← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 95

Sashe 2

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba tare da ya kanga wayan a kunnesa ba yace "Hello Assalam Ailaikum" wata Zazzakar murya su Ushee sukaji ta cikin speakers ba cewa "Hello Uncle Zaid kanajina?" Yayi murmushi yace "Ohh Meema, so nawa zan miki maganar amsa sallama? Oh sorry Waalaikum Salam, Uncle Zaid baka iso bane har yanzu? Meema ina cikin katsina, but sai naje masauki, idan na huta zuwa anjima ko da safe sai na zo gidan ko? A shagwabe tace "haba mana Uncle Zaid, You promised to come see us immediately you arrived" Ya sauke ajiyar zuciya, yace "toh bani 30mins zan karaso InshaAllah" tayi dariar murna, yay Uncle Zee Thanks, u d best" yace "erhm, Rafeek na gida?" tace "No be dawo ba ko" ya danyi shiru yace "toh sai na iso" kafin tace wani abu ya latse wayar.

Ushee ta kalli Seebi, sukayi murmushi, matuk'a wanda aka kira da Uncle Zaid ya burgesu, daga jin wanda su kayi waya da ita sun san yar gata ce, don yanda take shagwaba da magana, a hankali ushee ta rada ma Seebi 'kila diyar yayar sa ce' seebi gyada kai tayi.

Zaid ya dago wayarsa, ya dan rage gudu, ya shiga neman layin nephew dinshi, callertune din yazo karshe ba amsa, ya sake redialling, yanzun ma kamar ba za'a dauka ba, a ka dauka ba tare da ance komai ba, Zaid yayi gyaran murya, yace "Rafeek" chan kasa sukaji ance "Barka da yamma" Zaid yace "lafia lao, Kana ina?" kamar bazai tanka ba, yace "Gani nan Maalesh zai saukeni gida" yace"Okay toh, ku je ku min booking Liyafa hotel" Ok kadai yace ya kashe wayar, Zaid ya murmusa a baiyane yace "Rafeek ikon Allah"..

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg4⃣

Uncle Zaid ya tako har gaban shi ya, yace "kana da matsalan wani abu? Do u need anything?" girgiza kai rafeek yayi, yace No, nothing, Zaid yace "nawa aka kama min daki? Rafeek yace "na riga na bada" kayan abincin ka fada kudi? Rafeek yace "akwai saura" karatu fa? A takiace yace "Lafiya " Zaid yayi daria yace "baka tambayi Mami ba" Rafeek ya dago jajjayen idon sa ya kalli kawun shi, Zaid ya fara daria don ya san ya kure hakurin shi, tunda har ya sa shi magana haka, yace to "ka tafi ko?" kamar jira yake ya fara tafia part dinshi, Zaid ya juya gun maalesh, Mahmud ya abokin na ka? Maalesh yace "Uncle Zaid, akwai improvement, don yanzu yana zuwa lectures, daga chan muke wai yayi lectures 4-6", Zaid ya kalleshi yace "good, kai yaushe kake gama service din? Maalesh yace"karshen wata" Zaid yace yayi "kyau copper, ka kawo min CV dinka kafin na bar katsina" Maalesh yace nagode Uncle Zaid.

Kamar daga sama yaji muryan Rafeek nace wa "erhm, nace ba?" Zaid da Maalesh suka kallo shi, Zaid yace "naam, kace mene?" Rafeek ya danyi guntun tsaki yace " kace ma wannan yarinyar ta daina shiga harkata, ta daina kula ni" tsaf Zaid ya gane yarinyar da ya ke magana, amma sai yace "wace yarinya kenan?" Rafeek ya bata rai yace "Aneesa" Zaid ya dan murmusa, yace "haba Rafeek, ya zaayi ta daina kula ka? Ai ko ba komai zumunci ya hada ku, ba wani abu bane don ta kula ka, besides ai kanwar ka ce, duk da ba a saba ganin fuskar shi da murmushi ba, amma kallo daya zaka mishi yanzu kasan ranshi ya baci, ya daure fuskar nan tamau, zuciyar sa na tafarfa sa, da karfi yace " she's not my Sister, she's Nothing like my sister" Maalesh ya tsorata da yanayin abokin sa, don ya dade be ji ya daga murya haka ba, kuma uncle Zaid ya ke ma ihun nan? Kai Rafeek be cikin hayyacin sa"

