Sashe 55
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tabbas Sihiri Gaskia ce, Al Qurani Magani ne kuma Waraka ce, Haka yau Alhaji Habib ya tashi k'arfe ukun dare kanshi na juyawa, tun shekaran jiya yake tashi uwar haka yana ganin jiri, ya dafe kai ya bude idonshi a hankali, gani yayi dakin na juya mai, Sallalami ya fara, ya dinga karanta inalillahi wa ina ilaihir rajiun, har ya samu sa ida, dakin ya daina juya mai, wasu tunane tunanen da be san ko na meye ba suka fara mai reto a k'wak'walwa, haka ya k'arashe daren cikin juye juye bacci ya mai tawaye har Assalatu, haka ya daure da naunauyan ido yaje Massalaci, ga mamakin shi Rafeeq ya gani sahun gaba, anan idar da Sallah Daddy ya samu Liman ya sanar dashi abun da yakeji tun daren shekaran jiya, Liman yace "kana da Hawan Jini?" yace "Aa ban dashi ko jiya naje Asibitin Dr Dara an min Awon BP, Diabetes an tabbatar banda komai, Liman yayi shiru yace " toh Alhaji ko dai sammu aka maka, ko ana so a cimma wani buri a kanka" Alhaji Yayi daria, shi be yarda da Asiri ko wani Sammu ba, yana daria yace "yo ni wa zai min wani sihiri?" Liman yace "Uhm Uhm Alhaji, kar kayi saurin cewa haka, kana da Abokan Gaba, Mahassada wanda ba sa son Cigaban ka, nidai shawaran da zan baka ka ziyarci Islamic Chemist" Alhaji yayi shiru, wani ga6a na zuciyar shi ta yarda da fadin Liman,/yace ko kasan wani Islamic Chemist din da zaka turani? "Kaje Arriyadh Islamic Medicine, yana nan gun Filin Polo ta wurin Tasha " yace to InshaAllah zan i gurin nagode k'warai" sukayi musabaha, Rafeeq ya matso kusa da Alhaji Habib da murmushi kan fuskarshi yace "Daddy Ina kwana?" wani farin ciki ya ziyarci Alhaji Habib, rabon da ya samu irin gaisuwar nan gurin Rafeeq har mantuwa ta mance, ya amsa da "Lafiya lau Ibn Zaid, ya karatu" ba a jima ba Rafeeq ya amsa mai da "Alhamdulilah" haka suka jera da Daddy har suka shiga gida.
******************
"Kace Sunanka Alhaji Habib Lema?" cewar Mallam Usman, Daddy ya gyada kai yace "eh nine" Mallam ya tsura mai ido, a ranshi yace "tabbas shine wanda Mallam Muhammadu da diyarshi suka zo neman magani don shi da danshi", ganin yanda Malamin ke kallon shi ya sashi tsarguwa amma beyi magana ba, Mallam ya dan nitsa yace " Kace kana jin wasu abubuwa game da rayuwarka, kana iya min bayani yanda kakeji?yace "eh to, a shekaran jiya ina bacci wurin k'arfe biyu naji kaina ya min nauyi, na tashi na jini kamar wanda aka ma dukkar tsiya, tun daga lokacin naji bacci ya kaurace ma idanuna, jiya ma abun da ya faru kenan, yau ma haka, na yau ya fi na kullum, don yau harda wasu tunanetune nake tayi" Mallam yace "haka ne, kamar ya tunanin?" yace "Kawai ina tunanin yanda naga abubuwa sun sauya, kamar Matata ina tunanin ya akayi na aureta, nasan dai cewa Matata ce, amma bansan ya akayi na aureta ba, in tak'aice maka, bansan ya akayi abubuwan da suka faru suka faru tun bayan Auren mu ba, kawai ina ji a jikina Something is missing" Mallam yayi Murmushi tare da gode Allah ya fara dawowa hanya, yace "Matan ka nawa?" "Matata daya, ka taba auren wata kafin ta yanzu ko bayan ta?" yayi nisa yana san tunano wani abu kafin yace "aa, ban taba aure ba, Saude kadai ce Matata" Amma kana da d'a Rafeeq, Saude ce Mahaifiyar shi? Shiru yayi alamun yana