← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 95

Sashe 42

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da k'yar ya kunna mota, saboda jikin sa ya mace gabaki daya, ji yayi ya kasa tafiya, guntun tsaki ya sake ya duba Aljihun motar shi ya ciro paper da biro, rubutu yayi sannan ya fita ya shiga Asibitin, daidai Dakin ya chokara a jikin kofar yadda in an bude zaa gani, yayi tafiayar sa.
Seebi na idar da Sallah ta dauki Abincinta, Su Nene har sun gama da Abincin da Nasiba ta shigo dashi,nan zaman jiran Sallama sukeyi, Nasiba tace "bari inje in ga Dr, k'ila ma ya mance da yace yau zai sallame mu" Nene tace "E danAllah, na k'agara inga nayi juyi kan Gadon K'arfe na" sukayi daria duka.

Tana murda kofa wata kaaramar Takarda ta fado, duk'awa tayi ta dauka, ta na budewa tabi rubutun da ido, Murmushi tayi a hankali tace "R-Lema" a nutse ta fita daga dakin ta fara karantawa ga abun da yace
_"Ameen to your Duas. Idan an sallame ku, ga number na ki min text you DONT have to Call just TEXT"_.
Seebi tayi murmushi ta sake karantawa, tace *"R-LEMA kenan Allah ka bani ikon taimaka ma beautiful soul dinnan"*. Tasa kai ta wuce office din Dr. A hanya suka hadu da Dr da Nurse Sai suka juya suka koma dakin.

Nurse ta gwada Bp da Temperaturen Nene, komai daidai, Likita yace "Mama, kin ji sauki sosai, zan sallame ku, Amma donAllah ki rage cin Jan Nama" Nene ta bishi da kallon kai gaja, tace *"yaro wani Nama ne Ja?"* yace "Naman Sa, ko na Awaki" Nene ta tuntsire da daria, tace "Su balangu da tsiren da nake ci kake son hanani ci ko? Yace " Mama saboda Lafiyar ki ne, bawai ina son hanaki bane" ta tabe baki tace "toh dai bari kaji Ubana *Mamman* Shanun shi 31, duk bayan wata ake kashe mana daya, ba saidawa ake ba ci mukeyi, kuma ban taba jin ance wani naman Shanu yasa shi ciwo ko wani abun Allah sauwak'a ba, toh nidai _Aminene Mamman_ da bakin ciki ya kashe ni gwara Dadi ya kasheni Ehe" Nasiba tayi saurin cewa "I'm so sorry, She's always like this, InshaAllah she'll regulte it" Dr yace "Dont worry i have someone exactly like her at home" Nene ta cika tayi fam tace "Oho dai, Sai ka sallame mu yau, Ke kuma ni zaki chanzawa ko? To in ma zagina kukai da Ubanki Mahammadu kuke" Dr ya fashe da Daria yace "yi hakuri Mama ga takardar sallamar ki" yafi maka don yau ko baka sallameni ba gida zan kwan" Nasiba ta girgiza kai cike da takaici, Hajjo kuwa sai daria take tayi.

Dr na fita Nene tace " _kinga latso min Zaidu bawan Allah a waya, ba gardama Seebi tayi yadda nene tace, Yana ganin kiranta ya yanke ya sake k'ira
Zaid yayi Murna kwarai da jin Sallamar su Nene, kuma ya bata shawaran bin yanda Likita yace, jin shi kawai Nene tayi don ba ta da Mak'iyi kamar me son rabata da Nama, nan dai ta hau yi mishi Godia da Adduoi, Ya tsaidata ta hanyar cewa Haba Nene, Kun wuce nan, babu godia a tsakanin mu. Sukayi Sallama. Bayan Seebi ta karba wayar ne yace mata zai turo a maida su gida, tace ai "Hamma Rafeeq yace in gaya mai idan an sallame mu" da Mamaki Zaid yace "Rafeeq dai?" tace "eh shi" shi da kanshi yace haka?" tace "eh" "Rafeeq yana zuwa ne?" tace "Duk da ba shigowa yake ba, amma yana kawo mana Abinci Rana da Dare, sometimes ya na aje ni makaranta" Allahu Akbar zo ku ga jin dadi gun Zaid, Ashe Rafeeq na da sauran Mutunci da tausayi a tattare dashi? Be taba ganin Rafeeq ya damu da lamuran wasu ba kamar su Seebi lallai akwai Improvement, yace da Seebi "to sai kun koma gida mayi waya" sukayi Sallama. Duk zaton Nasiba da Nene Zaid ne ya sa Rafeeq dawainiya dasu, duk abunda yake yi saboda Zaid ne, nan suka gane cewa ashe Rafeeq ne ya sa Kanshi, ba kowa ba. Nan Nasiba ta k'ara samun wani k'warin guiwar Aiwatar da Kuddirinta.

