← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 95

Sashe 94

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Hajiyar Bana Hajiya Aminene Mamman sanye da hak'orin Makkanta, duk duniya bata da Kamar Zaidu Bawan Allah tunda ya kai ta dakin Allah, tunda ya biya mata kudin Makka taje ta sauke farali k'ima da darajarsa suka k'aru a idinta, Addua kawai take mishi don Zaid Alheri Ne, ta dage sai kassafa tsarabarta takeyi a gida, Akwatin kayan yara ta ma Hafiz da Aishatu diyar Aneesa, Sai kuma Akwatin dan cikin Seebi wanda Haihuwa ko yau ko gobe, sai zuwa sannu da zuwa ake mata.
Mami tace da Zaid "Kasan Maganar ka kadai takeji, ka shiga ka mata bayani zatafi Amincewa, Murmushi kawai yayi ya shiga Dakin Nene, tana ganinshi tace " yauwa Zaidu bawan Allah, ga Akwatin Hafizu, da Aishatu, in zaka wuce sai ka tai musu dashi" yace "toh sun gode" ya zauna kan Gado, tace "Ya akayi Zaidu Bawan Allah? Fadin bukatar ka komicece zan maka ita in befi karfina ba" ya ji dadi sosai yace"Nene kinsan Seebi ta kusa Haihuwa, kuka ba halin dawowa Nan sabida ta kusa fara Jarabawar ta, shine nake so ko kije ki zauna da ita har ta haihu bayan Jarabawan sai ku dawo tare" Nene tace "Haba Zaidu dama wannan maganar ce sai kayi 'yar murya? Seebi tace fa, in ban kula da ita ba wa zai kula da ita, wannan Solobiyon in banda kiranta da 'yar tsana(doll baby) ba abunda ya iya, dole ni zanje? Yaushe tafiyar?" Zaid ya ji dadi Sosai yace "nan da yan kwanaki ne an gama komai". To wa zai kaini? Kai ko Aishatun?" yace "Ko daya, ke kadai zaki, mik'aki kawai zanyi ni" ta zaro ido tace "kai Zaidu Bawan Allah, in ka ganni lahira to kaini akayi, ta ya zan tafi K'asar Yahudawa ni kadai? Salan a saceni ko ai man Illah, ba dani ba sa Lallen Kaza" Zaid yayi Murmushi yace "Nene, ba wanj abu bane ba fa, kamar yanda kikayi tafiyar ki Saudi ke kadai, banbancin wannan Jirgi kawai zaki chanza, zan tura ma Rafeeq lokacin da Jirginku zai isa, kafin nan zaije ya jiraki, da kin fito zaa ki ganshi, an samu cigaba yanzu ko yaro dan shekara 5 sai ka turashi shi kadai, tayi daria tace "balleni 'yar Shekaru Saba'in ba biyu (68) sukayi daria, haka Nene ke yarda da zancen Zaid, ta dauki zancen Zaid kamar yankan Wuk'a, sai dai in beyi magana ba, nan da nan zata yarda. Nan ya cigaba da wayar mata da kai kan tafiyar.

BAYAN WASU KWANAKI
LEEDS BRADFORD AIRPORT.
A gajiye take tafiya tana jan Akwatin ta, in ka ganta da wuya ka shaida Nene, ta Waye ta kile ta kara kyau, daga Nesa ta hangoshi washe hak'ora tayi ta kwala mai Kira "Dunkum" muryarta yaji a Sama, ya tabe baki "Here Comes My Headache"Ba ta bar shiru ba ba ta fasa kiran 'Dunkum' ba, Niyyar shi ya shareta amma da ya tuna Gargadin da Uncle Zaid ya dade ya na mai kan Nene, sai ya k'akalo Murmushi ya matso kusa da ita, ya karbi Akwatin hannun ta, bakin Nene kamar gonar Auduga, ya bude baki da k'yar yace "Sannu fa" ai fa ya tabota, "Kai Dunkum ka fita idona, in ci uban tafiar nan ni kadai in sha wahalar nan ka kallan kace min Sannu fa? Sannu fa?" ganin in ya biye mata zasu saida hali, shiru yayi ya ja Akwatin yayi gaba, binshi tayi tana Mita "Ka daiji haushi Wallahi, Dunkum kawai, Dunkum Dunkum, kana Girma kana cin K'asa, kana niyyar Zama Uba baka daina Dunkumcin ba, Dunkuk dangin tsaka, tsukakke" chak ya tsaya, Murmushi tayi na cin Nasara, burin ta kenan idan Feeq ya nuna mata be son abu tayi ta tsokanan shi, juyowa yayi a hankali da Niyyar yi mata magana amma sai ya fasa Securities din bayanta ya yafito fa hannu, da sauri suka k'arasa gunsu, Rafeeq ya fara magana ya na nuna Nene da hannun "Hello Officers, i need help from you, this is my Grandma, she's exhausted from her Journey, and shes having difficulty in Walking, you know how Annoying Old People can be, she wont let me Carry her or help her, i want you both to take her to My Car Over there, and Whatever happens you must'nt let go, keep hold of her" kai suka gyada mai Alamun sun gane, cikin Nene ya bada