son tunano wani abu, chan yace "Maman Rafeeq ta rasu" Mallam yayi shiru a ranshi uace wato an saka mance ta kenan, bakomai komi yazo k'arshe. Wayar Mallam ce ta katse mai hanzari, da sauri ya dauki wayar kamar jirarta yake, yace "Assalam Alaikum, muna lafiya ya Iyali?" "toh tazo? Toh ce mata ta shigo kawai" Mallam ya ajiye wayar ya saki Murmushi kafin ya kalli Alhaji Habib yace"Alhaji kayi Sakaci da Ibada, kayi Sakaci ga kai kukan ga Allah, tabbas kana tare da sihiri na dan tsawon lokaci, Amma InshaAllah komai ya zo k'arshe, kar ka gaya ma kowa abun da kakeji, kawai ka dage da Addua, nikuma akwai wani hadin maganin da zan maka, in ka tsare ibadunka kayi amfani dashi to waraka zata samu, zaka yi filling empty space din da ke Cikin zuciyarka" Alhaji Habib cikin kunya yace "Nagode Mallam, InshaAllah zanyi yarda kace" Sallamar ta ce ta katse mai tunani, ta shigo kanta a k'asa, Mallam yace har kin iso? Ke da zaki shigo kai tsaye amma sai da kika kira baban ki da ke wani gari, Murmushi kawai Nasiba tayi ta gaida shi, ya amsa, yace "Abbi dinki ya ce ko Jarkan Ruwan za a k'ara muku? Wanchan har ya k'are?" ta gyada kai tace "eh ya k'are, da yake har abinci ake misbi dashi " yace "to ya akwai Cigaba?" tace "Wallahi Sosai" yace "toh Alhamdulilah, ya cigaba da shan Ruwan Adduar da Maganin nan" ya tashi ya tafi cupboard inda ya ke ajiye magunguna.
Waigawan da zatayi taga Mutum zaune ya tsura mata ido, gabanta ya yanke ya fadi, Shakka babu wannan shine Alhaji Habib Iro Lema don wani kaman da sukeyi da Rafeeq, to me ya zoyi nan? Ta tambayi zuciyarta, Tun shigowarta ya tsura mata ido, yanayin maganarta yana mai kama da na Marigayiya diyarshi Rafee'ah, haka kurum yakeji kamar da Rafee'ah yake tare, sulalewa tayi har k'asa tace "Ina wuni?" Murmushi daddy ya mata yace "Lafiya lao Diyata" haka kurum taji dadin ganinshi, Mallam ya dawo da Jarkan Ruwa, Mallam yace "Ai Alhaji na duba yanzu naga ashe ba ragowan irin hadin da zan maka" Alhaji yace "Ashha! Sai nan da yaushe zaa samu?" yace "nan da awa uku, idan na gama da marasa lafiya sai in samu natsuwa in hada maka" Alhaji yace toh gashi ana jirana a office, ni da fitowa sai dare, kuma ka gargadeni da kar in gaya ma kowa,balle in turo a karban min, ko kuna kaiwa daren?" Nasiba tayi tsulum tace "Daddy zan kawo ma Gida" da namaki ya kalleta yana murmushi yace kinsan gida na ne? tace "Eh na sani, yana wurin Bayan gidan Rahusa" da mamaki ya kalleta yace "ya akayi kika sani?" tayi Murmushi tace "ni k'awar Marigayiya Rafee'ah ce munyi Islamiyar mu daya" Daddy yayi murmushi yace "Ashe diyata ce, toh nagode Allah miki Albarka kinji" ta yi Murmushi tace "Amin" nan Mallam yace hadin Dubu 7 ne, daddy ya biya harda ruwan Jarka Nasiba, dubu 6, haka ya lalle dubu 13 ya bada, Nasiba tayi Godia. Mallam yace zai mata bayani idan tazo ta mishi bayani, sukayi Sallama Daddy ya bar gurin, Nasiba kuwa tace "Mallam Baban Rafeeq ne fa wanda muke amsar ma magani" Mallam yayi murmushi yace "ai tun danaji me ke damunshi na san cewa shine" Saukar Kuranin da mukayi ne ya karkato shi har yazo nan" Nasiba tace "Allahu Akbar" yace yanzu ki tafi Gida, wurin k'arfe hudu sai kizo ki amsar mai" sukayi Sallama Nasiba ta wuce gida kamar an mata wahayin shiga Aljanna.
