Sashe 29
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ayman, ga Daddyn ki" dugul dugul ta tako tana ta washe baki, Zaid ya daga ta ya wulla ta sama ya chafe, ya rungume ta yana juyi da ita, ita ko sai dariya take tayi. Mami da ke kallon su tace "ka ga, kar ka sake min d'iya ta fadi" Zaid yayi daria, yace wane ni in kada diyar Mami?dariar tayi tace "ashe kana tafe? Ya hanya? Ya yan katsina? Yace "Alhamdulilah suna ta gaishe ku" tayi dai murmushi don ta san in banda iyayenta ba wanda zaice a gaida ta, tace "barin dora ma ka abinci, nasan ka gaji" yace "Wallahi kuwa Mami, Yunwa nikeji banyi breakfast ba na taho" me kake so kaci? Yace "tuwo miyan kuka" tace "ahh ba yunwar kakeji ba, tuwo ai zai dauki lokaci" yace "Wallahi ina jin yunwa, amma ina iya tsayawa har ayi tuwon" tace "sai dai daddawata ta k'are" ya mike tsaye yace "kar ki damu na miki tsarabar daddawa da kuka, duk sun bide min mota da wari, Wallahi kiris ya rage na wurgar dasu, ashe zasu min rana" be jira ta cewarta ba ya fita, Ayman a hannun shi, har ya bude mota ya dauko ledar k'ullin ya dawo, ya mik'a mata, ta bubbude tace "Zaid wadannan kayan daga ina? Yace " Wallahi wata tsohuwa ta bani" Tsohuwa kuma a ina? Yace "a Katsina" tace Zaid ka santa ne ka amshi wadannan abubuwan? What if shes upto something, number 1 lesson, u cant trust people?" Yace "Relax, i trust this one, i trust Nene, yanzu dai ki sa daddawan da yawa, miya ya fi dadi" Mami ta kwashi ledar ta na mita, tace "yanda na ga dama haka zanyi, in kayi fushi kayi aure and stop ordering me around" Daria yayi sosai yace "yi hakuri Mamin mu".
Haka Mami ta gama tuwo miyan Kuka da ya ji busasshen kifi, Zaid ya ci sosai, yaji dadin Miyar nan, ita ma Mami taji dadin Kukar, daga jinta sabuwar kuka ce, sai santi suke tayi, Mami ta kwashe kwanukan ta kai Kitchen shi kuna Zaid yac cigaba da ma Ayman wasa, Yarinya kyakyawa sosai, yar shekara 1 da yan watanni, idan ka ganta za kayi zaton tayi 3years din nan, sabida yanda take yar b'ulb'ul da ita, kuma ba wai Nono ta sha ba, bayan Rasuwar Safiyya Madara ta ke ta sha, NAN kuma aka ci saa ya karbeta, Dangin Mahaifiyar ta sunso su amshe ta amma Zaid ya hana, yace shima Mamar shi(Mami) zata riketa, haka suka hakura, Little Rafeeah na zaune tare da Mami a unguwar Malali, kullum Zaid sai yazo ya duba lafiyar su kafin ya tafi Gidan shi, yana tausayin Ayman, amma idan ya tuna tana tare da Mami sai hankalin shi ya kwanta don ya san Ayman ba za tayi maraicin Uwa ba.
*KATSINA*
"Me ya samu Nasiban Nene na ga ranta a bace haka? ko shi lapturo(lecturer) din ku ne ya bata miki rai gobe in mishi asubanci inji dalili?" ba ta san lokacin da ta fashe da daria ba, tace "Nene, Wallahi Hukumar Makaranta ce wai mu daina sa Nikabi saboda k'asa ba lafia, ana iya yin Basaja a shiga Makaranta ayi barna" Nene tace "kai sun kyauta, ba ki san yanda na k'ijinin in ganki da nikabi ba, kamar wacce tayi k'arya, ke da ba tsiraicin kika fiddo ba, amma duk ki rufe fuskar ki ruf" Nasiba ta shagwabe fuska tace "Kai Nene, so kike ranar Makaranta ta kodar dani? Kuma mutane suyi ta kallo na?" Nene tace "ke tafi chan, yo ai sai ki shafe fuskar ki da hoda, kuma in ta kallo ne ai kin kai a kalleki, yar jikalle ta jikan Yan Sudan, donAllah ki dinga gyara fuskar ki kamar wannan yar gayun, Meemo take ko wa?" Nasiba ta fashe da dariya, ta tashi ta yi hanyar daki tana cewa "Miemee ake cewa ba Meemo ba" Nene tace "ni rabani da sunan Aljannu, yarinya da sunan ta me dadi Maryam ta koma wata Meemai ko wace tsiya" ita dai Nasiba daga cikin daki take ta daria, Nene ta cigaba da Mitar da idan ta fara bata san tsa tsaya ba, "kema Baban ki ya bata miki suna wai ba a iya kiranki da sunan Yankan ki sai Seebi har ya koya min nima" a hankali tace "Amma fa sunan fa da dadi, na yan gayu, Seebi, Seebin Nene" me Nasiba zatayi in ba daria ba. Nene ma ta sa daria ashe ta na jinta, ta mik'e tana fadin "Uban me ake ma daria cikin k'urya?".
