← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 95

Sashe 87

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

8:10pm
Ko wacce ta samu gurinta a Mota, Motoci aka kawo sun fi 20, yawancin Manyan duk sun tafi, Mami da Aminanta sun wuce, yanmatan ne dama suka rage, Rafeeq da Seebi a bayan Motar Uncle Zaid, Miemee da Maalesh a gaban Motar, Usheey na motar wani friend din su Maalesh Faisal, tun farkon biki suka hade, kuma da alamu suna son junan su,
Nene ta shigo gidan, Da sauri tana murnan ga motoci nan basu tafo ba, dama sai da ta tabbatar ta sallami kowa a gidanta kafin ta fito, Daga dan Nesa ya hangota, a zuciyar shi yace "Neh-neh? ina take tunanin zata?" wata zuciya tace "Dinner"da sauri ya girgiza kai, In har ka bari Matar nan taje Dinner dinnan, to sunan ka sorry, zata kwafsa maka, ta bada kai gaban Friends dinka, zata ba ka kunya gaban Manya mutane, you have to stop her from coming, unless yiur name will turn to Apology" gargadin da zuciyarsa ke ma sa kenan, da sauri ya bude k'ofa yace "i'll be right back ya fice" ba su lura da ita ba, da sauri ya tare ta, ta yashe baki "Ahh su dunkum da manya kaya, ka ga kyan da kayi?" yayi Murmushin yak'e yace "ban Kai ki ba" Nene akaji dadi tace "Allah ko? Ni naga k'auna, ga motoci nan bari in dirje In shiga"Da sauri Feeq yace "No No Neh-neh, Mami tace " ki tafi mata da wasu kaya" Nene tace wasu kaya kuma dunkum?" ko dar yace ina jin kayan da zata raba wa mutane ne" suna ina? Yace Suna daki, kaje ka dauko min kar a tafi a barni" yace "wa zai tafi ya barki, ke ke da Ango" Nene ta ji dadi tace muje mu kwaso, suka jufa hanyar dakin Rafeeq, Rafeeq ya bude dakin shi, Nene ta shiga tace "ina kayan suke?" yace duba kewaye, aiko tana shiga yayi saurin fita ya sa Mukulli ya kulle K'ofar, ba ta lura ba illa ma cewa take "Ina kayan suke dunkum?" yana fita ya ma motovin gaban gida Signal da su fara tafia, aiko duka motoci suka kumna Motar su, da sauri ya hau tasu, Maalesh ya tada Motar suka bar haraban gidan fuk suna masu kunna fitilar motocin su, abun za kyau Convoy din ya hadu.
Haka su ka wuce NYSC hall, inda a Nan ne zaayi Dinner.
*******
"Bara'uba Salatin gwarawa" cewar Nene da ta fuskanci Dunkum ya kulleta a Dakinshi.
****
A Convoy suka isa har NYSC camp Hall, suna isa Maalesh ya kira Mom dinsa yace sun iso, Mom din ta sanar da MC Lubna Sufyan, nan MC ta buk'aci kowa da ya mik'e tsaye don shigowar Amare. Dj ne da Makadi(Mai Asharalle) nan da nan DJ ya sa wak'ar Nura M Inuwa na Amarya, Mom ta fita ta hada kan Amaren, Layi ne biyu, daya dogo na mata, daya na maza, in twos zaa shiga, Feeq da Seebi a tsakiya, ofcourse Miemee ce a gefen Maalesh su ne a gaba, Ushee kuma da Faisal a bayan su, Maalesh yayi kyau sosai, kayan shigen na Rafeeq ya sa, Abokan Ango Masu jiji da kai, duk ba zasu wuce shekarun Rafeeq ba, sai shan k'amshi sukeyi, ko don sun ga suna da kyau sun hadu ne oho, Kawayen Amarya kuwan sun sha kyau sun gaji, Anko suka yi na wani atamfa mai touches din Ja, sun daura Head Ja, ga kuma Amarya da Ango sunyi turquoise blue abun duk sai ya bada color, Mom tace da Miemee oya Yarinya na ku fara shiga da taku kunji?ta kashe ma Maalesh ido, nan suka fara taku sukayi hall din, aiko sauran suka bisu a baya, Fuskar Rafeeq ba yabo ba fallasa, shidai ba Murmushi yake ba, shi kuma ba daure fuska yayi ba, Suna shiga hall din Gaban Seebi ya fadi, ganin haduwar Hall din, ga Idon Mutane kan su, Hall din babba Ne kuma cike yake Mak'il, Rafeeq ya lura da ita, a hankali ya sak'alo hannun shi cikin nata, dumin hannun shi kawai taji a nata, da sauri ta kalleshi tare, ya kashe mata ido, a hankali yace "I got you" idonta ya kai kan Ummi, Mami Abbii da Daddy a chan gaba, duk kunya ya lullubeta, Zata zame hannunta Rafeeq ya matse hannun, ya ja ta suka cigaba da tafia har sai da sukaje suka zauna wurin da aka tanada domin su, kafin aka fara gudanar da Shirye shirye, Daddyn Maalesh aka bukata don bude taro da Addua, Alhaji Habib ya zo yayi Welcome Speech(Sannu da zuwa), sannan aka bukaci Baban Abokin Ango da K'awar Amarya su fito don bada takaicecen tarihin Ma'auratan, Muhawara ya kaure tsakanin Miemee da Ushee, Miemee tace "Oya Ushee tashi jeki yi Jawabi kan Amarya" Ushee tace "Tabdi, kinsan dai bazan iya magana gaban crowd ba, ai ke zakiyi, so kije dont waste time"Miemee ta harareta tace "don ace baki da hayaniya ko?" sukayi daria, Maalesh ya taso ya zo kusa da Miemee, suka jera sukayi kan Stage din a tare, abun sai ya burge Mutane.
Maalesh ya fara magana; "My name is Mahmud Ali Umar, and Rafeeq is a brother from another Mother, we've been together for 20years, Rafeeq is a•••••••• nan Maalesh ya shiga koda Rafeeq tare da mai Fatan Alheri, Rafeeq ya taso ya rungume Maalesh tare da bubbuga bayan sa ya rada mai a kunne "thank you brother".
Miemee ta fara bada bayani kan Seebi, ta fadi kyawawan halaiyarta ta kare da mata fatan Alheri" aka tafa musu, MC tace kafin su tafi sai sun taka rawa, nan Surajo mai Maalesh ya fara wak'e Malesh babban aboki, da Maryam Miemee yar gayu, sin dan taka zasu koma MC tace da su "Are you a couple?" Maalesh yace "yeah we are" tace "You suit eachother" sukayi Murmushi aka tafa musu suka koma mazaunin su.
Aka gayyaci Ango da Amarya a fili, Marok'i sai kirari yake ma Ango, Mom ta hau sama don Rafeeq da Seebi sunki tashi, Ita kunya, shi kuma be son hayaniya, sai da Mom ta je ta sauko dasu, Wannan karon karon Dj ne, Wak'ar Work-Rihanna ft Drake aka samu su, dukkansu tsaye sukayi, ba me rawa, Mom ta rada ma Feeq a kunne Spray her, Ta wuce ta zauna aka barsu su kadai a fili, hannu ya sa cikin Aljihu, ya ciro bandir din1k ya fara lik'a mata, kanta a k'asa, ya dinga spraying, Yana mata liki'i, nan Daddy da Abokansa suka zo suka lik'a musu kudade masu yawa, gajiya Rafeeq yayi, ya kama hannun matarsa ya ja ta suka koma mazaunin su, nan aka ba Abokan Ango da Kawayen Amare fili suyi rawa.

