← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 95

Sashe 3

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da tayi tafia sosai kafin ta iso gida, ta na ture kofar gidan ta ga Nenen ta tsaye, da sauri Nene ta rungumota tare da matse kwalla tace "Nasiba, ina kika tsaya haka? Duk kin tashi hankali na, ince dai lafiya ko?" Nasiba ta kalli kakarta cikin tausayawa, tace "Nene kiyi hakuri, darasi mukayi 4-6, ko da a ka tashi ba mu samu abun hawa da wuri ba, sai da ma mu ka tako har wajen gate kafin muka samu wani bawan Allah ya kawo mu har gidansu ushee" Nene tace bakiji yanda na tada hsnkali na ba, don naga baki taba kai wa haka a makaranta ba, na ci kuka na ni kadai, na fi minti 30 gaban gidan nan, ga shegen unguwar nan, ba wanda zaka aika. Da na hana babanki ya sai man waya, amma saboda irin haka, dole xai siyo min, Seebi tayi daria tace bari na shiga ciki in watsa, ko Laasar banyi ba wlh" Nene tace "yi maza, ga abincin ki chan a madafa" ta amsa tare da shigewa cikin gidan.

Assalam Alaikum yayi sallama a kofar falon gidan, mamimakon a amsa mai, sai jin ihu yayi, yayyy!!! Ga Uncle Zee oyoyo, wasu yanmata biyu suka zo suka rungumeshi, takaici ya cika Zaid, be da yanda zaiyi sai dai k'irk'iro murmushin dole wanda hausawa ke cema Yak'e kafi kuka ciwo, Babbar ta ja hannunshi zuwa dinning area, tace "Uncle Zaid, i know u must be hungry" murmushi yayi yace "Aa meema, ciki na a koshe yake" ta marairaice tace "donAllah kaci, ni da kaina na girka maka, wallahi na dade ina yi, please" Ya mata murmushin da ke kashe ta yace "Meema i'm full wallahi, some other time ko?" be bari tace komai ba ya kalli dayar budurwar yace "Aneesa Yaya na nan? Tace "eh Uncle Zaid yana sama" mikewa yayi ya hau sama.

Ya shiga da parlorn yayan sa da Sallama, Yayan ya amsa mishi cike da farin cikin ganin danuwansa, Barka da Yamma yaya, yayan ya amsa mishi da "Sannu da zuwa Engr. Zaid Ibrahim Lema, Zaid yayi daria, yace ka fara ko yaya? Nan suka fara fira irin ta wa da kani cike da aminci da kaunar juna, suna cikin firan ne Hajia Saude tayi Sallama ta shigo dauke ta tray, tana kwarkwasa kamar wata yarinya, "Ahh! Zaidu, ka iso kenan? Ya amsa mata ba yabo ba fallasa, ta dire tray din gabn mijinta ta na tsiyaya mai ruwan zafin shayi a dan karamin kofi, tace" Kaima a zuba maka Shayin ko Zaid? Ya mike da sauri yace "aa nagode, bari inje masauki nagaji" ya kalli yayanshi yace "Yaya bari na tafi zan shigo da safe in Allah ya yarda", Alhaji Habib Ibrahim Lema yace "Allah shi huta gajia Zaidu".

A parlorn kasa ya iske meema da alamun jiran shi takeyi, tana ganinshi ta nufo shi da sauri, Uncle Zee har ka gama da daddy? Yace eh nagaji ne, zan tafi na kwanta, tace yanzu ba za kaci abun da na girka domin ka ba ko? Yace "sorry Meema" sai da na ci abinci kafin na karaso. Ba haka taso ba sai dai ba yanda zatayi da shi tace "toh munje in raka masaukin naka" yace wa zai dawo dake? Don ni bazan sake fitowa ba sai gobe, ta mai fari da ido tace"ba sai na kwana chan ba" ya zaro ido, yace ke bana son shiririta, ta wayance tace "haba, kasan wasa nakeyi" ya wuceta ta bi bayanshi "mai zan dafa maka da safe?" Yace "Nothing". Ta juyo a fusace tare da fashewa da kuka haye sama..

Daidai haraban gidan mai gadi ya wangale gate, wata bakar mota mai bakin gilashi ta shigo, Uncle Zaid ya tsaya kallon motar har tayi parking, bangaren kujeran direba a ka bude, na cikin ya karaso gun zaid da sauri yace "Uncle Zaid sannu da zuwa, ya Kaduna? Zaid ya amsa cikin sakin fuska lafiya lao Mahmud. Dayan ya fito cikin takun kasaita, kamar be son taka kasa, ya karaso gun da su Zaid ke tsaye, sai da ya zo daf da su, ya tsaya ya cire baki da kyar yace "ka zo lafiya?" Zaid yayi murmushi yace "lafiya kalau Rafeek, ya karatu? Maimakon ya amsa shi, hannu ya sa a aljihu ya zaro makulli ya bashi, yace " room 108, Allah huta gajia" ya maida duban sa ga abokinshi yace "Night Maalesh" ya juya ya bar Zaid da Maalesh a gurin. Zaid yayi murmushi ya tsaida shi ta hanyar kiran sunan shi "Rafeek Lema " Chak ya tsaya.

_Bibilicious biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg5⃣

Zaid ya yi mamakin maganar Aneesa, banda yarinta ya za'ayi tace a aura mata Rafeek? Uncle Zaid baka ce komai ba, Aneesa ta katse mishi tunanin.

Yak'e yayi, yace "banda abunki Aneesa, wa zai ma Rafeek aure yanzu? Rafeek fa yaro ne, he is just 24" tace "Uncle zai- ya katseta ta hanyar daga mata hannu yace "please anee, no one is getting Rafeek married now" tayi raurau da fuska, tace"Wallahi ina son Rafeek, zan kuma jira shi, zan jure duk wani wulakancin da zai min.