Maalesh ya fito daga Motarshi da ya parka ta a haraban Gidan su Rafeeq, Aneesa na ganin shi ta k'araso da sauri tana yauk'i tana karairaya, Maalesh ya fara mata murmushin da be kai zuciyar sa ba, " Yaya Maalesh, howfa" yace "Anee baby ya kike?" Lafiya fa, dama ina so in kara maka tuni kan Yaya Rafeeq, Wallahi son shi na cinye min yan Hanjina, na rasa me na mishi da ko ganina ba ya son yi, idan na je gurin shi yanda kasan yaga bak'ar Jab'a, kallon arzik'i baya min, gashi zuciya ta ta kasa hakura dashi, ya zanyi?" Maalesh da ya k'osa ta gama maganar ta don warin gashin dokin ta ya cika mai hanci, yace "karki damu zan mai magana" dadi ya rufeta, kafin tace wani abu Maalesh yayi gaba.
"Guy Yane?" Rafeeq ya dago kai ya kalli Maalesh da ya shigo yanzu, da k'yar yace "Normal" Maalesh yace "ba ka kirani nazo nayi picking dinka yau ba?" kamar ba zai ce komai ba yace "Da mota naje" "Ohh, is that so?" nan Maalesh ya shiga bashi labarai, abubuwan da suka faru da friends din su, har zuwa inda Aneesa ta tare shi, Rafeeq dai be ce komai ba ya cigaba da latsa wayan shi, Maalesh be damu da shariyan Rafeeq ba don inda sabo ya saba, wasu lokuttan Maalesh na bashi labarai ne ba don yaji ta bakin Rafeeq ba, kawai don dai Yayi keeping dinshi Company, kasancewar he's alone, Ba wai Rafeeq be gane Labaran da Maalesh ke badawa bane, tsaf ya ke fahintar shi, don wasu lokaci idan Maalesh ya bashi daria ya na dan murmusawa abu kadai ke mai wuya, Magana. Ya na jin k'yuwan Magana, yana ganin Asaran Yin magana.
"Sis nikam Nagaji, ya zanyi wai da son Zaid?" Sauda ta kalli kanwar tace "Meema, dont give up so easily, kafin ki samu abun da kikeso dole ki wahala, kar ki manta wahalar da na sha kafin na samu kaina a Gidan nan, kar ki damu, ke dai kawai ki cigaba da jawo hankalin shi" wani Jawo hankali? So nawa kuma? Ai ni ina ganin idan har na yi Zindir gaban Zaid ba zai ji na burge shi ba" Sauda tace kar ki damu in ya san wata, be san wata ba".
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg3⃣1⃣
A cikin mota suka lumama Hafiz Wuk'a, bude k'ofa sukayi suka wurgar dashi suka wuce, nan da nan mutane Suka taru kan Hafiz, Zaid ya fito daga Jamiar ya dinga kiran layin Hafiz har ya katse ba a dauka, nan ya ga taron jamaa daga gefe, kamar ya wuce sai Zuciyar shi ta kwadaita mai da ya tsaya, yayi parking motar yq kutsa cikin mutanen nan, ganin Hafiz yashe a k'asa jini ya sa shi karasawa da sauri, Yana kwala mai kira, Ya rungume Hafiz a jiki, sai tari yake tayi, murmushin Karfin Hali Hafiz ya sake da k'yar yace "Zaid, brother, ina neman yafiyar ku kai da Yaya akan duk wasu abubuwan da na muku, ku yafe min, ka ce ma Aunty Aisha ta yafe min itama, na san na mata laifi" Zaid kuka yakyi sosai, yana cewa "Stay Still Hafiz, i'll bring you to a hospital" Jamaa ku taimaka mana donAllah, Aiko bayin Allahn gurin Suka ciccibi Hafiz, suka kaishi motar Zaid, Zaid ya rokesu idan da wanda ya iya tuki ya jasu, wani dan makaranta ya ansa key din, shi da wani gaba, Zaid rungume da Hafix a Bayan mota, tarin Hafiz ya tsananta, kafin a kaishi asibiti ya amsa kiran Allah, Zaid ya fashe da wani irin Kuka, Gida ya bukaci su wuce, Alh Habib yai ta kiran Zaid a waya, da kyar Zaid ya dauka ya gaya mai halin da ake ciki, nan gaban Alhaji ya yanke ya fadi kasa Sumamme, don har Ranshi yake son Hafiz, DVC din UMYUK ya shiga rudani, da sauri ya dauko bottle water ya shafa ma Alhaji Habib, Attishawa yayi da k'arfi ya farfado, Sallalami ya farayi, yana kuka kamar mace.
Gida DVC ya kawo shi, a tsakar gida ya ga an shinfide gawar Hafiz, duk yan gidan na nan tsaye, ya tako har gaban gawan ya bude fuskar Hafiz, gashi nan fuskar tayi fayau, Waiyo Allah, zo ku ga kuka gun Alhaji Habib, Rafeeq na tsaye yana hawaye, mutuwar Rafeeah ta dawo mai sabo, ga Uncle Hafiz ya rasu, kwana Goma Tsakaninsu da Rafeeah, Zaid a zaune kusa da gawan yana kuka, Sauda da ke gefe sai ihu take tayi, Aneesa da ba wani sabawa sukayi dashi ba taji jikinta yayi sanyi, kuka take kamar ranta (Mahaifi ba wasa bane) Liman yace "ai sai a gaggauta a mishi sutura akai shi Makwancinsa" da taimakon Baba Tj da Yan Unguwa aka yi ma Hafiz wanka a Parlon Gidan, cikin Mintuna da basu wuce 50 ,ba aka kai Hafiz gidan shi na gaskia.
Alhaji Habib fa ya zare, ko Rasuwan Rafeeah be firgita shi kamar yanda na Hafiz ya gigita shi ba, duk ya bi ya fita daga hayyacin shi, Ya fara tambayan kanshi? Why are these happening to him? Da sauri yayi Istighfari da zuciyar shi ta tunasar dashi kar kayi sabo, kai musulmi ne.