← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 95

Sashe 78

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saude tayi mugun shiga taitayinta, yanda taga Alhaji ya banzatar da rayuwarta, ya nuna mata cewa da ita da banza daya suke, ita har ga Allah tana sonsa. Mami ta samu Aneesa a daki wata rana bayan ta dawo daga School, Mami tace "Aneesa, komai yayi zafi maganin shi Allah, nasan Saude ba ta kyauta ba, ba kya tunanin cewa abubuwan zasuyi mata yawa? Kin dauki gaba da ita, watan ta kusan 1 a Asibiti ba kije kin dubo ta ba, Sannu be taba hadaki da ita ba, Aneesa horon da kika mata yayi tsanani, Uwa uwa ce, ko ya take, donAllah kije ki sassamta da ita ko ta samu sauki, nasan hankalinta a tashe yake, i was once in her shoes, Rafeeq turned his back against me, banji da dadi ba please Have Mercy on her, go talk to her" Aneesa ta share hawayenta ta san tana matuk'ar Son Mamarta, amma what she did was unforgiveable. Ok kawai tace ma Mami. ••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••• "Kanaji ko? Kwana 1 na baka, ko ka kawo min cikon kudina, ko wallahi in sa Guys su min gunduwa gunduwa da kai, you cannot run away from me, wherever you go, i will find you and i will Kill you, i want my Money" Ya hadiye wani mugun bakin miyau, duk Iskancin shi ya san Steve ya fishi, yayi dana sanin Shiga Chachar nan, da beyi Chacha ba k'ila da ya rage Bashin 2million din da Steve ke binshi yace " Sorry Iga Steve, i'll get you your Money, kayi hakuri" Steve yace "Ka sanni, kasan me zan iya yi, get my money Ready or else, hmm" ya kashe wayar, cikin shi ya duri ruwa, da sauri ya lalubo Numberta. "Fatara me tada Tsohon Bashi, Aminiyata ya kike?" a tsure tace *Mak'ale, meyasa ka kirani, we dont have any Bussiness left, kar ka sake kirana, You might get me into trouble, danAllah kar ka sake kirana" dif ta kashe wayar, tana waigen bayanta Allah yasa ba wanda ya jita, wayarta ya sake ringing har ta katse bata dauka ba, ya sake kira ta dauka a masife " Ke Sauda, butulu, ni zaki kashe ma waya? Kar ki kawo min Iskanci mana, haka kurum da ina kiranki ne? Kudina zaki ciko min, na sha miki aiki kina bani rabi baki ban rabi ba, nasan ina binki bashi fiye da 7million, amma na bar miki 5, ki bani 2million ciki, i need it, its an emergency, kuma ina sonshi kafin gobe" cike da rudu tace "Makale me kake cewa ne? Are you insane?, banda sauran Alaka da kai, please ka rabu dani, i am a born again person, ina so in saita rayuwata, i want to start new, so Please ka rabu dani, kar ka sake kirana" wani mugun daria Mak'ale yayi yace "Nice Joke Sauda, kinsan dai na fiki tasha ko? Ni zaki cema you are a born again hahah Sauda bani ke da wuta ba amma na san ke 'yar wuta ce komin tuban da kikayi, kin dade kina tsula tsiyarki, mtsww, yanzu ba wannan ba, Kudina nake so, someone is threatening me, if i go down i promise to drag you down with me, idan baki son Asirin ki ya tonu ki hada min kudina kafin Gobe wallahi in ba haka ba, komi zai iya faruwa" dif ya katse kiran,Zufa ya fara jike kayan Saude, ya zatayi? Ai ba zata taba bari asirinta ya tonu ba, wanda ya tonun ma tsautsayi ne, tana cikin tararrabin nan ne Meema ta shigo dakin tana zuba uban k'amshi, Saude a razane ta kalli Meema tace "Meema akwai Matsala, i need your help, Makal'e ke min barazana, wai zai tona min Asiri idan har ban bashi 2millionn ba donAllah ki taimakeni, bana tunanin a Account dina zan samu ko da 100k" Meema ta kalli Saude galala tace "Sis are you crazy?ke matar the great Habib lema baki da kudi sai ni? Please stop this nonesense now" baki wangale Saude ke kallon Meema da mamaki, yau ita Meema ke ma magana Gatsau? tace "Maryam nike ma magana haka?after all i've done for you? I took care of you tun kina k'arama and now don banda wata mamora kike min magana yanda kika ga dama" Meema tace "nifa kin dameni, haba, gori zaki min don ina zaune a gidan Mijinki? To karki damu i'm leaving and never coming back, dama son Zaid ne da burin samun Shi ya sa ni zama a gidan nan all this while, amma naga banda chance din samunshi kwatakwata bana gaban shi, to banga amfanin zamana a gidan nan ba, bayan inada Sugar daddies din da zasu ingata rayuwa na da kuruciyata, da kyau na, na hakura da Zaid, ba zan lallace kanshi ba bayan inada Future , so zamana a gidan nan be da amfani" ta juya da sauri saude tace "No No Meema donAllah Dont Go, dont leave me like this, i need you now more than ever, you are the only one i have left, kema ni kadai gareki, pleaee kar ki tafi" Meema ta