← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 95

Sashe 52

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Tabdijam, ai yanda ka bashi Magungunan nan haka zai dire maka su don ba sha zaiyi ba Wallahi" cewar Nene bayyan sun bata labarin abunda ya faru a Islamic center, Nasiba tace "Abii ka kirashi ka mai Magana k'ilan idan yaji daga bakinka, ya dinga sha" Abbii ya jinjina kai, yace "Kira min shi a waya" da sauri Nasiba ta amsa wayar Abii ta sa mai Number Rafeeq tayi dialing, Wayar ta dade tana ringing, har ta gaji da ringing ta mutu, kallon Abbi tayi tace "be dauka ba" Nene tace "ina zai dauka yasan zaku sa shi magana, Abii yace "sake kiran Shi" Nasiba ta sake kira, sai da ya kusan tsinkewa ya daga, dama yana ganin kiran farkon, ganin be san number ba yaki dagawa sai yanzu, Karawa kawai yayi a kunne ba tare da yace komai ba "Assalam Alaikum" muryan Abbi ya ratsa mai kunni, zumbur yayi ya mik'e, sai dai ya kasa amsa Sallamar, Abii yace "Rafeeq, in ka samu lokaci, kazo gidan Nene yau ina jiranka" Abbii be jira amsar Rafeeq ba ya kashe wayar, Rafeeq ya tsura wa Wayan Ido kamar zai ga Abii a hankali yace "Why is he Bossing around?" guntun tsaki ya koma ya kwanta.

Da kyar ya iya cewa "Assalam Alaikum" Abbii ya amsa tare da umurtan shi ya shigo, ya shiga ya zauna kan tabarma, Nene da Nasiba na ciki, basu san shigowar shi ba, Abbii ya tsura ma Rafeeq ido, guntun tsaki yayi yace "Barka da Yamma" Abbii yace "lafia lao Rafeeq, ka ci Abinci?" samun kanshi yayi da girgiza kai alamun "aa" Abbi ya ciri baki ya kira Nasiba "Seebin Nene, zubo ma Rafeeq Abinci" Nene ta kalleta tace "Dunkum yazo ne?" Seebi tace "ya zaayi in sani ni da muke nan zaune dake" Nene ta kai mata duka tace "Tambayar ki nayi ba ce miki nayi ki gayan magana ba". Rafeeq ya kalli Abii, yana so yace mishi kar a zubo mai abinci amma ji yayi bakin shi yayi nauyi, ya kasa Magana, shi besan dalilin da yasa yake jin shi wani iri gaban Baban Yarinyan nan. In ma dai girma ne Daddyn shi ya girme Abbii Nesa ba kusa ba, guntun tsakin mts yayi, Nene ta zubo mai Shinkafa da Miya, da lettuce a gefe, tazo ta ajiye mai, karaf idon shi ya kai ga Zoben yatsan ta, kafin ya samu damar sake ma Zoben kallo ta tashi, tace "Hamma Ina wuni" bata sa ran ya amsa ta ba ta koma cikin daki, Abbii yace "Bismillah" ba musu ya ja plate din gaban shi ya fara ci a hankali, be ci da wani yawa ba ya ture, Abbi bece komai ba yace "Rafeeq" Kasa amsawa yayi ya dago kai ya kalleshi, Abbii Wani makaranta kake? A k'agauce yace "Umyu" wani Course? "BioChem" Abbii yace shekarar ka nawa a School din? Da sauri Rafeeq ya kalleshi, Abbi ya mishi alamun ina sauraren ka, guntun tsaki yayi yace "6years" Abbii yace "Spilling kake tayi?" "Uhm" kawai yace don baban Nasiba ya fara k'ureshi, "Let me help you" a dan tsawace yace "I dont need your help" Shiru Abbii yayi ya kawar da kai gefe, ganin be kyautu a ce ya daga ma Babban Mutum murya haka ba yasa shi cewa "Look i'm sorry, but i dont need your help". Ya mik'e zai tafi, Abbii beyi yunkurin hanashi ba don yasan dole Rafeeq zaiyi wuyan Sha'ani, amma zai lallaba shi har ya yarda.

