← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 95

Sashe 86

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

A kan idon Nene Mami ta ba Ummin Seebi gate pass da yawa tace "gashi ke da mutanen ki" Ummi tace yanzu sai munje?" Mami tace "Ehmana, duk zaaje har Alhaji da mutanen shi zasu, kinga kema harda Abii dinsu zaki" sukayi daria duka.
'Toh wadannan takardun da ake rabawa na meye?" Mami da Ummi suka juya ta inda sukaji Muryar Nene, Nene ta k'araso tace "ko bakuji ba?" Mami tace "Gate Pass ne" Nene ta yatsuna fuska tace "meye haka nan?" Mami tace "Kati ne Nene, na shiga wurin Dinner, idan baka nuna ba, ba zaa barka ka shiga ba" Nene tace "ina wai?" Mami tace "Dinner kamar Walima aka hada, zaa hadu duka a ci Abincin Dare don murnan Biki" Nene tace "Tab, Munafurci ya sa ba a a gaya min ba? Ya ake abu ne ba a sanar min?" Ummi tace kiyi hakuri, dama katittikar mu ne nanz shine yanzu zan kai gida a shirya a tafi" Nene ta harari surukar ta tace "bani su nan" da sauri Ummi ta mik'a mata IV's din duka jiki na rawa, Nene ta zaro daya ta mik'a mata, tace "muje gidan, zan ba wamda ya dace yaje don kar muje su ba mu kunya, sai wanda yayi wankan Suwaga(Swagger) zaije" duk sukayi Daria, Mami tace "to Nene ku je ku shirya da anyi Sallahr Ishai zaa tafi, Nene tace bari mu je da sauri suka fita ita da Surikarta Ummi.
Mami kuma ta wuce Parlorn Daddy inda aka ma Nasiba Makeup, Sanye take da Turquoise Blue Wedding gown, da dogo Veil dinshi wanda Houseofkaya suka dinka mata, Rigar ta hadu iya haduwa, Aneesa ce ke koya ma Nasiba yanda zatayi tafia gun dinner din, Mami ta shigo da Sallama, Nasiba tayi saurin Sadda kai, Mami ta isa gunta ta rungume Nasiba tace "MashaAllah Seebi kinyi kyau sosai"Murmushi kawai tayi, Wayar Mami yayi k'ara, ta dauka " Yeah Okay, we are ready as well" Mami ta kalli Lynaz me Makeup tace "Thank you Lynaz, you've transformed my daughter" Lynaz tace "thats my job maam, we bring out the beauty in you" Mami tayi Murmushi suka tarkata kayansu Aneesa tace "i'll show you the way out" Mami tace daga nan ki kira min Wayr Maalesh, Rafeeq yazo ga EventsUnlimited(masu hoto) nan sunzo, yazo ayi Post wedding pictures kafin a tafi dinner din, Aneesa tace "Ok Mami" Mami ta tsura ma Nasiba kyau, duk kunya ya kamata ya sadda kanta k'asa, Mami ta kamo hannunta tace "Nasiba Wallahi ina sonki ina jinki kamar Rafee'ah, kinyi kyau sosai, Allah ya Albarkaci Rayuwanku duka" a hankali ta amsa da "Amin".
Ta k'ofar baya aka shigo da Masu hotunan, don kar a dauki hankalin mutane, aka bi dasu ta baya suka hau sama Parlorn Daddy. Bayan gaishe gaishe suka hada kayan hotunan su. Mami ta fita waje don kiran Rafeeq ko Maalesh ta ko ci Sa'a wayar Rafeeq ta shiga, " "Hello Feeq kana ina? Mam ina tsakar gida, Oya ka shigo ciki ka hayo Sama, ga Eventsunlimited nan, kazo ayi Postwedding pitures, ya marairaice kamae zaiyi kuka, Mami ta ya zan shigo, Mutane da yawa, tace "ta baya fa zaka shigo" "ni Mami i cant" tace "Ina Maalesh ya rako ka mana?" Mam Lesh yaje tattaro Friends dina yanda zasu a kwashe mutane a tafi at once" tace "Alright gani nan zuwa in taho da kai".
Ta sauka kasa ta ga Rafeeq, sanye yake da shiga irinta Nasiba, manya kanya Turquoise Blue ga hularsa yayi kyau fiye da tunanin me tunani ga wani k'amshi yana zubawa, Mami ta rungume shi tare da mai kiss a kumatu, tace " Yaro na ya girma " Sake rungumeta yayi ta ja hannunshi har Sama ta sada shi da Parlorn Daddy ta turash ciki. Sandarewa yayi da ya hango Sanyin idaniyar shi daga chan gefe ana kashe mata hoto, Kallonta yakeyi cike da so da k'auna, ya shagala da kallonta sai ji yayi Me daukar hoton tace"The Groom is here, come over here" Hankalin Seebi ya koma kan Rafeeq, gani yakeyi Yafi ko wa Dace tunda yana da Seebi, itama hakan ne, don yau ya mta kyau matuk'a, a hankali ya taka har gunta yana mata kallo kasa kasa, ta sadda kanta k'asa ya sa hannun shi ya dago fuskarta ya kai bskinshi kan kumatun ta ysyi kissing a hankali, daburcewa tayi Lokaci guda ya sa hanayenshi duka hya ya rike kafadunta, idonta a runtse ta bude su a hankali, Cikin muryar rada yace "Calm down baby, i got you" Me hoto tace "Oya Romeo Shall we?" kao Kawai ya gyada mata, nana aka fara kashe musu hotuna kala kala.
Chapter 86 · 0% Book details