Rafeek ya runtse ido gam, Zaid ko sai daga baya yayi da na sanin cewa Aneesa kanwar Rafeek ce, tunda ya ga haka, ya san ran shi ya baci, kwata kwata be son ganin tillon dan yayan shi a damuwa.Rafeek ya bude ido a hankali ya sauke su fes kan Zaid, dan gajeren tsaki yayi yace "I am sorry" Zaid yayi murmushi yace "je ka kwanta Rafeek" Maalesh kai ma ka wuce gida Allah ya bamu Alheri" ya fada motarsa, Maalesh ya shiga motarshi ya tada, a ka bar rafeek tsaye yana kallonsu, maigadi ya bude gate Maalesh ya fara fita, daidai Rafeek uncle Zaid ya tsaya, yayi winning glass ya miko mishi takarddun Kilishi guda 2, yace a hanyar K'ank'ara na siya " Rafeek ya amsa yayi murmushi da gefen bakin sa, Zaid yace "Baka tambayi Ayman ba" Rafeek ya dan gajeren murmushi, yace "she's fine, she is always" Zaid ya jinjina kai yace "Good night Son" Rafeek ya daga mai hannu ya wuce.

Nasiba, yau ba darasi ne zaki tashi ko sai kin makara? Nene, na gama makara wallahi, amm dai shiryawa nakeyi, na kusa gamawa, Nene tace" kin san nafi kowa son karatun nan, so nake naga kin zama dapta" Seebi tayi daria, tace"Nene Doctor ake cewa, kuma ai Nene ai ba karatun da nakeyi ba kenan" Nene tace "ke dalla rabani, duk daya ne, tunda ance zaki iya aikin asibiti da karatun,dama ni buri na in ga yar jikalle na aikin asibiti, idan naje ba ruwana da bin layi" Nasiba ta fito tana daria, tace "Oh Nene akwai abin daria, nikam bari in tafi don na san nayi latti." Nene tace "ga kalacin ki chan, yanzu na siyo miki kosai, ga koko na dama miki" tace Wallahi na tsaya kalaci latti zanyi, ushee na chan National ta na jirana, idan naje makaranta zan siya, Nene ba ta ji dadi ba, amma ba yanda zatayi, ta ciro #200 a hab'ar zaninta tace "gashi kin kara" Nasiba ta rungume kakarta, tace "nagode Nene sai nadawo" har waje ta rako Seebi ta na mata addua.

Ya shigo gidan Cikin shiga k'ananun kaya, yayi kyau matuka, a parlo ya zauna yana neman layin Rafeek, ringing na 3 ya dauka "Barka da Safiyya" Zaid yace "Rafeek, ka tashi lafiya?" eh kawai yace, ka tafi school din ne? Rafeek yace "Eh, ina da lectures ne yanzu" Zaid yaji dadi sosai, yace "ni gani nan zan wuce Abuja, sai na dawo kaduna, ko na biyo ta makarantar muyi bankwana?, Rafeek ya girgiza kai yace ba sai kazo ba, Allah ya tsare hanya, ina gaida Ayman dina" Zaid yace "Ayman dinka zataji, amma ita kadai? Rafeek yayi saurin cewa "Safe journey" tare da latse wayan.