Knocking yaji anayi a k'ofar shi, a ranshi yace who could it be?Maalesh ya dawo ne? Mik'ewa yayi ya zira takalmin shi ya nufa kofar, ya bude, tsaye ya ganshi ya k'ara Haske da kyau, ga cikar kamala kamar kullum, beyi tsammanin ganin shi a wannan lokaci ba, murmushi me hade da mamaki ya keyi, shima na bakin k'ofar Murmushi yayi yace "Hello Son" A hankali Rafeeq yace "Uncle Zaid" tare da rungume shi, shima Zaid din rungumeshi yayi yace "I've missed you so much son" a nitse yace"Meyasa baka gaya min ka dawo ba? Yaushe ka iso? Ta Abuja ka sauka?, Ya aikin?" mamaki ya hana Zaid amsa tambayoyin da Rafeeq ke jera mai, tun shigowar shi ya lura da changes gun Rafeeq, Rafeeq me magana da k'yar amma yanzu shike mai wannan tambaya kan tambaya? Lallai an samu cigaba, Zaid yayi murmushi yace "jiya na dawo, ta Abuja na sauka, immediately na dauki Drop zuwa Kaduna, yau kuma na taho Katsina" Murmushi Rafeeq yayi yace "Ina Ayman? Is she okay? I've missed her" "ai kasan inda zaka kira kaji ya take, me ya hanaka kiranta?" nan da nan duk annuri Fuskar Rafeeq ya dauke ya sha mur, ya koma kan gado ya zauna (Au baka sauko ba?) Zaid ya san ya 6allo ruwa da ya ambatar ma Rafeeq Mami, Murmushi yayi ya dawo kusa dashi ya mik'a mai Key yace "Je ka mota, i have a bigger suprise for you" murtuk'e fuska yayi, don Uncle Zaid ya 6ata mai Mood dinshi da k'yar yace "What is it? Sa mai mukullin yayi a hannu yace j"e ka bude ka gani" talalman shi ya zura ya futa ya bude motar ta gaba, haske ya bayyana a motar don Maghrib ya k'arato, Karaf idon shi yayi kan wata yarinya kwance bayan Seat tana bacci, da murna ya bude bayan seat din ya cicibota ya rungume wasu zafafan hawaye suka soma zuba, a hankali yace "Ayman-Rafeeah" Zaid ya karaso tare da bubbuga mai Baya, Rafeeq ya kalleshi yace "Thank you" ya koma daki da Ayman rungume kan kafadarshi, ya kwantar da ita. Wani farinciki ya lullube shi, yau ji yake kamar yana tare da Rafee'ah Habib Lema ne. Zaid yace "tagaji ne, bata ta6a fita Rigachikun ba, yau ne rana ta farko da tayi tafiya me Nisa" Rafeeq yace "she must be tried, thank you for coming with her" Zaid yace "kawai nace if Hamma wont come to see her, why cant she come see Hamma?" Rafeeq ya dan kawar da kanshi, yace "its complicated, shes here already, ka daina damuwa" girgiza kai kawai Zaid yayi.