Tagumi ta rafka hannu bibiyu tana tunanin irin dukan da zata ma dunkum idan ta samu ta fito, ita zai ci ma fuska? Don kar taje lanchin (luncheon)din shine zai kulle ta don bakin hali. Agogon dakin ta daga kai ta kall 9:15, ji tayi ana bude k'ofar dakin da Mukuli, da sauri ta mik'e ta la6e bayan labule don yau watan cin uban Dunkum ne ya shigo, fitowa tayi daga Bayan labule tace "Zaidu bawan Allah, kaine anan bakaje gun patin ba?" da mamaki yace "Nene, me kikeyi anan?" tace "ba wannan shegen yaron bane ya kulle ni a dakin don ya tsane ni, wai don kar inje partyn" Zaid yace "Wa kenan?" cikin fada Nene tace "Wa fa banda fitsararen Danka Dunkum" Zaid yace "shi Rafeeq din ya kulle ki? Saboda me to?" tace "Af Sabida ya tsanan mana" "aa Nene ki bar cewa Haka, bari in dauki abu mu tafi" ta yi Murmushi tace "Yawwa Zaidu Bawan Allah" da sauri Zaid ya bude Wardrobe ya ciro wata Envelop yace "muje Nenenmu, kai Nenen mu kinyi kyau wallahi" dadi kashe Nene tayi ihun murna tare da juyi tace "Ai nasani wallahi, kaima kayi kyau Sosai dama Zainabu ta na nan sa ta ganka" yana tafiya tana bin shi a baya yace "ai ta ganni" tace "ta ina? Ko ta zo ne? Yace " Aa Wallahi, ta Video Call, itama ta sa na makara" Nene tace "Miye Bidi'o kwal?" suka shiga Mota Zaid ya fara mata bayanin Video Call.
Chapter 87 · 0% Book details