← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 95

Sashe 75

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ki kirashi donAllah ya maidaki Gida Seebi, ba fa ki da lafia, baki ta dan cije alamun tana dan jin zafin ciwon tace "Ku bari kawai, zai daina with time, haba abunda an riga da an saba" Usheey tace "Tab, dama ana sabo da ciwo? tace "bari nidai sai na kirashi in ma Zagina zeyi yayi, ta dauki Wayar Seebi ta latso Hamma na ta kira, Ba yanda Seebi zatayi da Miemee da Usheey. Yayi ringing har ya katse bai dauka ba, Usheey ta sake kiran layin shi, a ringing na 3 ya dauka, yabkara wayar a kunne ba tare da yace komai ba, Usheey tayi saurin cewa "ina wuni?" ya danyi jim, wannan ba muryan Naseeba bane, yace "Yeah" "um um dama Seebi ce bata dan jin dadi, tunda safe take fama da ciwon ciki har yanzu, kuma lectures zamuyi 4-6 tace zata tsaya amma ya kamata ace ta sha magani ta dan huta a gida"cike da damuwa a ranshi yace "Oh Allah why is she sick" a fili kuwa cewa yayi "kuna ina?" da sauri tace "Bayan theatre" dif ya kashe wayar, Miemee tana na Usheey daria tace "ai gwara da ke ce kika kirashi, dani ce ya katse ma waya da yaji ba dadi" Usheey tace "Toh ko we should get her on a bus, sai in rakata, na yafe Lectures din yau din" Miemee tace "muje Kawai, mayi attending nextweek" Seebi tace "ku barni please, zai daina, kar kuyi missing lectures saboda ni pls" kafin daya daga cikinsu ya k'ara magana Wayar Seebi tayi ruri, Usheey ta dauko wayar ganin Hamma ya sata dauka da sauri ji tayi yace "ku matso da ita" ya katse wayar, ya yace? "Cewa yayi a matso da ita, which means yana kallon mu, Miemee tace ga motarshi chan, Usheey tace "Oya Seebi, kiyi k'okari ki tashi ga R-Lema chan yazo, suka taimaka mata suka nufi motar, Idonshi fes kanta, cike yake da damuwa, ji yake kamar ya fito ya taimaka mata, ya dai daure ya zauna cikin mota ya k'wama Glass a ido yanda ba zasu gane yanayin yake ciki ba.
Sun so sata a baya amma tak'i bata so ya gano me ke damunta, tace su sata gaba,haka sukayi, suka rufe, be ce musu komai ba ya ja motarshi ya tafi, kallo daya ya mata ya dauke kai, Seebi na da dauriya, haka ta dinga cicijewa tana mutsitsika baki alamun zadi, har ranshi ya ke jinta, Da alamu tana shan wahala, ya na tausaya mata sosai, ya dinga driving, Seebi duk'e a gaban mota idonta lumshe Rafeeq ya dan juyo ya kalleta, kamar yayi kuka yakeji, a hankali yace "Sannu Kinji?" tadan kalloshi ta gyada kai, gani yayi gwara ya tsaya ya sai mata magani, don in taje gida kwanciya zaa sata tayi ko kuma wannan lunatic grandma ta bata wasu maguna marasa dadi, a hankali yace "Naseeebah, Me ke damunki?" ta dago a daburce ta rasa me zata ce mai, daure fuska yayi dan guntun Tsaki yace "Period pain ne?" waiyooo Allah k'asa bude Seebi ta shige, kunya ya rufeta ta rasa me zata ce mai, tsakin ya sake yi ya maida hankalin sa kan tuk'in sa, chan kuma ya kira Mamin sa Waya "R-Lema yadai?" Kamar bazai yi magana ba yace "Mam, First Aid for Mentsrual Pain, drugs? Anything?" ta danyi shiru chan tace "ba a cika san ana shan kwayoyi ba, its better to use natural remedy, like Hulba, Khal tuffah in hot water, hot water bottle" Mami ta shiga zanyano mai sunayen magunguna kala kala, Rafeeq ya danyi guntun tsaki yace "Mam-Mam, its an emergency, just name a thing, Mami tace "ok kane ma mata Khal tuffa cider vinegar sai hot water bottle sai ayi using dinshi" "Thanks Mam" zai kashe tace "Rafeeq wacece bata da Lafiya?" a takaice yace "Naseebah".
