Sashe 85
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Massalacin Commasie Cike ciki da bai, har toshe Hanya akayi saboda chunkosa, Manyan Mutane k'usoshin k'asa, yan Siyasa, Yan Kasuwa Yan Uwa da Abokan Arziki zaune Cikin Massalacin, Abbii na gaisawa da mutanen shi, suna mai Murna, Liman yazo, ana jiran zuwan Waliyyin Ango, har 12:30 ba alamun su, Daddy cikin bacin rai ya ciro Waya ya danna kiran Uncle Zaid, yana dauka Daddy ya rufe shi da Fada, kai Zaid kar ka maida mu k'ananun mutane mana, ka tara mu a nan, ka k'i zuwa, kowa fa na da abun yi haba" daddy na iya jiyo Sautin Murmushin Zaid, yace "Kwantas Yaya, i had to make sure My Son is looking Good, yanzu dai juyi daman ka, gamu muna kallon ka" Da sauri Daddy ya kallo Daman shi, Aiko sai ganin Zaid yayi sanye cikin Shiga ta Alfarma, Babbar riga ce Milk color, Rafeeq a kusa dashi wanda ke sanye da Farar Shadda da ta sha Bakkin Aiki harda Baban riga, sai Maalesh da ya sa Skye blue Shadda shima da Babbar rigar shi, Wani farinciki ya ziyarci Zuciyar Daddy, ya dade be ga tilon danshi cikin wannan farin ciki ba, Dukda fuskar sa Murtuke yake, kallo daya zaka mai kasan yana cikin farinciki Mara Misaltuwa, Tafiya sukeyi cike da Tak'ama da Isa, suka je har gaba suka samu wuri suka Zauna bayan Zaid ya nemi Afuwan mutane na Latti da sukayi.
Liman ya fara da cewa Ina Waliyyan Maauratan? Su matso gaba, Uncle Zaid da wani d'an k'anin Nene suka matsa Gaba, Aka buk'aci Sadaki, Zaid ya sa Hannu cikin Aljihu ya ciro bandir din 1000, dubu Dari, bayan anyi yanda Addinin musulunci ta tanada, nana Dubannin Mutane suka Shaida Auren RAFEEQ HABIB LEMA da Amaryar sa NASIBA MUHAMMAD Bisa Sadaki naira dubu 100 lakadan ba ajalan ba, Rafeeq ya ji hawaye a kuncinshi da sauri ya goge ya zaro Wayarshi tare da tura mata Text, nan aka shiga gaigaisawa ana taya juna Murna, Rafeeq ya ji dadin ganin Old Friends dinshi a gun Daurin Aure, na University dana Secindary, yasan aikin Maalesh ne, daga nan suka zarce KATSINA MOTEL inda zaayi Reception.
Tun Safe suka dawo gidan Nene, Gida ya cika Makil, tun wurin 8 aka fara zuwa yinin biki, Nene tayi kyau abunta cikin shiga ta Lifaya, sai wani kankanba take ma kawayenta tsofi irin ita jikarta ta dangwalo arziki, ana ta ba ciki hakkinsa, Abinci sai wanda ka zaba, Amare na rawan kidin kwarya, Nene na tayasu, Nene ta kalli Miemee tace "Miemee Yar gayu je ki hankado min Seebi yanzu" da sauri Miemee tayi hanyar Dakin.
Usheey ta mik'o mata Wayar ta, don ta ji kamar Alamun shigowar Sak'o, tana duba wayar ta ga BABY ne, da sauri ta bude Sak'on *"YOU ARE MINE"* abunda ke ciki sak'on kenan, wani Farinciki ya ziyar ce ta a hankali ta zame ta yi Sujjudushukur don nuna Godiar ta. Usheey tace "yadai? Cikin Sanyin jiki tace "An daura" Miemee ta shigo k'uryar tace "wai me kukeyi ne? Nene tace kar ku bari ta iske ku Wallahi, ku fito bak'i nata zuwa" Usheey tace "Sorry Sallah mukayi" Miemee tace donAllah ji an daura miki Dankwali kin kwance" Seebi tace "Alwala fa nayi" Miemee ta harareta ta hau gyara mata dankwalin kanta, suka fita Masu kidan kwarya na ganinsu suka fara wak'ar *giringibishi*.
