← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 95

Sashe 68

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Fitowar su Lectures kenan, sun nufi busstop, Miemee tace "Kar ki ga don kina gidansu kice zakiyi tolerating shit dinta, Wallahi i wont forgive you in tace miki 'a' bakice mata 'b' ba, Usheey tayi daria tace " Sai da haka don na lura Aneelema na da izgili" Seebi tayi murmushi "ku kwantas ba ruwana ma da ita balle ta shiga sabgata, ban ma bada chance din mu hadu, akwai komai a dakin da aka bamu, to fita ma be dameni ba balle mu hadu ai ta chechekuce" Miemee tace "Oops, ai na ma manta da The Boss, Nenenmu bata daukan Nonsense, ba zata yarda ko hararki ayi ba" tare sukayi daria. Jin horn ya sa su juyawa, ganin Motar R-Lema ya sa Miemee tamk'e fuska, ga Hamma kuzo mu shiga ya ajiye mu" cewar Seebi, Miemee tace "aje lafiya ni bus zan shiga gata baa cike ba" Seebi tace "haba mana Miemee love kizo muje" tab kinsan dai idan ya gaya min daci zan gaya mishi madaciya ko? Usheey tace ba ma zaayi haka ba, mu dai mu kama kanmu in mun shiga, da k'yar sukayi Convincing miemee. Zuwa tayi ta bude k'ofar gaba taji shi a rufe gagam, Kasancewar Motar Tint ce bata ganin na ciki, Usheey tace kizo baya su biyu ne, Suka shiga bayan a tare. Maalesh ne ke tuk'in sai Rafeeq a kujera me zaman banza, Ya Maalesh ina wuni? Ushee ma ta gaidashi, ya amsa fuska a sake da "Lafiya lao yan makaranta ya School? Suka amsa mai, "Hamma ina wuni?" dauke kai yayi kamar be ji ta ba, bata damu ba don inda sabo ta saba. Maalesh ya kalli Miemee ta side mirror da ta hade girar sama da ta k'asa, yace "Ammata ba gaisuwa?" Seebi dake tsakiyarsu tayi saurin muntsinin Miemee tace "Sannun ku?" murmushi yayi yace "Sannunmu, meyasa kike daure fuska? Ko lectures ne ya bata miki rai? Ko rana din ne? You are beautiful, dont let anything ruin your day Okay? Gajeren Murmushi Miemee tayu, Ushee da Seebi suka matse hannun juna irin suna sonyin gulman nan amma ba chance, haka Maalesh ya cigaba da tuk'i Binibini sai ya kalli Miemee ta mirror, yana sakin murmushi, sometimes kuma ya tsomata cikin firar su da Seebi, Rafeeq najin Maalesh ya lura da taketaken shi amma be ce komai ba, don ya san Maalesh da playing Mata, kuma ya zaayi yana son Seebi kuma yana flirting da Miemee yayi dan guntun tsaki. Wayar shi ta hau ruri. Ya dauka ya soma magana kamar baya so
"Kun wuce din? Ina Angel?Okay Safe journey". Ikon Allah inji Miemee a ranta, shikuma haka yake 3sentences har ya gama waya lallai "Uncle Zee din ya wuce ne?" cewar Maalesh, "Uhm" kawai Rafeeq yace. Haka suka kai Miemee har gida, Miemee tace thanks ta bude motar, wanda ma ta ke sha ma maganin be san tanayi ba, Maalesh yace "excuse me" ya bi bayanta duk suka bishi da ido, yace "Beautiful, Allah sa ban bata miki rai da surutu na ba? Tace " No kar kadamu" yace "no na damu" tayi murmushi tace "Ka shiga ku tafi suna jiranka" ya dan marairaice yace "DonAllah in amsa numbernki gurin Nasiba?" tayi murmushi tace "ba laifi" "awwn thanks beautiful ya kashe mata ido tare da komawa cikin motar" ba wanda ya ce mai k'ala ya ja motar suka bar Unguwarsu Miemee.

