Sashe 12
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aishatu tace "anya Baba anyi ma Zaid adalci? Ai ya kamata ayi bincike, Habib yace wani bincike kuma? Bakiji ya amsa laifin sa ba? Tace ya amsa ne don bai da mafita, bayani yake muku amma ba ku son yarda, hasalima da ya fara bayani kuke katse shi, be da wata mafita in banda ya amsa laifin da bai aikata ba. Idan ana maganan irin wannan tarin dukiyar, be kamata ace an bar magana haka ba, what if Zaid bai dauka ba? Shikenan dukiyar ta salwan ta? Nidai ina ganin ayi bincike" Hafiz ya shiga hararrar ta a ranshi yana kiranta 'munafuka' Baba Tijjani yace kuma maganar ki Aisha abun dubawa ne, dole a yi bincike kam. Hafiz yace "toh a fara da dakin shi mana?" Zaid yace "wani gun zai kai ai ba zai aje a daki ba" Hafiz yace muje dai mu duba, dukkan su suka nufi waje don zuwa dakin Zaid, dakinshi ne na farko sai na Hafiz, Hafiz ne a gaba suna bin shi a baya har Aisha. Zaid na ciki yana kuka yana ganin su ya tashi ya matsa gefe, Hafiz ya shiga neme neme a wardrobe, Habib na daga katifar Gado sai ga Save na kallon su, gabaki daya suka sake sallati. Habib yace "Ahap, ai na gaya muku, ni na sani gashi nan dai, Habib ya ciro save din ya bude password din 'Zaid Lema' wayam ya ga save din, ko allura babu, Zaid ya hadiye wani irin mugun bakin miyau, ya san bai da wata mafita. Habib yace kagani ko Baba? Ba komai cikin Save din, ya salwantar da su. Baba Tijjani ya girgiza kai, yace "Zaid, ka bata wayonka" ya fita, Habib da Hafiz suka bi bayan shi.
Aishatu ta kalle Zaid cikin ido, hawaye ne malale kan kumatun shi, fuskar nan tashi tayi Ja, tace "Zaid why?" girgiza kanshi yayi yace "Aunty wallahi i didnt do it" gyada kai tayi tace "i believe you".
Bayan Sati 2.
"Haba Habib, meyasa kake haka, don me zaka biya ma Hafiz kudin makaranta ka ce ba ruwanka da Zaid, ya biya ma kanshi? Naga dai da Hafiz da Zaid duk daya suke a gunka?" yace "Aisha, Ni Zaid ya sire min, ya bata wayon shi, ya ban kunya, shi yasa na zame hannu na kan lamarin Zaid, tunda yana da kudi sai ya biya ma kanshi duk makarantar da ya ga dama a fadin duniyan nan" tace "wai shin in ma haka ne, ai naga Hafiz shima an raba Gadon nan an bashi, shima yana da kudin nan, ai sai ka biya musu duka, ko ka k'i biya musu duka, duk su biya ma kansu, yace "hakan na ga daman yi" tace "kana raba daya biyu, na fa lura da kai, tun bayan da abun nan ya faru ka ke kyaran Zaid, ko gaisheka yayi baka amsa wa, ko yaranka ya dauka sai kayi ta mishi fada,kana hantarar sa, haka akeyi? Kar fa ka manta kaine uwarshi, kaine ubanshi. Habib yace "ke Aishaba abunda ya dameki, ko taro ba zan sake kashewa kan Zaid ba, and baki da hurumin yi min magana kan Zaid, duk randa kika sake cewa na ma Zaid kaza zaki fuskanci fushi na, this is my decision, and its final" ya tashi ya bar mata parlorn, Hafiz na jinsu, a ranshi yace wannan matar na shigar min hanci amma zan fyato ki...
Tafiyar Hafiz ta kankama, yau suka tafi Abuja shi da Habib, inda Jirgin su zai tashi zuwa kasar Malaysia, Zai fara karatun shi fanni Computer Studies.
Zaid ya ci kuka da ya ga Hafiz ya tafi, dagaske Yaya Habib yake kenan, dagaske ya zame hannun shi daga lamuran shi, toh shi ya zaiyi? Shi kenan ba zai yi karatu ba? Burin shi na zama Injiniya ba zai cika ba? Wa zai sponsoring dinshi? A yau ne yayi kuka sosai, a yau ne yake kukan Maraici. Ji yayi ana share mishi hawaye, ya dago kai da sauri, Rafeeq ya gani da sauri ya dauki yaron ya rungume shi yana hawaye. Aishatu tace Zaid tashi share hawayen ka. Ya dan zabura, ashe ba Rafeeq kadai ya shigo dakin ba, ya dan kwakulo murmushi yace Aunty tun yaushe kike nan? Tace "tunda ka fara sambatu" anan ne ya fuskan ci zancen zucin da yakeyi ya fito fili. Yace "Aunty yaya ya dauke Hafiz ya kaishi Malaysia, ni ina nan, ba sanaa ba karatu, ni ina ga zan fara aikin karfi kamar Welda ko Kanikanci, idan na tara sai na siya Jamb in cike ko ABU Zaria ne. Aishatu tace "kai Allah ya sawwake, Wallahi kafi karfin yin Welder ko Kanikanci. Aunty ba yanda zanyi, dole zan nema sana'a dole inyi karatu, ina son cin burin,tunda ba wanda zai dauki nauyin karatu na dole in tashi tsaye don neman yanda zan cigaba da karatu na. Aishatu ta mike tsaye, tace Zaid, ni Zan dauki nauyin ka, Zaid ka nemo duk makarantar da kake so a fadin kasar nan, in har be fi karfi na ba, Zaid zan tsaya maka da ga farkon karatun ka har karshen shi.