"Tunda maganan Soyayya akeyi, bari kuji labarin rai na"
Meema ce ke fadin haka a yayin da ta ke sauko wa daga bene har ta karaso gaban su, sanye take da shara-sharar rigar baccin da ko guiwar ta bata rufe ba, Zaid ya dauke duban sa daa kanta, masauki tayi kan kujerar da yake zaune, fari take mai da ido tace "Uncle Zee, kasan irin son da nake maka? Ni bansan yanda akayi na fara sonka ba, kuma na sha mafarkin mun yi aure mun haifi kannen Ayman, Uncle Zaid ka aureni please.

"Ya Salam!" Zaid ya furta a hankali tare da dafe kanshi, wasu irin mata ne wannan? Masu tallan kan su, Ya cije ya kalli meema da ke ta wurwulla idanuwa don ta burgeshi, wani takaici ya tokare mai wuya, ya san Meema na son shi, tun kafin yayi aure, amma ba zai iya auren ta a haka ba, sam rayuwar su basuyi kama ba.

Alhaji Habib Lema da matarshi Hajiya Saude suka sauko kasa, da sauri Zaid ya tashi ya nufi gun yayan shi, yace "Barka da safiyya" Yayan yace "lafiya lao, Engr. Har anyi harramar tafiya?" Zaid yace InshaAllah "ya juya ya kalli matar yayan sa yace "Madam an tashi lafia?" fuska sake tace "lafiya lau Uncle" yayan yace "Zaid muje daga waje akwai wata maganar da nake so muyi, yace "toh yaya" Zaid ya musu Sallama da ga chan zai wuce, ba haka hajia saude ta so ba, ta so taji maganar da Alhaji zai gaya ma Zaid, ta so taji me zasu tautauna a kai.

Meema ta kalli yayar ta rai a bace tace na "Nagaji Sauda, ya za'ayi na dinga mishi tallan kai na ya na ba dani? Nifa na fi karfin wulakanci da namiji" H.saude ta murmusa, tacd dadi na dake Maryam gajin hakuri, ai komai sai an bi a sannu a ke dacewa ko? Kiyi laakari da yanda ni na samu Alhaji, ki kara hakuri komai ya kusa zuwa karshe" Aneesa tace "Mummy ni kum-- Hajia saude tace " shhh, Matsalarki Rafeek ko? Nima shine kadai matsala ta, bana jin Zaid, Rafeek nakeji, amma kar ya damu idan ya sn wata be san wata ba, ku bar komai a hannuna kunji?" Meema da Aneesa suka chafe hannu cikin murna suna fadin "sai ke mata daya rak a gidan Habib Lema" ita ko dadi wannan kirarin ya mata dadi ta haye sama.

A hankali yake tuk'insa, yana tunanin maganar da yayan sa ya gama mishi yanzu, a kan karatun Rafeek ne, inda yayan ke cewa "kaga Zaid, ni sai nayi wata da watanni ban daura Rafeek a idona ba, be yarda mu hada hanya, anya yaron nan be shaye shaye? Da sauri Zaid ya girgiza kanshi, yace " wallahi Rafeek be shan ko Sigari"

Yayan yace "Zaid na kasa yarda da hakan shekara ta uku kenan Rafeek na Spill over a makaranta, last upper year spill over from nowhere, be gyara ta ba, last year ma be gyara ba, ina tsoron wannan shekarar abun da ya faru ya sake faruwa don da alamun abokan banxa yake bi suke bashi wasu k'wayoyin da ke taba mai kwakwalwa, shisa ya kasa kwantar da hankalinshi yayi karatu" da sauri Zaid ya katse shi, ta hanyar cewa "aa yaya, ka fadi Alkhairi ko kayi shiru, kowa ya san Rafeek mai k'okari ne da hazaka, kar ka manta tunda Rafeek ya shiga UMYU shine over roll dinsu, 4+pointer, komai ya dagule ne sakamakkon k'addara da ta riga fata, amma InshaAllah komai zai daidaita. Alh. Habib ya jinjina kai yace "haka ne Allah shi kyauta, amma kasan har yanzu ba ya min magana? Zaid ya tashi yana daria yace bari na tafi "Yaya sai na dawo karshen Sati"
Alh. Habib yayi daria "wato ba ka son laifin shi ko?" Toh Allah ya kiyyaye.

Wata tsohuwa ya gani da ga gefe ta na sa mai hannu, yayi mamaki don ba a titi yake ba, har yanzu be fita daga cikin Unguwar ba, ya dan gangara ya sauke gilashin motar shi, yace Lafiya Iya? Tsohuwar tace Yauwa bawon Allah taimaka ka zo ka ka duba min layin wutan chan, k'auri yake yi,nafi minti 30 tsaye ko zan ga wani namijin da zai duba mun, amma tun dazun shiru, Zaid yayi shiru ya na karantar tsohuwar nan.

Can ya fito ya kulle kofar yace muje nagani, tsohuwar ta ja shi har cikin madaidaicin gidanta, daidai gurin, fuse din har ya fara spark , "SubhanAllah, kinga ya fara kamu da wuta" Zaid ya ga in dai ya bata wani lokaci wires din wurin za su fara ci, kuma baa san inda wutan zai tsaya ba, yayi jihadin sa hannun shi ya zaro fuse din ya cillar.
Tsohuwar ta sa ihun murna har da tafin ta, tace "sannu dan Albarka, Allah ya sa ba abunda ya samu hannuka" Zaid ya dago hannun shi, Cikin ikon Allah ba abunda ya samu hannun.
Chapter 3 · 0% Book details