← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 95

Sashe 57

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Seebin mu, zo ki tayani kwasan kaya" tayi murmushi ta biyo shin gun booth, Nene kuwa tayi shigewar ta ciki tana murmushi, Manyan Ledoji guda 3 ya kwaso a booth din, yace "muje ko?" tace "Uncle Zaid cewa fa kayi inzo in tayaka" yace "kuma nagode muje" sukayi daria suka shiga ciki, Nene na nan kan tabarma, ya dire ledojin gabanta yace "Nenenmu ga tsarabarki ta Ingila ga kuma na Seebi" Nene ta bude ta na murna, Seebi kuwa kasa taba ledar tayi, tace "Allah ya saka da Alheri, Nene ta ciro Dogayen riguna marasa nauyi, tana murna, tace kamar kasan ina son dogayen riguna, sai dai kawai na zumbula su, kai madallah madallah da Zaidu dan Albarka, kai ALHERI NE, Allah ya biyaka ya raya Zuri'a, ta dinga shatato mai Adduoi, yaji dadin adduoin ta yace " Amin Ameen" Nene tace ke baki bude taki ledar ba, sadda kai tayi k'asa Nene tace "ke tafi chan shashasha, mik'o min ni in bude" kwalin waya ta fara cirowa, Iphone 6s, sai doguwar Riga mai wando, da dan jacket dinshi me kama da boyfriend jacket, sai takalma, sai kuma kwalin turare, sai kuma chocholates. Nene tace "Anya Zaidu BawanAllah kayan nan basuyi yawa ba?" Nasiba ta kalli kayan ta wutsiyar ido da sauri ta zabura ganin kwalin Apple, tace Uncle Zaid, i cant accept these, they are too much wallahi" ce mata yayi "Shhhh, they are not, they are all yours, and you are accepting all" Nasiba ta girgiza kai tace "Nene kingani ko, ki ce mai sunyi yawa, bazan iya amsa ba donAllah" Nene tace "gaskia ne kayan sunyi yawa, daga gani zasuyi tsada, amma ya zaayi aikin gama ya gama, Ingila ne balle a ce zaa maida su, ya zakiyi dole ki karba, amma nesitym(next time) kar ka k'ara irin wannan kaji? Zaid na daria yace " toh Nene ba zaa k'ara ba" Yauwa danAlbarka, ke kwashe kayan ki kai daka zamuyi hiran yaushe gamo da Zaidu dan Albarka.
*****
"Zaidu gaya min kana Son Seebi ne ko? Don wannan kayan sun fi kama da na toshi" cewar Nene ta na me daga mai Gira, Zaid ya daburce ya fara in ina, Nene da ta dago jirgin shi tace "kai kar ka wani damu, naji ka harda su in-ina, ai tuni na dago Jirginka, Son Seebi kakeyi" Zaid yayi murmushin jin kunya ya shafe k'eya yace "Nene taya kika sani?" tace "kai Zaidu na fa kwan biyu, ko kallon da kake binta dashi ai ya isa in gane, balle ni nan da saurin dago zance nikeyi, kaga ko Maalush sonta yakeyi" Zaid ya dan kallo ta yace "Mahmud dai? Tace shifa, shima kallon da yake binta dashi ne yasa na gano shi, kaga kar ka damu, kar kace baza kayi takara da Maalesh ba, bana zato ya ma sanar da ita, hikima ta ce ta dago min shi, Kayi saurin isar da sak'on zuciyarka gareta, don bana tunanin tana kula wani da namiji" Zaid ya share gumi yace "Nene kina ganin zata soni? Ba za tace na mata tsufa ba?" "Kai dallah tafi chan, kai tsoho ne? Duk tsufan ka ka kai Aminene Mamman? Ko ni zaka aura eyi? Ka manta kai Hadadden mutum da duk mace zata so samun ka? Kai ka kai da ba macen da zata guje ka, ko tace ka mata tsufa, ko da ka kai tsufa na, kaga Zaid, irin Ka nike ma Seebi adduar fatan samu, kaga mu ba makwadaita bane, Mu muna da rufin Asirin Allah, munfiso ayi Aure cikin rufinAsiri da so da k'aunar juna, kagane? Gwara ta aurei wanda ya san darajarta da kimarta, kuma ni Wallahi kai nikeso da Jikata, shawara daya zan baka, ka nemi So gurin Seebi" ya jinjina kai yace "InshaAllah Nene, zan nemi So Gurinta, in kuma Allah ya yarda, Zan auri Nasiba" Nene ta tafa hannayenta, tace yo Seebi zata zama sirikata don ni fannin Ango nike" yayi daria. A bangaren Nasiba ta gama jin komai don Nene ba a yi sirri da ita, ta rasa ganewa murna zatayi ne ko kuwa? Tabbas Uncle Zaid ya kai a So shi, don bai da makusa ko kadan, bata damu da tsufan shi ba, amma ta kasa yarda, Namiji kamar Uncle Zaid yace zai aureta, ai kam ta dace, ta nuna kanta da Yatsa, Wai ni Uncle Zaid keso?. Ba ta ankara ba taji yana kiranta, yace ta dauko mai wayarta zai saka mata Sim a sabon wayarta, duk ta kasa fita, Nauyi da k'imar shi suka k'aru a idonta, da k'yar ta fita tana susuna kai, Nene ta shige ciki bayan sunyi bakwana da Zaid, yanda takeyi ne ya bashi tabbacin taji su, hakan ma daidai ne, ya samu saukin wani abun, ya lura ta kasa daina murmushi, da kyar ta mik'a mai wayar, cikin muryar shi me sanyi yace "Seebin mu ni da Nene yadai? ta dago a hankali ta kasa hada ido dashi don kunya, yace " so you've been eavesdropping? Kinji tace gobe zaa daura auren mu ko? Shine kike ta kunya" da sauri tace "laaahh ba haka tace ba fa, cewa tayi ka nemi So a gurina" da sauri ta toshe bakinta, shi kuwa yayi daria yace "ashe dai kinji komai, so tell me, Zaki iya Auren Tsoho kama na? Ta rufe fuskarta da hannunta biyu ta tura kanta cikin cinya, yace " Magana fa zakiyi 'yanmata na, I love you Seebi, right from the first Day, i want you to give me chance and experience 'the Old School' love" da sauri ta tashi ta shiga daki ta barshi zaune don ya cika ta da kunya, kalaman shi sun mata nauyi, Zaid yayi murmushi, yace "i take that as a Yes" ya kwashi wayoyin duka ya fita dasu, saboda zai kai a yanka Sim din ta window take lek'en shi, ta na Murmushi, muryan Nene ta ji a sama "Hegiya ana so ana kaiwa Kasuwa" da sauri ta murtuke fuska ta fita zuwa kitchen.