"Zaid i will Sponsor you if you'll let me". Zaid da mamakin furucinta yace "Aunty, kar ki damu, bana son daura miki wani nauyi, ba kuma na son ki samu matsala da Yaya" Aishatu tace "Kar ka damu, ba wani nauyin da zaka daura min, ko ban auri Habib ba ni me iya daukan nauyin ka ne, Babana ya gaya min irin Halaccin da Marigayi Lema ya mishi, kaga ko ban fadi ba duk abun da na maka. Kuma maganar Habib, ai ya amince kayi karatu, yace dai kwabon shi ne ba zai yi ciwo ba a kanka, to kar ya damu kwabon shi ba zai yi ciwo ba, kuma zakayi karatu a Turai. Muje muyi searching relevant Schools before its late" ba ta jira amsar shi ba tayi waje. Cikin farin ciki ya dauki Rafeeq yana wulla shi sama yana cewa "Rafeeq maman ka wace iri ce?"
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg1⃣6⃣
A parlor ya iske ta ta ciro Latop dinta ta shiga yanar gizo, tace "wacce Kasa kake da burin karatu, kumae kake so karanta?" Ya danyi jim alamun tunanin yace "USA, ina son karantar Engineering". Murmushi tayi ta fara searching Relevant Schools a USA; tace " zo ka gani Zaid, ga wani Havard University Cambridge nan" ya matso, details din School da komai ta duba, tayi naam da makarantar, shima haka ama ba laifi makarantar zaiyi tsada.
Nan da nan ta fara ma Zaid processing, bayan Sati daya ta tura wani Yaron babansu da Zaid American Embassy dake Abuja don neman Visa. Komai ya kankama, don saura kwana 2 tafiyar Zaid Makaranta.
A ranar Habib ya dawo gida Bayan ya sada Hafiz da makaranta, ya mai Wa'azin da ko kofar kunnen shi be shiga ba, Habib ya tabbatar mai da cewa duk wata zai dinga jin Alert na shigo mai, Hafiz yayi godia Sosai.
Zaid ya zo mishi sannu da zuwa amma ko tanka shi baiyi ba, Aisha tace ya yan makaranta? Yace "Hafiz dan Malaysia ana chan bawan Allah, da zan taho harda kukan shi, ya ban tausayi". Aishatu tace "Allah Sarki, Allah ya bada Sa"ar karatu" yace Amin.
Tace "Shima Zaid dai ya kusa tafiya" ya dan zaburo, ina zai tafi?" tace "yo karatu mana a USA, ko nan zai tsaya ya lallace?" Habib yayi tsaki, yace kinga abunda nake gaya miki ko? Shi ya dauke dukiyarsa,in ba haka ba, waye zai biya mishi karatu a Havard University? Aisha tace "nice nan,ni na dauki nauyin shi, zan tsaya mai har sai inda karfina ya kare" cikin mamaki Habib ya kalleta yace "Ke Aishatu, ina mai umartan ki da ki janye hannunki kan Zaid, tace ita sam, ita ta sa kanta Shin ba kai kace ba ruwanka da duk wanda zai taimaki Zaid ba? Kaine dai kwabon ka ba zaiyi ciiwo ba?Toh ni zanyi sponsoring dinshi, i'll endorse him, Deal with it Habibullah! Ta fice ta barshi zaune da mamaki.
Kwana biyu ba zaman lafiya tsakanin Habib da Aishatu, Zaid yayi takaici, don a ganin shi shine sillar faruwan komai, har ya sameta yace "Aunty, tunda Yaya ya haneki da taimaka min, a bar maganan karatun nan kawai, Allah ya biyaki". Tace sam Zaid, karatu kamar ka tafi ka gama ne, i've spent alot on it, ba zan yi hasara ba, so make me proud, kaje kayi karatun ka, ta mishi yan nasihu da waazi.
WasheGari Zaid ya je Gidan Baba Tijjani ya maj Sallama, Ya dawo gidan yayan shi ya durfana gaban sa ya na hawaye yace "Yaya ka yafe min, kar kayi fushi dani, kaine Ubana, kaine Uwata, fushinka kamar na Iyaye ne, Yaya kayi wa Allah ka samin Albarka a karatun nan da zanyi"
Sosai ya ba Habib hakuri, shi yasan yana son kaninshi, amma fushi ya rinjaye shi, a ranshi ya sa ya yafe ma Zaid, yace "tashi ka tafi Zaid, Allah bada saa, a kula, know where you come from".
Rannan tafiar Zaid da kyar aka banbare Rafeeq jikin shi, kuka yakeyi kamar ana zare mai rai, Ko Rafee'ah da bata san komai ba sai da tayi kuka, Aunty Aisha ma ta koka.
4Years Later(Bayan Shekaru 4)