← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 95

Sashe 28

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Fitowar Hafiz kenan daga Parlorn Alhaji Habib lema, ganin Zaid ya sa shi fitowa, ya dan basu guri ne don su tamu tataunawa da Zaid, yazo wuce wa, daidai kofar dakin Sauda yaji tana cewa;
Saude ta kalli kanwarta tace "Meema, shi wannan Rafeeq din da kikaji Aneesa na magana dan Alhaji ne fa, wani irin banza yaro ne me baudaden zuciya, wai shi Aneesa ke so, kinsan kuwa yaron nan har Marina suka tabayi shi da wanda ta mutu?" Meema ta zaro ido tace "ke haba?, to ke me kika musu,kar kice min baki masu komi ba? Tace "trust me, ban musu komai ba time din, illa kara jan su jiki da nayi, sai Mak'ale ya kawo mun poison, na zuba musu Abinci, poison din ba me kashewa nan take bane, slowly ya ke cin yan hanji, a karshe sai mutum ya mutu don gudun zargi, to too bad Rafee'ah din ce kadai ta mutu da alamu shi be ci abincin ba, amma bakomai shima ba dadewa Zai bi yaruwar sa". Sowa Meema ta sake tace " shisa nake sonki, nobody dare mess with us" tashin hankali ya rufe Hafiz, Ya bugo kofar dakin da karfi. Sauda da Meema suka tashi a firgice.

Suna rok'on Allah yasa Hafiz be ji su ba, wani irin kallon tsana ya bi Saude da Meema, Yau duk me zai faru sai dai ya faru wallahi, don he wont let this pass, dole ya tona asirin Sauda, Meema tayi saurin cewa "Uncle Hafiz ina wuni kwana da yawa" wani irin mugun kallo ya wurgeta dashi, cikin dacin murya ya fara magana "Sauda ashe rashin imanin ki yakai haka? Wani irin zuciya ne dake? Shin baki tsoron Allah? Ba kiji komai ba kika kashe innocent soul kamar Rafee'ah? Kisa fa Sauda? Toh wallahi asirinki ya gama tonuwa, yau din nan xaki fuskanci hukuma, Duk duniyancin Sauda yau ta rude, ta shiga rok'on hafiz da ya tsaya suyi magana, ba abunda yake zato bane, yace "baki da hankali, kina nufin banji me kuka ce bane? Ko ban fahimci abunda kuka ce bane? Ai duk abunda kuka fada is straight, ba sai na nema wani bayani ba, abu daya kadai zance miki, dole a zartar da hukunci kanki. "I wont let you keep hurting innocent souls, i wont let you keep hurting the people i love" ko ina na jikin Sauda rawa yake, tace "Hafiz Is not that you are saint or perfect, kar ka manta kai ka kawo ni matsayin da na ke a yanzu, da taimakon ka na shigo gidan nan, kuma kar ka manta da diyarka Aneesa, think wisely, tona ni barazana ce ga ruining reputation dinka, kuma if i go down, you go down with me as well". Hafiz yayi wani murmushi, yace "Sauda kenan, i dont care, ko me zai faru ya faru, ni nakawo ki gidan nan right? Kuma nine silan barin ki, its time i do good thing to the people who did alot for me, i dont care about the consequences, I am Ready, you cannot use me again". Yana kaiwa nan ya juya don barin dakin, Sauda da Meema a rude suka bishi a baya suna mai magiya amma fir ya k'i kula su, Parlorn Alhaji Habib ya shiga, Wayam ya gani, ya lek'a dakin nan ma baya nan, Sauda ta sauke numfashi, Hafiz ya wurga mata harara ya ciro wayar shi ya danna ma A.Habib Kira ringing daya ya dauka "Hello Hafiz" "naam Yaya, kuna ina, ni da na barku parlo kai da Zaid" yace "Eh wallahi, dama Zaid ne ya buk'aci muje Makarantan su Marigayi mu sanar dasu Rasuwarta" Hafiz yace "Okay, gani nan zan biyoku Umaru Musa din" Alhaji Habib yace "lafiya Hafiz?" Hafiz yace "sai dai nazo, yau ranar tonon Silili ne, there are things you need to know, yau ZAN FASA KWAI" dif ya kashe wayan, Sauda ta rude matuka, tana ma Hafiz magiya, we can fix this, feez-boy na tuba kar ka min haka" ai ko kallo bata ishe shi ba ya fice ya bar dakin.
Hannu ta daura a kai ta saka ihu, "Shikenan tawa ta sameni, karya ta ta kare asiri na ya tonu"