Seebi ta kwafi numbern da Rafeeq ya bata, ta masa text din as he demanded. Ga abun da tace;
_"Assalamu alaikum Hamma Rafeeq anyi discharging din mu, mun shirya, we are good to go"_

Yana wanka yaji wayarsa alamar shigowar sak'o, bayan yayi Sallah, ne ya daga wayar ya ga message daga new number, ya bude ya karanta, dan guntun tsaki ya ja (Ikon Allah! sak kace bashi yace ta mai ba).
Key kawai ya dauka ya fice daga gidan sai Asibiti, yana isa ya mata text "Ku fito".

Seebi na jin shigowar text ta duba taga Shine, ba su wani dau lokaci ba suka fito harabar Asibitin da kayan su. Inda yake aje Motar shi sukayi, ta na zuwa ta iske Booth a bude, be fito ba haka Seebi ta shiga saka a kayan boot sai da ta gama, sannan ta bude gaba ta shiga ta zauna su nene kuma sun shiga baya.
Sai da suka bar Asibitin, da kyar yace " Ya Jikin?" Nene ta murmusa a ranta tace Uban Kasaita, a fili kuma tace "Alhamdulilah, na watsake" kamar ba zai ce wani abu ba yace "Sannu Fah" tace "yauwa" a hankali tace kamar dangin Maguzawa wai sannu" Hajjo da Nasiba kadai suka jita, Murmushi kawai sukayi, tun daga nan ba wamda ya sake magana har sai da suka iso gida, ya juya ya dan kalli Hajjo yace "Hajjo Mom tace ki k'ara Sati daya sai ki koma gida" tayi murmushi tace "ba damuwa"
Tare da taimakon Hajjo suka shiga da kayan su ciki, sai da ya tabbatar sun gama kwashe wa ya danna horn, ta lek'o ta window, ya mik'a mata manyan ledojin Abinci, yaja motar sa yayi gidan su Maalesh.

*England*

Zaid ne kwance kan tafkeken Gadonsa yana waya da Mami, inda aka bashi Ayman ta dinga mai gwaran cin ta, har sukayi Sallama sannan ya kira Nasiba,
Suk gaisa ya tambayeta ya jikin Nene ta amsa masa da sauk'i.
Suka danyi hira sannan ya gaisa da Nenen itama ya musu Sallama.
Nan ya hau tunanin wanda zai sa ya musu Grocery shopping, don ya tabbatar suna da Buk'ata, baya son takura wa Rafeeq, Saboda abunda ya fahinta, Rafeeq has done more than Enough, kuma baya so ya k'ure shi .

Maalaesh ya fado ransa, Take ya kira wayansa, Ringing biyu ya dauka "Hello Mahmud" nan take ya gane Uncle Zaid ne, don shi yasan shi kadai ke kiran shi da sunan shi na Asali, "UncleZee ina wuni" suka gaisa, yace "Mahmud ina so donAllah ka min Shopping na kayan Abinci, da kayan buk'ata na Gida, ina so ka kai wani Gida na nan ku sa da gidanku na Layout(Gidansu Rafeeq yake nufi) Nan ya mishi kwatancen gidan. Malaesh yace "Angama, anything for you uncle Z" barin je yanzu ma, "barin maka transferring kudin" da sauri yace "Noo akwai kudi hanuna Uncle Z" "dont be Silly Son, i'm sending now" Murmushi Maalesh yayi yace "Nagode" suka yi Sallama, Nan take Zaid ya mai Transfer din 100k.