Waiyo Allah na is she alright?" Mami zanje in siya Mata maganin, sai mun dawo Gida" "Toh Feeq ina mata Sannu" ya kashe wayan, ya dan waiga ya ga Nasiba ta dan jingina kan kujerar, ya danyi parking ya dan rankwafo ta wurinta har tana jin saukar numfashin sa, ya kwantar mata da kujerar yace "kwanta kinji?" haka ya wuce ya siya mata duk abunda Mami tace ya kaita gida, ya taimaka mata da jakkarta, Mami ta sauko da sauri ta rungume Seebi tana mata Sannu, Nene tace "wannan ciwon Marar naki na fara tsorata dashi,Muje ga ruwan Zafi na dan dauraye ki" Rafeeq ya mik'a ma Mami ledar magungunan, Mami tayi sauri ta shiga kitchen da hado mata da dan ruwa mai dan Zafi.
√√√√√√√√√√√
Kula suke ba Nasiba kamar wata k'wai, Ba Daddy ba Rafeeq ba Ba Nenen ba, Zaid ma da ke Kaduna yana kira, binibini Rafeeq zai lek'o ya ganta tana bacci sai yayi murmushi ya juya, ya ci karo da Nene a wurin juya, Nene ta daga gira "yadai Dunkum ya da mana lek'e?" ya danyi tsaki yace "Ya jikin Naseebah?" ta ta6e baki tace "ni bansan wata Naseebah ba" ya dan kalleta da mamaki tace "nadai san Nasiba Seebin Nene" cikin rashin gane inda ta dosa yayi tsaki zaibi ta gefenta ya wuce tace "ni dai bansan ko a Amuruka a ka haifeka ba, naga iyayin ka ya soma yawa, in banda fi'ili da felek'e sunayen mu na da turanci ake fadansu, kace Mam, Neh-neh, oh ni Aminene diyar Mamman, har Nasibar ma da turanci kake fadarta? Wai Naseeebah" ta kwaikwayi muryarshi tana gyatsine, tsaki yayi me Sauti ya wuce ta tace "woo dangin tsaka".
*******
Kasa hak'uri yayi, ba inda zaije cikin daren nan, ga Maalesh yaje Kano, yana son sake ganinta, yana son Sanin in jikinta yayi sauk'i,ya kalli Mami, "How's she?" Mami tace "Taji sauki kam don yanzu nan ta bar Parlorn Nan" "wai Naseeebah?" inji Nene ta fada tana daria, yasan shi take kwaikwayo bece komai ba ya mik'e ya fita, Daddy na cewa "Nene sai na hadaki da Zaidunki, kin sa ma danshi ido" sukayi ta daria.
*******
Saude ta kulle kanta cikin daki tana ta kuka ta k'agara ta ga dawowar Meema taji yanda suka k'are, tana fatan dacewa, Aneesa tace "Mommy, wai ba zaki bari a kai ki Asibiti ba? Wannan kurjin sub ki warkewa, sai karuwa suke tayi suna fashewa ga wari, nidai gaskia bazan kara matse miki ba" Saude tace "Sorry my Baby, nasan gaji, karki damu Auntynki kawai nake jira, da ta dawo komai zaiyi daidaita, trust me my child".
*********
"May i come in?" da bata saurara da kyau ba, da bataji me yace ba, da Sauri ta latse wayar da takeyi da Miemee tace "Hamma shigo" tana dan gyara dankwalin kanta, ya shigo kan stool din madubi ya zauna cikiciki yake magana kamar ance dole sai yayi, yace "cikin ya bari?" cike da kunya tace "Eh ya bari" yace "Sannu fa" tayi murmushi yace "I'm hungry" da sauri ta mik'e tace "i'll cook you dinner" ya yamutsa fuskar sa yace "No no no, bana son cin Solid food at night, tashi ki rakani in har kinji sauk'i" da sauri tace "i'll just get ready" smilling yayi yace "good girl" ya fita. Ta bishi da ido tana mamakin shi, duk ya bi ya sauya, damuwarshi k'arak'ara a kanta, ta bude Sif ta ciro Hijab ta bi bayanshi.
Chapter 75 · 0% Book details