Aneesa ce ta saukko taga Uncle Zaid zaune, bude murya tayi tace "Aunty Meema, ga Uncle Zaid" ta karasa gunshi "good Morning Uncle Zaid, Zaid yayi dan murmushi yace "Aneesa kin tashi lafia? Lafiya lao Uncle Zaid ba dai yau zaka tafi ba? Yace yanzu kuwa "yaya ya tashi ko?" Eh ya tashi, Uncle Zaid, ina da matsala" Ya dan kallota na me fa?, ta gyara Zama "Uncle Zaid, Yaya Rafeek ne, ba ya son in rabe shi, kullum da ya gannin kamar ya ga mutuwar shi, rannan har mari na yayi don na je dakin shi" ta karashe maganar ta tana kwalla, Zaid ya sauke numfashi, shi ma besan ta inda zai bullo ma lamarin Rafeek ba, kullum sai fadin rai, ya kasa manta abunda ya faru a baya, ya kasa cigaba da rayuwar sa kamar yanda wasu ke cigaba da rayuwar su idan wata k'addara ta fado musu. Ya daure yace " kiyi hakuri Anee, kinsan halin Rafeek, Miskili ne, ki daina shige mishi, kar wata rana ya illata ki, ki yi hakuri, ki taya shi da addua Allah ya shirya shi, da ina da ikon chanza shi da na chanza shi, amma Addua kadai yake bukata. Da sauri Aneesa tace Uncle Zaid wallahi zan iya chanza, ina son shi, zan iya zama da shi ta ko wanne hali, ku aura mishi ni, ni ce ALHERINSA.

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg3⃣

Zaid ya kallo Miemee yace"Ina kukayi?" mimi ta yi far da ido tace"dukkanin mu unguwanni daban muke, ka ajiye mu a National, sai mu hau keke napep" yace "Junction din bus? No, kubari na sauke ko wacce a unguwar su" mimi ta yi murmusi mai sauti tace "ji fa nayi ana jiranka" yace kar ku damu, ya kalli mudubi daidai saitin Seebi, yace Malama wani unguwa kuke? Seebi baki ya fara rawa ta kasa magana, da sauri ushee tace mu muna ta Wurin Gidan Masari, Miemee kuma na GRA wurin motel. Zaid ya jinjina kai yace wace Miemee? Miemee na murmushi tace "nice nan" ya sake kallon madubi yace kece wa? Ushee tace nice Ushee, wannan kuma Seebi, Zaid yayi murmushin da ke kara ma fuskar sa annuri, yace "inyee!, sunan yan gayu ne daku, Miemee, Ushee da Seebi" sukayi daria duka, yace toh bari mu fara sauke Miemee, ku ta unguwarku nayi.

Da taimakon Miemee na nuna mai hanya Zaid ya iso har kofar Gidansu, yayi parking, miemee ta sadakar zaid zai tambayi numbern ta, sai wannan yanga takeyi, amma shiru takeji, a ranta tace kila zai tambayi su Ushee, ta bude murfin kofar tace "Thanks So much Uncle Zaid" ya yi murmushi yace bakomai, ta juya ta kalli kawayenta tace "toh kar dai a manta a fito da wuri gobe don muna da GSP karfe takwas (8:00)" Ushee tace "InshaAllah" Seebi tace "ki gaida Mummy" Miemee tace "Zataji, dayanku ya dawo gaba" Ushee ta bude murfin motar ta koma gaba. Mimi ta daga ma Zaid hannu, Ya ja motar ya bar layin ita kuma ta shige gida.

Shiru ba wanda ke magana, sai da yazo unguwar yace ta wurin ina kuke? Ushee tace "ka ajiye mu a wurin Makarantar Salamah" ba wanda ya sake magana har suka zo daf da makarantar Salamah, yayi parking, Ushee tace mungode sosai, Seebi ta bude murfin motar, tace"Jazakallahu khair" Allah ya biyaka yanda ka taimake mu" da sauri ya waigo don yaji dadin adduar nan, duk da be samu ya ga fuskar yarinyar sosai ba yace "Amin Nagode" Suka rufe kofar ya ja motar sa yayi cikin unguwan, Ushee tace toh Seebi sai da safe, Allah ya kaimu Ushee, ko wa tayi hanyar Gidansu.
Chapter 2 · 0% Book details