k'ululu da ta ga Masu Jan fatar nan sun kusanto ta, a hankali ta fara Ja da Baya, "Kai Dunkum Uban me zasu min? Uban me kace sumin? Eyi, Nene ba ta ankara ba sai ji tayi su chafkota kamar wacce tayi sata, Gabanta ya fadi da ta kalli mutanen nan sanye suke da Glass a ido so tashin hankalin da ta shiga ya hanata gane Yananyinsu, amma a zahirin gaskia Murmushi suke mata, Janta suka fara yi Feeq na ganin haka ya ja trolly dinta yayi Gaba, shikenan Feeq ya saida ta ga Nasaran nan masu jar fata mara Imani, Daga zuwanta, Shiyasa tace da Ziadu ba zata zo ba, Ashe Ajalinta ta biyo har Ingila, idon nene ya kawo ruwa, duk yanda taso hana hawayen fitowa sai da suka fito, don ta tsorata Ainun, Nene ta kwala mai Kira, "Dunkum, DonAllah kayi hakuri kar ka barni da Jar fatar nan, Dunkum ka taimaka, na tuba Wallahi, ba zan k'ara ba" banza yayi da ita ya cigaba da tafiar sa, ganin ba wanda ya damu da su, kowa harkar gaban shi yakeyi, kuma ba wanda yyi yunkurin taimakon ta, da taga dai tafiyar zaiyi ya barta da marasa Imanin nan tayi saurin cewa "Rafeeq Habib Lema, ka yi hakuri Na tuba, donDarajan Allah kayi Hakuri, na daina takura maka na bar kiranka da dangin tsaka, sunan ka Rafeeq dan Alhaji Lema" chak ya tsaya yana wani shegen Murmushi, takowa yayi har gabanta yace "Ya Sunana?" da sauri tace "Rafeeq Habibu Lema" ya sake Murmushi yace "ba Dunkum ba?" ta gyada kai tace "Ba dunkum ba, nice ma dunkumar" Yayi mugun Murmushi, duk ta tsure ta fita hayyacinta kamar ba Nenensa ba be takura mai idan ya nuna be son abu, ya kalli Securities din yace "Officers, I'll take it from here" suka saki Nene suna daga mata hannu wai byebye, da sauri ta k'arasa gun Feeq tana cewa "Mugaye Allah tsine muku" Feeq ya daure fuska yace "Me kikace?" da sauri tace "bance komai ba" yanda ta yi ne duk ya sashi daria, Har suka shiga mota Nene ba ta daina sauke Ajiyar Zuciya ba, Rafeeq ya kira Uncle Zaid yace ta iso har ya bata suka gaisa, ya tsareta da idanuwa, ta kasa gaya ma Uncle Zaid Rafeeq yayi Niyyar saidata, ko da ya tambayi ya yaji muryarta haka sai cewa tayi "Gajiya ce" haka suka iso gida.
Seebi ta fito daga daki tana murna ga Nene ga Nene, gannin Seebi ya gusar mata da ko wane bacin rai da ke tattare da ita, suka rungume Juna, cikin Seebi ya mata kyau, Nene ta fara mata Fadar saka matsatun kaya ga Ciki, Rafeeq ya hade rai yace "Neh-neh, ki daina daga mata murya" da sauri Nene tace "Dama Rafeeq ba daga mata murya nayi ba, kasan matsatin kaya na takura ma Babyn da ke ciki shiyasa na ke cewa ta bar sawa" Yanda take magana ya sa Seebi gano wani abu, Rafeeq yace "Baby muje ki chanza kayan kinji?" kallom tuhuma ta bishi dashi ya dauke kai yana Murmushi ta mai kallon zamu hadu, Murya na rawa Nene tace "Rafeeq dama ince ina dakin da zan sauka?" a takaice yace "ki jira sai mun fito" da sauri tace "a fito lafiya" daria ta bashi sosai ya ja hannun Seebi sukayi daki. "Baby" Seebi ta kirashi, "Naam baby" ya amsa ba tare da ya kalleta ba, tace "kalleni nan, why is Nene nice to you? Why is she Suddenly calling You by your Name not by Dunkum? And why is she polite to you" Rafeeq yana daria yace "Baby i'm suprised to, but its a good thing she's changed" tsareshi da ido tayi yace "Fine, i did what i should have done a long time ago" Seebi tace "what is that?" "I settled her Ish" Seebi tace me kamata? Tiryen tiryen ya kwashe abun da ya faru a Airport ya gaya mata ya kare yana daria itama Abun ya bata daria sosai, ta kaimai dukkan wasa tace "Haba baby its not funny, not even in the history naji ance Nene ta tsorata da wani abu, koa Aljani baya ba Nene tsoro, amma gashi ka tsorata ta, baiwar Allah shiyasa ta tsani Turanci da Turawa" Rafeeq ya fashe da daria yace "Ai na kara sawa ta tsani Turawan, but its a good thing i did, coz my son wont grow up to hear his Great GrandMa calling His Dad Dunkum or Whatever" sosai Seebi ke daria, yace "Enough, zo in cire miki rigar muje mu lallasheta don naga ta tsorata dani".