Sai da suka gama Fira da Baba Maigadi wanda duk rabin Firar gardama ne tace kai ni bari in shiga ciki in dan yada kafadata kafin Seebi ta dawo, Baba Maigadi yace "toh Aminene ta" Nene tace "Wallahi kwalelenka na fi karfinka, ni sai me lamozin (limousine) sukayi Daria duka, ta wuce, sai da ta shiga ciki sannan ta tuna da Sansamin Zogalen da ta siyo don ta shuka, tace " barin dauko in shuka kafin na mance" ta shiga ta dauko, ta wuce baya inda take ganin shukokin flowers da kayan itatuwa (Garden) tana waigawa taga gatari tace "yauwa ta kwana gidan Sauki" ta dauko daga gefe ta fara hak'a rami, ji tayi ta finciko da wani abun, toufa tace "a hankali tare da duban abun me kama da k'ulli, tace "wannan k'ullin na meye? Ta dauka ta warware a hankali, laya ce da yar takarda an rubuta ~Aisha Habibu~ da larabci an sokeshi, Nene tace "wacece Aisha kuma?wata Zuciyar tace "ko sunan Mamin Rafeeq ce?" tayi murmushi tace "Haba biri yayi kama da mutum, ni na san wallahi ba a banza ba Saude, babban kuskurenki daya da kika bar Nenen Seebi ta zauna a gidan ki, a hankali duk zan warware duk wani muggun tuggu da kika k'ulla, mafarin kenan, da ni kike zancen.
*********
Rafeeq ya kalli Maalesh dake kwance rigingine kan gado yana waya da Miemee bayan da suka sauke seebi ya amsa numbern a gunta, har ya gama ya dago Rafeeq na lura dashi, chan ya cire baki yace "Lesh, me kake nufi ne wai kai?" Maalesh ya dan kalleshi da mamaki yace "guy bangane ba, me kake nufi?" dan guntun tsaki Rafeeq yayi yace" ka amsa numbern wannan yarinya mana, yanzu kazo kana waya da ita" Maalesh ya dan bata fuska yace "do you have a problem with that? Rafeew ya harzuk'a yace " Tun farko mesa zaka ce kana son Naseebah idan kasan you wont ask her out ba, why? Na baka number don kace min kana sonta har kace aurenta kake sonyi, ko dama yaudara ce? meyasa ba ka fada mata ba? Kullum kana damunta da waya, kana kasheta da words dinka, ka sata tana ta jiran tsammani, and yanzu don cin fuska ka tambayeta numbern friend dinta, Seriously Lesh?Why? Tell me why?" Ya karashe maganar shi a dan fusace, Maalesh ya dan kallo Rafeeq shima a fusace yace "Why Rafeeq? You want me to tell you why? Fine! Its Because of you Feeq, i didnt ask her out because of You, You R-Lema" a firgice Rafeeq yace "Bangane ba, me kake nufi saboda ni? Kar ka manta i gave you her number" darian takaici Maalesh yayi yace "Eh ka bani numbern ta saboda baka san your true feelings for her ba, ba ka san cewa she's your Happiness ba, you are blindloving her, why cant you realise it? Kana mata wani makahon so da kai karan kanka baka san kana yi ba, You love her Feeq" Cike da tashin hankali Rafeeq ya wurgar da Roban ruwan, ya tashi a fusace ya cukume rigar Maalesh, yace "Inji uban wa yace maka sonta nakeyi? Are you crazy Mahmud Ahmad? You know me better than anyone, No girl is worth my love, I cant fall for her, cant fall for any girl, Ba macen da ta isa in so ta" Maalesh ya katse shi "Why? Saboda kai ba mutum bane? Sabida kai baka da Feelings? You are inhuman? Or your Humanity is shutdown, you think you dont have right to love? Who are you to say you cant love anyone? Rik'on da ya mai ya sake matse mai wuya cikin daga murya yace "duk me zakace kace , ban damu ba, ba yarinyar da ta isa in sota because I'm Rafeeq Freaking Lema"

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Get Well soon Aunty (Maman Sultan)💘. Allah ya baki lafiya Amin.

Pg5⃣3⃣
Chapter 68 · 0% Book details