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg4⃣9⃣

7:45am

"Ayman Zauna kici Indomie kinji?" Ayman ta k'ura ma Nasiba ido kamar me son gane Wani abu chan kuma sai ta fashe da kuka, Nasiba tayi saurin Rungume ta tana cewa "yi shiru kinji babyna in kaiki gurin Mami?" gyada kai tayi, tace ''to kici sai muje gun Mami a Motar Daddy ko?" nan ta shiga bata Indomie din tana ci har ta fara fiddoshi idan ta bata alamun ta k'oshi, Nasiba ta fita da plate Ayman a binta a baya duk inda taje, Nasiba ta sata a baya ta juye ruwan Zafi cikin bokiti ta tu6eta ta mata wanka, ta zo ta mata shafa ta sa mata wasu riga da dogon wando, sai ta sa mata Sweater sabida sanyi, tana cikin haka ne sai ga Zaid yayi Sallama, ai ko Ayman na hango babanta ta ruga a guje gunshi, ya dagata ya chafe, yace "Baby Good Morning" ita ko sai daria takeyi, Nasiba ta fito tana dari-dari ba tare da ta kalleshi ba tace "Ina kwana" cike da k'auna ya amsa mata gaisuwar, yace "Ya Bak'uwa, halan ta hana ku bacci?" Nasiba ta girgiza kai tace "Ai tunda ta kwanta bata tashi ba sai yanzu" a ranta tace "zai so ya san me taci" tace "yauwa taci Indomie kawai, ko akwai abunda zaa k'ara bata? Ya ta6e baki yace " Oho, ku kuka san in ta k'oshi, but ai nasanta bata da juriyar yunwa, da ta ji yunwa za tace miki "Friso" duk sukayi daria, yace "ina Nene?" tace "Nene taje siyan K'osai tun dazun, k'ila akwai layi ko suna chan suna Gardama da Maigadin gidan Lema" dariya yayi yace "wai kullum sai taci k'osai?" tace ai kuwa harda koko da ta dawo zata dama koko, wai idan bata ci K'osai ba ji takeyi kamar mara lafia" Zaid yayi daria yace "Nene Ikon Allah", ya sa hannu cikin Aljihu ya ciro wayarta ya mik'a mata, yace "gashi an yanko sim din" cike da kunya ta amsa tayi Godia. Suka yi dan shiru na wani lokaci sai chan yace "yau ba Lectures ne?" tace "Akwai" yace "to ya? Banga an shirya ba?" tace "ai bazan je ba" ya kalleta yace "saboda me?" tace "Ayman mana" yace "No No No, bamu yarda ba ko Ayman? Jeki ce ma Mummy ba mu yarda ba ta shirya yanzu mu kaita mu jirata ta gama lectures ko baby? Mummy ta maimaita a ranta, tirkashi, yace " Oya Madam, je ki shirya, hubbynki da babynki zasu raka ki Makaranta. Mun baki 30mins to dressup, Oya make it fast" ta tashi cikin jin kunya, bata so ta mishi gardama, haka ta shige dakinta" Daidai nan Nene ta shigo gidan da Sallama hannunta dauke da bakar Leda. Ahh Zaidu BawanAllah har ka iso kenan, yayi daria suka gaisa, ta shiga kitchen ta juyo K'osai din a plate ta shek'a Koko, ta fito inda su Zaid suke dauke da Jug da kwanon ta dire gaban Zaid da ke ta wasa da Ayman, ta koma ta dauko Kofi da teaspoon, ta dauki k'osai daya ta ba Ayman a hannu, Zaid yace "anya kuwa zata ci?" Nene tace bari ka ga ku yaranku sai indonie ko? To bari ka ga" Cikin saa yarinya ta hau cin k'osai, Nene ta fashe da daria tace "Yarinya is know K'osai" Sosai Zaid yake daria, harda k'warewa, tace "maza muci na san bakayi kalaci ba, ka zuba kokkon" ba musu ya sa hannu cikin plate din yana mai kara son Nene har ranshi bata da matsala wallahi (Anya Zaid? Tambayi Rafeew ka sha labari) chan yace "Nene ina na Seebi?" tace ce maka tayi zataci? To bata ci nai" ita sai Tea da biredi, ko indomie.
Chapter 57 · 0% Book details