Yinin Bikin Nene yayi Armashi Har wurin bayan Laasar ba a bar zuwa ba, anan ne aka kira Nene aka sanar da ita 'yan daukar Amarya zasu zo, Nene ta lek'a chan k'urya ta ga Seebi rakube tana Kuka kamar ranta zai fita, zuviyar Nene ta karaya, ta dai dake tace "Ke kika ce kina so, da ba kice kina so ba da ba a baki dunkum ba, to kuka na me? Tashi muje inkai ki gun Babanki ya miki fada da Nasiha" Aiko Seebi ta sake fashewa da kuka, ta ba Nene tausayi sosai, nan ta samu ta shiga lallabata har ta ja ta sukayi Parlo inda Abbii da Kawu Magaji ke zaune, Nene ta aika aka kira mata Ummi, aka gurfanar da Seebi gaban Abbi, Nene tace "to Mahammadu ga Seebi nan kai mata fada" Abii yayi hamdala yace "Toh Seebin Nene Allah yayi yau na ga Aurenki, Seebi, duk me hankali zai yi duba ga lamarin Aurenki, kin shiga rayuwarsu a Matsayin wata Haske ba tare da ke kanki kin sani ba, Haduwarki da Rafeeq har zuwa yau itace K'addaraki, abubuwan da kikayi domin shi, shine Jarabawarki, ki kasance me boye sirrin Mijinki, Abubuwan da suka faru, na dadi da na rashin Dadi, hakan ya zama ishara gareki,, ina Miki gargadi da ki rike gaskia da Amana, kin taimaki Mutanen nan, suma sun taimake ki, Suna sonki Sosai, Kar ki zama butulu, ki kaunce su da zuciya daya, na sanki da hakuri, ki kara a kan wanda na sanki dashi•••• Nasiha me ratsa jiki Abii ta cigaba da yi ma 'yarsa, tana kuka yanayi, Ummi nayi, sai da ya gama Nene ta sa Ummi daura mata kan na Abii, Kawu Magaji ya mik'a Ma Seebi Sadakin ta yace "ga Hakkinki" Seebi kasa amsa tayi sai dai Nene ta sa hannu ta amsa, suna cikin haka sai ga yan daukar Amarya sunzo, Suna Guda sosai, dangin Mami da dangin su Daddy yan Azare ne sai Mom din Maalesh, Bayan an gama yan surutai aka basu Amarya Nene ta yana Lifayar ta zata bi bayansu, wata abokiyar wasanta tace "Kai Aminene ba dai binsu zakiyi ba?, ke fa ce Uwar Amarya" Nene tace "Yo saboda me? Ai wallahi kafata kafar Seebi in gaya miki" ta bi bayansu da sauri.
Gidan Habib Lema akayi Da Seebi, dama chan zata fara Zama cewar Uncle Zaid saboda dalilin shi daga shi sai Rafeeq suka sani, sun dai ce ma Mami tun Kafin ayi Bikin nan zata zauna, saboda haka nan akayi da Amarya, ba abunda ke tashi sai Guda, Sama akayi da ita aka kaita Dakin Mami, kan tsakiyar Gadon aka ajiyeta, inda take kuka a Hankali.
***********************
"Sweet Zee ka huta kaji? Bana so wata ta ganka ta lik'e maka a Dinner dinnan a Son" Cewar Aunty Zee da ke kwance rigingine tana waya da Mijinta, Uncle Zaid yayi dariya yace "Cute Zee ki kwantar da hankalin ki, ba wacce zata ganni, kowa ya san nima fa Ango ne, dont worry kinji Cute Zee? I'll keep myself for you alone, I love you so much, Gobe First thing in the Morning zan taho, i cant wait to set my eyes on you" Murmushi me sanyi tayi kalamanshi sun kwantar mata da Hankali, Sallama sukayi bayan ya shaida mata zai dinga tiro mata Pictures da Videos ta Whatsapp.
"Beautiful Akwai Sauran Gate Pass a gurinki" Miemee tace "Handsome Wallahi duk sun k'are, Wasu Friends din Seebi 'yan Zauren Biebee Isa da Miemee Bee Novels group sukazo kuma duk na rabe musu Gate Pass din" "and kuma dukkansu sai da kika basu?" Miemee tace "duka Wallahi,Friends din Amarya me, daga wurare daban daban, garuruwansu nesa da na kusa suka zo, they mean alot to Seebi, kaga dole a sama musu gate pass" "Alright ba Matsala, barin je in shirya Ango, Please ki cema Friends dinku su shirya, Immediately Isha zaa zo ayi kwasa daya a tafi, kinsan abun ba African Time, saboda harda su Daddy da Friends dinshi, so Everything has to be on time" Miemee tace "Alright Handsome baka da Matsala, ana chan ana Makeup din Amaryar, mu kuma a shirye muke ku muke jira" "Alright bae, i love u". Me too bye.