← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 95

Sashe 13

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abubuwa da yawa sun faru, cikin shekaru biyar nan, Ciki kuwa harda gama makarantar Hafiz da Zaid, ya kamata ace Hafiz ya gama ya dawo gida tun last 2years saboda Course duration dinshi 2and half year ne, amma shashanci da Iskanci ya hanashi dawowa, Hafiz ya kware a fannin Chacha da harkar cocaine (Gambling) duk Malaysian Gambling center sun san da zaman Hafiz, duk ya karar da kudin Zaid, kuma kullum shine tambayan Habib kudi, gashi duk bayan Wata 5 yake zuwa Nigeria, abun ya damu Habib amma bai yi magana ba.
Hafiz shine drugs, duk wasu kayan maye Habib ba wanda be sha. Amma abun alajabi shine, hafiz beyi kama da mai shan ko da sigari bane. Yanzu dai Hafiz ya talauce, baida kudin Chacha, baida kudin Cocaine, ga Bashi ana binshi na wurin Gambling, wasu thugs ke barazanar daukan rayuwar shi, sunce ya biya su, yace Yayan shi zai turo, shiru sukeji don tunda ya ma Habib maganar kudi shiru kakeji, zaman shi Malaysia baida wani amfani, Returning ticket dinshi yaje yayi renewing don zuwa Nigeria, Ogan Yan Chacha ya had Hafiz da wani yaron shi don ya bishu Nigeria ya taho musu da kudin su. Hafiz beyi gardama ba, don shima yana da bukatar kudi, dole ko yazo Nigeria Alabasshi idan ya kara hada wasu kudadden ya dawo.

Tunda Zaid ya tafi USA ya fara karatun shi cikin kwanciyar hankali, Kullum suna waya da Aishatu, Rafeeq da Zaid sun yi wani irin Shakuwa kamar yana Nigeria, da ya dawo school har ya san ya bude datan maman shi ya shiga Skype don suyi Video Call da Uncle Zaid, Rafee'ah tayi ta kuka kan Hamma Rafeeq ya bata wayar amma haka zaiyi banza da ita ta yita tsala ihu har sai Mami tazo ta amshe wayan ta bata ko shi Rafeeq din ya ga daman bata wayan. Duk wata Aishatu na raba Albashin ta ta tura ma Zaid rabi, Habib kan kira shi su gaisa, amma bai taba tura mai ko taro sisi ba itama Aisha bata taba tambayn shi ba. Wata sa'in idan ba a ma Aishatu Albashi ba, ba ta da sukuni, ta dinga zirga zirga kenan, ina zata samo kudi ta tura ma Zaid? Zaid ko yana fuskantar ta duk da ba ta fito fili ta gaya mishi damuwar ta ba ya kan fahimceta. Yace Aunty kar ki dinga damun kanki, zan sanu part time job a nan ko da Cafe ne, zanyi serving as Waiter. "Waiter? kar ka sake inji Zaid, kafi karfin nan, kar ka damu, i'll find a way to make money kaji?" yace "naji Allah rufa asiri" Jin ta kawai yayi, ba zaiyi kwance tana mishi komai ba, shima zai tashi don taimakon Kanshi.

Tun tafiar Zaid Shekara Biyar kenan be taba dawowa gida ba, a ganin shi takura ne ga Aishatu ko kudin Jirgi matsala ne, shisa duk yanda taso yazo gida fir sai yaki yace har sai ya gama toh gashi dai ya gama sai shirin dawowa.

BAYAN DAWOWAR HAFIZ.
Tunda ya dawo ya ke sak'e sak'en inda zai samu kudi, yaje Warehouse be ga komai ba, da alamu Habib ya chanza ma'ajiya. Tunanin mafita yakeyi, gashi ba zai iya tambayan Habib kudi ba. Wani tunani ya fado mai, da sauri yayi murmushi.

Karfe sha dayan dare(11pm), bayan Yara sunyi bacci, Aishatu ta dauke su ta kai dakin su, ta wuce dakinta ta tsala wankan ta, ta saka night gown ta fito ta jawo kofar tayi dakin Mijinta Habib, da sallama ta shiga, yace "Shatou na, har yaran sunyi bacci? Tace eh sunyi, Rafee'ah da rigima wai sai dai kar hamman ta ya Kwanta a cinyana, Habib yayi daria, yace "ina ruwan kishiyoyi, yauwa Shatou, dauko bargon dakin ki, jiya naji sanyi wallahi, tace kamar akwai bargo a nan, yace "eh yayi k'ura, gobe zan bada a wanke" tace "toh bari naje na dauko" ta juya ta fita a hanzarce.

Hafiz na ganin Shigewar Aishatu dakin Habib yasan ita da fitowa sai gari ya waye, sadaf-sadaf ya shiga dakinta, drawern madubi ya je ya jawo be ga wani abun dauka ba, side drawer ya koma ya bude, dubu biyu da dari biyu ya gani (#2200) ya gani ya zare ya sa a aljihu yace ko sigari na sha. Yana jawo na kasan ya ga wayam, kamar ance ya ciro dirowar ga baki daya, yana cirowa sai ga wani dan case a kasa, ya ciro case din hannu na rawa, yana budewa ya ga wata dankareriyar Saitin Sarka da yankunne, da abun hannu da zobe, tsaf ya gane sarkar ce da ya siya ma yayan shi a matsayin gudummuwa lokacin bikin Aishatu, ihun murna ya sake harda yar hamdalan shi, yayi daria yace "wannan shi ake cema ja ya fado ja ya dauke" yayi sauri maida Drawern ya tura case din cikin rigar shi ya mik'e don fita. Juya wan da zaiyi wa zai gani? Aishatu ce tsaye kikam tana kallon ikon Allah hannayen ta kan kirjinta.