2:47pm

Seebi na zaune bisa kujera yar tsugune, tana yi wa Nene tsifa, i Nene da Hajjo na kan tabarmar k'asa, Sallama suka ji, da sauri Seebi ta zaro Mayafin ta kan Igiyar Shanya, Nene ta daura dankwali tare da Amsa Sallama, Maaleah yace "donAllah nan ne Gidan Nene?" da sauri tace Eh Yaro Shigo, nice nan Aminene, yace toh ina zuwa, Yara ya samu ya sa su kwasan kayan ya ce suka shiga gidan nan, Mamaki ya rufe su Nene, ana haka ne Maalesh ya bi bayan su ya shigo, yana ganin Hajjo ya bude baki "Laaaah Hajjo, kece nan?" tace "Maalesh yaushe a gari?" yace "jiya na shigo, na tambayi Mom kina ina tace ba kya nan" tace aiko dai gani anan, ya durkusa ya gaida Nene, ta amsa mai cikin Fara'a, yace "kece Nene daga gani" ta nuna kanta da Yatsa tace "Nice nan Aminene Yar Mamman, duk duniya ba wata Nene sai ni" ta nuna Nasiba da hannu tace "Nenen Seebi kake ji" ya juya ga wacce aka cema Seebi, ya ga shi take kallo, tsaf tagano shi, shine wanda kwanaki da zai basu Lift yace sai ta cire Nikab, kuma Shine Abokin R-Lema, ta dai maske ta gaishe shi, "Lord have Mercy" inji Maalesh, tuni Nasiba tayi gaba da Imanin shi, da kyar ya amsa mata fuskar shi cike da Annashuwa.

"Hajjo tace Maalesh wannan kayan fa?" yace "Uncle Zaid yace a kawo" Nene ta chafe "Allah Sarki Zaidu Bawan Allah, Allah shi biyaka ya saka da Alheri, Malush kaima Nagode maka" Yayi daria yace Nene "Maalesh nake ba Maalush ba" duk sukayi daria, na da nan Maalesh suka dinke da Nene, k'wank'waman su iri daya na surutu, sai yi suke tayi yanda kasan sun dade da sanin juna, dama shi Maalesh saurin Sabo ne dashi, nan Hajjo ta zubo mai Burabusko ya kwasa kamar ba gobe, sai kallon Nasiba yake tayi, ita kuwa sai smilling take tayi tana jin diramar su da Nene, har kusan Laasar be da niyyar tafiya. Wayar sa tayi k'ara, ya ciro daga Aljihu ya duba, ya kalli Hajjo yace dan gidan ki ne, tayi murmushi tace "Rafeeq Ho" ya dauka "my guy howfa?" kusan sakwan 3 beyi magana ba chan yace "kana ina? Nazo gida baka nan" Maalesh yace "Wallahi gani ta wurin gida Uncle Zaid ya aikoni" tsaki Rafeeq yayi yace "ina jiranka" ya kashe wayar, Nasiba ta tsura wa wayar Maalesh ido, kamar tana jiran Rafeeq ya fito daga ciki, Nene tace "Wannan uban Yan k'asaitan ne ko?" Maalesh yayi daria yace "Nene kinsan Rafeeq ne?" ta ta6e baki tace "ai wannan sai kun hada mai da tofi" yayi daria yace barin je, sai na dawo ya musu Sallama ya kalli Nasiba yace "Bye Beautiful" ita kunya ma ya bata ta rufe fuskar ta da tafin hannayen ta.
Chapter 42 · 0% Book details