kalleta a tsaye tace "Sorry sis, i cant do anything for you" Aneesa tace "Aunt Mee, you are leaving? Why?" Meena ta daga kafada tace "Anee take care of your Sis, ni na shiga dunia, i'll come back when i acheived what your Mom wasnt able to Acheive" ta banga k'ofa ta fita, Saude ta rushe da wani irin kuka, Aneesa ta karasa gunta don lallashi.. ****** "Saude kin hada min kudina ko kuwa?" jiki na rawa tace "Kayi hakuri i need more time" da tsawa yace "I dont have any time left, once 2 yayi clocking it would be the end of me, and you are my last hope, so i ask You nicely ina zanzo in karbi kudina?" cike da tausayin kanta tace "Mak'ale, inada ATM's biyar, ina jin kudin cikin duka zasu kai 400k, ga Sark'a na da yan kunne sai a saida, na san zasuyi 500k, in aka harhada nasan zasuyi 1million, ina kuma da Gona duk sai in baka ka har hada" Mak'ale yayi Murmushi yace "Good Girl, yanzu kikawo min, ina ta wurin Magama" Saude ta fashe da kuka yace yadai? Tace "Mak'ale banda k'afa, k'afa ta daya, an gundule dayan?" cikin halin ko in kula yace "Really? Yanzu ki ba Meema kayan kawai ta kawo mun" "Meema left me Jiya" haan to ya zaayi? "Ya zan samu kaya na ne? Ina diyarki?" da sauri tace "keep my daughter outof this" "So tell me how can i get my Shit?" tace "Shi nake tunani ni idan na fito they'll be suspicious" yace "i'll come get it" tace "no you cant come over" yace "like you have an option, nagaya miki need to get the whole shit kafin 2, and this is past 12, the earlier the better, if you are worried i'll be caught kar ki manta waye mak'ale, i'll gt everything under control like always, ki tuna duk aikin da kika sani bantaba failing dinki ba, so dont worry i gt my ways" ba dan hankalinta ya kwanta ba tace "Ok". ******* Dawowar shi daga School kenan, a gajiye yake don a yau ya ga Project dinshi, Cikin gida ya shiga, ba kowa a Parlorn k'asa Sai Saude da mak'ale yace ta harhada mai komai gashi nan zuwa, ganin Rafeeq a wannan lokacin ya tada mata hankali, amma ganin be nuna ya ganta ba ya sata dan kwantas, hayewa sama yayi yana kiran "Mam". Doguwar riga jallabiya ce jikin Mak'ale, yayi rolling da gyale, ya k'wama bakin glass wanda ya mamaye fuskar sa, ba ka taba gane shigar maza yayi, a bakin gate yace da Baba Maigadi suna ciki? Yace " Hajia babba ko karamar? A takaice yace babbar yace eh ta na nan, Makale ya shiga gidan yana taku kamar mace, kai tsaye Saude tace tana Parlorn kasa da ya shigo zai ganta, kawai sai ya amsa ya ware, a saukake batare da kowa ya ganshi ba, kan Mak'ale a kasa ya shiga, ko magana basuyi da Saude ba ya amsa k'aton Envelop din hannunta ya juya ya fita, Saude ta sake ajiyar Zuciya ganin ba wanda ya ganshi har ya bar Parlorn, a ranta tana tunanin dabara irin ta mak'ale. Da sauri sauri Makale ke tafiya a farfajiyar gidan, karaf ya ci karo da wani abu, ko da ya dago wata tsohuwa ya gani, Nene ta yashe Baki tace "ikon Allah, saurin me kikeyi ne haka da baki kallan gabanki in kina tafia? Iye? Makale ya sadda kai, Nene tace" ko da yake ya zaki ga gabanki bayan sanye kike da wannan bakin tabarau din?". Daddy da Uncle Zaid suka shigo gidan dama tare suke da Nene ta dai riga su shigowa inda sukuma suka tsaya a waje suna dan magana, daga gidan Nene suke, su ne dubo Ginin ne, A k'asa sukaje. A lokacin kuma Fitowar Rafeeq kenan daga cikin gida, ya sa Mamin shi dafa mai indomie, ya ga Nene na ma wata Mita, tsaki kawai yayi yace "this woman, she annoys everyone, har bak'in ma bata barsu ba" yayi hanyar Dakinshi ya ga Rigimar Nene wai sai ta cire gilashin Matar nan, ya tsaya ganin ikom Allah wannan karfin halin Nene na bashi mamaki, ina ruwanta da Glass din da matar ta saka? Makale na dan karewa ba dama ya sa hannu ya bangaje Nene don kayan dake hannunshi, Nene ta ci nasarar cire Glass din fuskar Mak'ale.Nene na daria tace"Diyata ya na ga fuskarki kamar ta gardi?" Fuskar da bazai ta6a mantawa ba ko anyi shekara dubu, fuskar da ta jefa rayuwarshi cikin Garari, Fuskar da ta sashi cikin K'unci da Ukubar Rayuwa. Tafia yake be ganin gabanshi idonshi a rufe, ba abunda yake gani sai bakar ranar da bazai taba mantawa ba, komai ya dawo mai sabo, ba su san da zuwan shi ba, sai da Mak'ale yaji an rike mai k'ugu anyaye gyalen kanshi, Nene ta dan daka tsalle tayi baya tare da karanto "Summa Alaiyna bayana" na shiga uku me zan gani haka? Gardi da shigar Mata, Idon ryafeeq ya kada yayi Jazir, tabbas shine, aiko Mak'ale ya zubda kayan hannunshi zai Arta a guje Rafeeq ya damk'o shi ya sauke mai
Chapter 78 · 0% Book details