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg1⃣8⃣

Ihun da Habib yayi ne ya tashi Zaid da Mdaga bacci, da sauri ya fito suka fito daga dakin baccin shi, yayi cikin Gidan don ya san tabbas ba lafiya.

Hafiz a kidime yace " Akwai Matsala" Anas yace "mu ware kawai" Hafiz yace "aa its too late, lets just act smart" daidai nan Habib, Zaid, Aishatu suka shigo dakin.
Zaid ya damke Anas, Habib kuwa bai yi sanya ba ya chakumo wuyar rigar Hafiz yace "What have you turned yourself to? A monster? A heartless, selfish person? Me ya sa ka dauke Safe din Zaid? Bayan kowa an bashi Kason shi? Ka k'ulla mai sharrin shi ya dauka, Wannan wani irin cin Zali ne?" Zaid ya kalle su cikin rashin fahimta, yace "whoa!, wani Safe aka dauke nawa? Hafeez cike da borin kunya yace " I dont know what You're talii about, let me go" Habib ya kai mai nushi a baki, ya ja wuyar Rigar shi har gaban TV din Office din ya kunna, ya kara jan shi har gaban Safe din ya saka Password din, Safe ya budu, dan karamin security camera da ke jone da Safe din Habib ya danna, sai ga fuskokin Hafiz nan da Anas tunda suka fito da Safe din, duk abubuwan da suka fada sai da suka gani kuma suka ji kamar a film, Zaid ya dinga maimaita Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Be son sanda ya sake Anas ba ya nufa Hafiz cikin zafin nama, Anas na gannin haka ya arta a guje. Zaid na zuwa ya daga hannu ya faska ma Hafiz mari har kala 2, yace "how dare you Hafiz?" dama kai ka dauki Akwatin nan kace nine? Ka sa Yaya ya tsane ni? Ka sa ni cikin Halin Kunci? Hafiz me na maka? Ni da kace ka na son kudin wallahi zan mallaka maka halak malak, amma sai ka bi ta bayan Gida, Hafiz i wont forgive you "

Hafiz ya fashe da daria cikin borin kunya wacce aka ce da hauka ake nadeta, yace " *So what? Now that y'll know my deepest secret, what are you going to do? Ehh? Ya kalli Yayan shi what are u going to do Habib Lema? Hand me over to the police? Go on you never cared dama, ka kira min polisawa su tafi da ni, kaga ko ba wani Abu bane don dan kishiya ya tura kaninsa gidan kaso(jail)*."

Zaid yace "Kar ka damu Hafiz, ai daga nan Police station kayi, naga you are so eager ka ganka behind bars(bayan kanta.) Hankalin Habib ya tashi ba zai taba tona asirin Gidansu ba, hada Hafiz da police kamar tona ma marigayi mahaifinsu asiri ne, Habib ya kalli Zaid yace "Zaid, so kake Hafiz ya biya ka kudi da kaddarar da ya satan maka?" Zaid yace "ni ba abunda zanyi dasu, Burina Allah ya ji kan mahaifa na, ya ji kan yanuwa na" Habib yace "Madallah, let him go" a tare Zaid da Aishatu sukace "what?" Habib yace Hafiz is our Family, kar mu tona asirin junan mu, mu taya shi da Adduan shiriya" Zaid be tanka ba ya bar office din, Aishatu ta bi bayan shi, Habib ya kalli Hafeez cikin sanyin murya yace"Jeka kwanta its late" Hafiz kunya da tausayi suka lullube shi, ya sa hannu cikin aljihun shi ya ciro Agogon Swatch din da ya sata, ya mika ma Habib yace "da a ce baba na da rai, he'll be very oroud of you Yaya" habib ya sa hannu ya amshi Agogon ba tare da yace komi ba, shi ko Hafiz ya sauka kasa zuwa dakin shi.

Cikin dare Hafiz ya tattara kayan shi tas, ya ciro wayar shj ya kira Anas, Anas a tsorace ya dauka yace "hello, matsoraci kana ina,?" Anas yace kaii kaji yanda hanji na suka kada, na mugun tsorata?" Hafiz yayi dan tsaki yace "kai ni zo ka dauke ni ina nan ina jiran ka" Anas yace wa? Ba dai ni ba, bari ma turo maka Escaley kawai" cikin mintuna kadan Escaley ya kira Hafiz yace mishi yana waje, Hafiz ya kwashi kayan shi da kyar ya fita waje, Escaley ya taimaka mishi, Mai gadi na tsaye yana kallon ikon Allah, farar takarda Hafiz ya ciro ya ba mai gadi, yace ya ba Yayan shi ko Zaid da safe, me gadi yace "Oga Hafiz ina zakaje da daddaren nan, 2 ta kusa fa" be amsa shi ba ya shige mota Escaley ya ja motar.
Chapter 13 · 0% Book details