Meema cikin tashin hankali, don gani take idan asirin Yayarta ya tonu, bata ba auren Zaid gashi ita kuma har ga Allah ta sama ranta auren shi, cikin bacin rai tace "Haba sis, dont easily give up, akwai hanyar hana tsaida Hafiz, tunda yanzu fita zaiyi, kawai ki kira bad boys dinki kice su tareshi su gama mai aiki" Sauda cikin doki tace "kutt har na manta da wannan hanyar, hankalina ne baya jikina, bari nayi hanzarin kiran Mak'ale" da gudu ta fita tayi dakinta ta dailo numbern Mak'ale. Ringing biyu ya dauka "Hajjaju mutanen makka" ba ta tsaya sanya ba, tace "Mak'ale kana ina?" yace "gani ta wurin Fatima Shema Housing Estate" Hamdala tayi tace yauwa, wani aiki nake so ka min, ga Hafiz nan zuwa Umaru Musa University, so nake ka tareshi, ka kashe shi, i dont want him to make it to Umyuk" mak'ale yayi shiru yace "haba hajia, wannan aiki da safiyyan nan? Ba kya tsoron aka mamu? Gashi mu uku kadai ne, ba sauran mu" tace Mak'ale ka taimakeni, akwai matsala idan Hafiz ya isa Jamiar nan, zan baka Miliyan Guda" Shewa Mak'ale yayi yace angama "Hafiz Lema ya zama gawa" tace "yauwa Mak'ale, zaka gane shi ko?" yayi daria yace "baki da matsala, har kalar motar shi na sani" ya datse wayar Sauda ta sake Ajiyar Zuciya tana labarta Meema yanda sukayi da mak'ale.

Tuk'i yakeyi gaban shi na faduwa, ya sha round din Alkalem University ya dauki hanyar Institutions Road, ya na duba side mirror daidai FCE yaga kamar ana binshi, ko da ya duba mirror din sosai ya gane fuskan Mak'ale, shine ya fito daga dakin Maman su Rafeeq a ranar da suka ganta zindir. Nan jikin shi yayi sanyi, tabbas Sauda ce ta turo shi ya mishi wani mugun abu, gaban shi ya tsananta faduwa, ya taka giya ya k'ara gudun motar shi, suma su makale suka kara gudu, Hafiz ya tsorata matuk'a ya zaro wayar shi yayi dialing numbern Zaid "Hello Hafiz ka taho?" Hafiz yace "Zaid kazo ka taimake ni, akwai wasu masu bina" SubhanAllah a ina? Gamu nan mun kusa Batagarawa, sai fafatawa mukeyi, a guje Zaid ya fito daga office din da suke zaune shi da Alhaji Habib be tsaya mishi bayani ba ya fita, Alhaji Habib ya mik'e, yana kwalawa Zaid kira, Zaid be tsaya amsa shi ba. "Hafiz kana jina? "Eh zaid ina jinka" "yauwa i'm on my way" Zaid incase i dont make it-- Zaid yayi saurin katse shi Hafiz stop, i wont let anyone hurt you gani nan zuwa" "Zaid listen to me, ina so ku yafe min, And you cannot trust Sauda" kafin Zaid ya ce wani abu ji yake kiiiiiiii Alamun cin birkin mota, da karfi Zaid yace "Hafizzzzzz" sai ji yayi ance "kai fito daga motar nan" Zaid ya kara gudun da yakeyi har ya kai inda yayi parking motar shi.
Mak'ale suka ma Hafiz mugun bugu kafin suka tura shi motar su suka bar gurin.

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg3⃣2⃣

*UMYU Katsina*.

"Nasiba Muhammad, maabociyan sa nikab, yanzu da hukumar Makaranta tayi hani da sa nikab sabo da matsalolin tsaro ya zakiyi?" Miemee ce ke maganar nan, ta na yi tana daria, Ushee tayi saurin shafewa tace "Ahh, k'ila zata daina zuwa Makaranta, yajin aiki zasuyi ita da yanuwanta Ustazai masu sa Nikab" suka sake fashewa da daria. Nasiba ta dan harare su, tace ba abun daria bane "Dollah ku bar dariya, its not like its funny, ni ban ga amfanin hana mu sa Nikabi ba, idan yan Boko Haram din sun tashi shigowa Makaranta Nikabi zasu saka?" Miemee ta sake fashewa da wani dariyan tana cewa "Seebi dangin Shekau" Ushee ta tuntsire da daria, duk suka k'ular da ita, ta san cewa idan ta biye musu zata iya fashewa da kuka, sai ta tashi ta bar musu Ajin, su kuma daria taci k'arfin su, sun kasa bin ta.

Tafiya takeyi tana mita, R-Classes ta nufa, hanyan da tasan ba kowa ta bi, tana ta tafiyar ta ta na tunanin yanda zata cigaba da zuwa Makaranta ba Nikab taji kamar K'andagare ya hau ta, wani irin tsalle ta daka sai ta ji ta buge wani abu, a firgice ta dago, tsoro ya kamata da ta ga R-Lema, yana lulaya goshin shi don anan ta kaimai karo, ta tattaro nutsuwar ta tace "donAllah kayi hakuri, K'andagaru suka biyo ni, ban ganka a gabana ba, sannu kaji? rabawa yayi ta gefenta ya wuce ba tare da yace mata uffan ba, Mamaki ya turnike Nasiba, a baiyane tace "shi kuma wannan wane iri ne?".

*Malali, Kaduna*.
Chapter 28 · 0% Book details