← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 95

Sashe 38

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Rafeeq ya shirya don yana da Morning lectures, ya fita daga dakin shi, a tsakar Gida ya ci karo da dukka 'yan gidan, dauke kai yayi kamar be gansu ba ya chanza hanya ya nufa motar sa, Alhaji Habib ya ciri baki yace *"Rafeeq"* kamar ba zai juyo ba ya juyo yana kallon su one by one, Daddy, Saude Meema sai Aneesa ne a tsaye, wani gololon bakin ciki yaji da ya hada ido dasu duka, dadi kamar ya kashe Aneesa yau tayi tozali dashi, kwana biyu ta lek'a dakinshi sai taji a kulle, a hankali ya tako gaban su kallo daya ya ma Baban shi, da kyar yace *"Daddy Barka da Saffiya"* Alhaji Habib da murmushi a fuskar shi yace *"Ibn Zaid ka tashi lafiya?"* kai kawai ya gyada mai, yace *"Zanyi tafia, zanje Abuja , zanyi kwana biyu"* yace "Sai ka dawo" "yaushe Baban ka zai dawo?" a k'agare yace *"Upperweek"* *"baka gaida Auntyn ka ba"* da sauri Rafeeq yace *" na makara, na tafi"* ya wuce ya bar su tsaye a nan, Saude ta bude baki cike da mamakin Rafeeq, Alhaji ya wayance *"Rafeeq kenan, an samu yau zai je school"* Aneesa tayi saurin bin shi a baya, "Ya Rafeeq jira ni nima makarantar nayi, sai ka ajiye ni" be tanka ba, burinshi ya fada motar sa, *"Ya Rafeeq mana"* tayi saurin shan gaban shi haushi ya kama shi, shi dai ya tsani Aneesa,cikin hargowa yace *"zaki matsa min ko sai naci Ubanki"* Duk diramar da akeyi akan idon Saude,Meema da Alhaji akeyi , ita kuwa Aneesa dadi ya kama ta, yau wace rana Rafeeq ya mata magana, ita ba ta k'i ya dinga lailaya mata Ashar kullum ba, indai shine hanyar maganar shi gareta, Rafeeq ya lura kwata kwata hankalin Aneesa be gun shi, ta tsura mai ido tana zabga murmushi, tsaki yayi ya raba ta gaban ta ya wuce, ta an kara da hakan da sauri ta rik'o hannun shi, yana waigowa a fusace ya haska ta da wata irin hadaddiyar mari, ji kake tass, Ya nuna ta da yatsa, *"kar ki k'ara gigin tab'ani, idan ke maiyace to ki ci kanki, banza dangi Mayyu"* ya idasa motar sa, ya fada ya danna wani uban horn Baba Maigadi ya bude gate, a sittin Rafeeq ya bar gidan. Zo ku gane min Fuskar Saude, yanda ku kasan Zakkanya, sai huci take tayi, Meema kuwa zaro ido tayi sosai tana Mamakin Rafeeq, wato sune dangin Mayyu? Alhaji kuwa dafe kanshi yayi don kunya, Aneesa kuwa tana ganin fitar Rafeeq ta fashe da wani irin kuka, A gudu Saude ta karisa ta rungumo ta, ta ma kasa cewa komai don Rafeeq ya gama kashe ta, Alhaji ya matso yace *"Anee Baby kiyi hakuri, kema tunda kinsan halin Rafeeq, ki daina kulashi"* Waiyo Allah zo ku ga takaici kwance kan fuskar Uwar Aneesa, wato ba zai yi fada ba ko? Gaskian hausawa da suka ce Naka Naka ne, Hajia Saude ni barin wuce, da kyar tace *"Allah ya tsare Hanya"* be tsaya wata wata ba ya fada mota direba Ya ja motar suka bar gidan, kamar jira suke ya fita Meema tace *"JarUban chan, Sis kina kallo? Ya zaayi ya mare Aneesa?"* Saude da haushi ya mata katutu tace *"Bari dai Meema, ina mamakin wannan karfin halin Rafeeq, Ko ni uwarta ban mareta ba, sai shi lallai Ya Tafka babban kuskure, this is the last time you will hurt my daughter Rafeeq, i know What to do with him"* sai a sannan Aneesar ta dago, tace *"No Mom, you are so not doing anything to him, if anything should happen to him, i'll hate you for the of my Life"* ta ruga a guje ta koma cikin gida. Yanda kuka san an shuka Saude haka ta tsaya, saboda Rafeeq Aneesa ke cewa zata tsaneta? Lallai kam dole ta dauki mataki kan Rafeeq, Meema sai tunzurata take tayi, ita kuma sai hawa take, ta cika tayi Pam.