Sati Biyu Bayan Zuwan Nene Seebi ta santalo Danta Namiji, Haihuwar da Allah ya kawo mata shi a Sauk'ak'e, Farinciki Gun Rafeeq ba a magana, ya Rungume danshi yace " Welcome to The World ZAID RAFEEQ LEMA, i love you with all my Heart" Nene bata taba ganin Farincikinshi a baiyane kamar yau ba, a gaban ta da Drs ya ke ta rungume Seebi yana kissing dinta, yana mata Godia, Nene ba daman tankawa don ya mata hankali sai dai ta kallesu ta tabe baki, ko irin kawaicin nan va suyi na diyan fari" haka aka Sallamota Asibiti, har dan Aikin ya daina zuwa, kullum yana Manne da Seebi da Yaronta, be taba jin son yara irin haka ba, ba yanda Nene zatayi illa ta sa mai ido, don abun ya fara isarta, komai zaa musu a gabanshi, ya dinga wannan abu kamar kanshi farau gun Samun Haihuwa, sai tayi tsaki don kar ya jita.
Zaune suke gabaki daya har Nene a Parlor, suna Video Call ta System din Feeq da Uncle Zaid, Rafeeq ya kanga mai fuskar Baby, Zaid da Aunty Zee sukace "MashaAllah, Rafeeq ka sa na tuna randa aka haifeka, you look just like him" Feeq yayi Murmushi yace "Zaid Rafeeq lema, open your eyes and see your Grandpa, Your Dad's Hero, your Dad's Saviour, Your Dad's Favourite, Your Dad's Best" Farinciki ya maimaye Uncle Zaid, bakinshi ya k'i rufuwa, don dai ya tabbatar da abun da kunnenshi yaji sai yace "What did you just called him?" Rafeeq yayi Murmushi yace "Zaid Rafeeq Lema" ya kalli Aunty Zee yace "Ga Miji nayi miki" tayi daria tace "Aikam nagode dama wannan ya tsufa ga sabon Jini" sukayi daria Hafiz ya lek'o yana ta cewa "Baby baby" duk sukayi daria. Nene tace "Zaidu Bawan Allah yaushe zaku zo?kace da ta haihu xaku zo?" yace "Eh Nene, zamuzo ranar Laraba dukkanmu Har su Yaya da Abbii, Mahmud kuma sai Jumaa shi da Iyalinshi InshaAllah" Rafeeq yace "Meye Laraba?" duk yanda ta so tayi shiru ta kasa, tace "Kai Rafeeq, ka fita idona, Kar kaga kwana biyu na sa maka ido ka dinga min wasu kamkamba da iyayi, ba fa tsoronka nike ba, don Tsiya Laraban ne baka sani ba? To bature yaci buraubashi" daria sukeyi sosai, yace "dagaske bansan meye Laraba ba" ganin iyakar gaskiar shi Yake fadi, Seebi tace "Wednessday ne Laraba baby" yace "yauwa Baby you the best, Uncle Zaid bari na baka short story, nan ya basu labarin yanda sukayi da Nene a Airport aiko suka fashe da daria, Nene ta ja kunnenshi ya tashi da sauri ta bi Rafeeq da throw pillow suna Zagaye parlorn tace " ni za kayi wa Bariki da turanci? Ashe ba saida ni kayi ba kasa na daga hankali na? Ya Rungumeta yace "ya zanyi in saida uwargida na, kinsan ina sonki Sosai" itama Rungume shi tayi tace "I lobiyu too" duk sukayi daria, tace "Zaidu BawanAllah idan ka gama murnan Takwaran da aka ma, kaje ka biya min Makarantar Yaki da Jahilci, da na dawo Turanci zan fara zuwa in koya, saboda kar Baban Zaid ya sake min irin haka" gabaki daya suka sa Daria.
Chapter 94 · 0% Book details