina iya tafiya?" Haisam ya buqata yana duban sultane cikin girmamawa,ganin bai sake cewa komai ba,ga kuma saqon da abdii ya aiko masa kan maher yana jiransa.
Murmushi ya saki yana jinjina kai.
"Kana iya tafiyarka muhammad,ina fatan kuma ba zaka gajiya ba a duk sanda na sake kiranka".
"In sha Allah" Ya amsa masa a nutse sannan ya miqe,cikin girmamawa sultane shima ya miqe,a jikinsa yakejin haisam din abun girmamawa ne.
"Na gode qwarai da gaske da sadaukarmin da lokacinka da kayi" Sultane ya fadi. Sosai haisam yakejin godiyar sultane din tayi girma a gareshi,saidai kuma baice komai ba ya fara takawa sultane din yana masa tattaki har bakin library din.
A nutse yasa hannu ya sauke yankin daya lullube bakinsa zuwa hancinsa yana sheqar iska sosai yana aikata hunhunsa gami da ci gaba da takwa da qasaitaccen takun nan nashi. Har yanzu idanunsa na hango masa magana kwance a idanun sultane......to wacce magana ce?,wacce damuwa ce haka data masa nauyin daya gaza fadi.
Bai kammala aje zaren wannan tunanin ba yaji kamar an wafci hankalinsa da kalaman.