Tuk'i takeyi cikin kwanceiyar hankali, kamar ba abunda ya faru, ko kadan beyi tunanin abunda ya faru gidansu yanzu ba, ko a kwalar rigar shi Burin shi kawai ya sake ganin ta, tsintar kanshi yayi da zuwa Crispy, yayi ordering breakfast leda 3, Chips egg and Plantain, aka mai packaging, ya biya ya koma mota, ya kunna yana tunanin yaje ko kar yaje, zuciyar sa me tunzura shi ga mai yanayi da Rafee'ah tace yaje, haka kuwa akayi, don Rafeew Asibiti K Dara ya nufa, cikin minti k'alilan ya isa, ya kwaso leda 2, ya fita yana tafian nan na shi, sai gashi gaban Dakin da aka kwantar da Nene, ta window ya lek'a su, inda Nene ke cewa *"Kinga dai ki shirya ki wuce Makaranta ko? nace miki zan iya zama har ki dawo, ba abunda ke man ciwo "* Nasiba tace *" ni fa na gaya miki ba inda zanje, ni da Makaranta kuma sai kinji sauki kinyi garau abunki"* Nene ta sausauta murya tace *"kiyi hakuri Jikata, ki tafi DonAllah, bana so ki samu matsala da Makaranta"* Seebi tace *"Wallahi ba zanje ba"* Nene ta buga tsoki da k'arfi tace *" Nifa bana son mutum me shegen taurin kai da kafiyyar tsiya"* Seebi tayi daria tace *"Ai fah, ni barin je in siyo mana Kalaci"* Rafeeq na jin haka yayi saurin Aje ledojin gaban k'ofar dakin, da sauri ya bar gurin. Ta na bude k'ofa ta ci karo da wadannan ledoji ta tsugguna ta dauka, tace wannan kuma fa? Wani Kamshi da tayi amanna na Rafeeq ne taji, da sauri ta juya ko zata hango shi,amma wayam ba ta ga kowa ba, tabbas wannan ledojin Rafeeq ya aje su, ta hau tambayan kanta, to meyasa be shigo ba? Ohh na manta he is R-Lema, he cannot come in, ta saki wani Murmushi, tace *"R-Lema i'm Coming for you"*.

A kan Sitiyarin Mota ya kifa kanshi Ya shiga magana a zuciyar shi shi kadai, *"She cannot start skipping School"* guntun tsaki yayi ya tada Mota, ya bar Asibitin, me makon ya wuce Makaranta, sai ya wuce Gidansu Maalesh, yana shiga gidan ya wuce Cikin Gidan straight, kai tsaye ya shige ciki, Mom din Maalesh ya gani zaune kan 3 sitter, ta hade kafa daya kan daya tana kurban Koko a cup, Hajia Maryam kenan{Om Eman} kallo daya zaka mata zaka san cewa Yar boko ce, zatyi tsarar Mamin su Rafeeq, k'awarta ce sosai, da k'yar taji sallaman Rafeeq, ta dago ta kalleshi, ta amsa da fara'a tare da mik'a mai hannu ta mai nuni da yazo ya zauna kusa da ita, tana son dan Aniniyarta sosai, Zama ya zo yayi kusa da ita a hankali yace "Mom barka da Safiyya" tace "Son Ka tashi Lafia?"* kai kawai ya daga mata, Murmushi tayi a ranta tace oh ni Rafeeq when will you ever change? Shiru ya dan gifta, tace zaka sha Koko? Girgiza kai yayi alamun Aa, tace "to me kakeso in hada maka?" da kyar yace *"bakomi"* chan ya kamo hannun ta yace *"Mom, Hajjo zaki bani"* (Hajjo Mai aikin su Maalesh ce, tsohuwa ce, tun Maalesh na jariri take gidan) ta kalleshi da alamun tambaya, yace *"Jinya zatayi a Asibiti"* Mom tace Jinyar wa? Waye be Lafiya? To anzo gurin, idan akwai abunda Rafeeq ya tsana be wuce ya bude baki yayi bayani ba, baya son dogon surutu, be san ta inda zai fara bata bayanin nan ba, kawai sai ya mik'e zai fita tayi saurin kamo hanun shi, *"haba Rafeeq, ya zaayi ka fara magana kuma sai ka tashi ka fita?, jinya wa Hajjo zatayi?* Tsaki mara sauti yayi yace *"ki bari kawai, na fasa"* Girgiza kanta tayi tace "Rafeeq you are very Stubborn" ta harare shi ta mai umarni da ya zauna, ta shiga ciki ta iske Hajjo na kakaci, tace da ita Hajjo, idan ba matsala Rafeeq ke so kije Asibiti kiyi jinya, kinsan hali na tambaye shi waye be lafia,da ya min bayani ya gwammace a barshi, Hajjo tayi dari tace kna ruwan dan gidana, ba komai Wallahi, zanje, kinsan akwai ladan masu Jinya, ina kwadayin shi, Barin tashi in shirya, Mom ta mata Godia, ta koma parlor inda ta bar Rafeeq, ta daure fuska tana hararar shi, shi ko sai Murmushi yake tayi, dan yana jinsu ita da Hajjo, ba jimawa Hajjo ta fito da ledar kayanta, ta ma Mom Sallama, Rafeeq ya kamo hannun Mom tayi saurin fizgewa, a hankali yace *"Mom, Nene ce bata da lafia, Kakar erhm ya ma sunanta? ya tsaya yana son tuno sunan da yaji ana kiran yarinyan, yace toh na manta sunan, i've said enough mun tafi"* be jira cewar ta ba ya fita, ita kuma Murmushi tayi, tana me tausayin Yaron Aminiyyarta.
Chapter 38 · 0% Book details