"Dunkum Yazo daki ya gaida ni, k'afana na ciwo" chak Rafeeq ya tsaya shi beyi gaba ba shi beyi baya ba. Me wannan tsohuwar ke nufi da shi ne, kamar yayi gaba kuma sai ya tuna She's Uncle Zaid's Favourite, in har ta kirashi ta gaya mai bata da Lafiya, to tabbas zai maido shi yace yazo ya dubata ko kuma ya kaita Asibiti, kuma dole ya buge mata warning, ta daina ce mai Dunkum" Dogon tsaki yayi ya dawo ya wuce Abbi, ya cire Takalma gaban daki ya shiga ko Sallama, Nasiba na ganinshi ta mik'e tsaye, bata yi tsammanin zai dawo ba, ko kallo bata ishe shi ba, ya kalli Nene cikin b'acin rai yace" ki daina ce min Dunkum, ba sunana kenan ba" Nene tayi daria tace "Au haba? Ashe ba sunanka kenan ba, ai ni bansani ba, duk zato na sunan ka Dunkum, ya sunanka? Cikin daga murya yace *"I am Rafeeq Freaking Lema* "get that into your Oldie Skull" Nasiba cikin rudu tace "Heyy, Watch It" ya juyo ga Nasiba a fusace yace "Warn your GrandMother She should Stay the Hell away from me, you all should" ya bar Wurin a fusace be ma lura da Abbii baya nan ba ya fice, Nene ta bude Murya, "Sunanka Kenan Dunkum dangin tsaka, har sai randa ka koyi Magana kuma ka bar tsaki, rannan zaka koma sunan yanka ka, amma yanzu dai muje a Dunkum din" yana jinta amma be tsaya tankata ba, don ya san ya sake bude baki yana iya fashewa da kuka.

"Nene meyasa kike ce mai Dunkum? Ki bari donAllah, kinsa shi ya tunzura har yana gaya miki magana, Gudumuwar da zaki bada wurin ganin Ya warke kenan?" cewar Nasiba, "Ke dallah rufen baki, kinzo kina min fada kamar Inna Ladingo(Maman Nene) ni ko zan bada Gudummuwa babba wurin saito Rayuwar Dunkum, Gundunmuwata daya shine zan taimaka in dinga sa shi yana magana ko ya k'i ko ya so, tun beyi har yazo ya saba ya dinga magana, kuma wannan shegiyar tsakin, dole sai ya bari, in yayi tsaki har k'walkwata wallahi, amma dai yanzu ya daina ban haushi tunda na fahimci cewa ba yin kanshi bane, be 6atan rai, tun asali ma be 6atan rai, shirun shi da miskilancin shi ne bana so, kuma dole sai ya koyi magana" Seebi ta kalli Nene ta girgiza kai "to wa ya ce miki ana so ya dinga magana, miye matsalarki da rashin magana?" "ke tafi chan, ke me kika sani? Sai ya koyi surutu ko yana so ko be so, wata rana kuma sai ya gode mun dana bada guddumuwa gun sa shi magana" Daria kawai Nasiba tayi tace " ta ina bayan kin korashi, bana tunanin ko gidan nan zai sake zuwa" Nenen tace "Lallai yarinya baki sanni ba, ai ni ba wanda ya isa ya shareni, ko ka shareni kan ka ka mawa, shiyasa lokacin ina kamar ki banjin komai don saurayi yace ya fasa, don ba a kwana zai dawo, kar ki damu da sannu Dunkum zai kawo kanshi" daria Nasiba tayi tace "yo ai ko halinki ya isa ya kori saurayi, nasan lokacin ki an sha gwagwarmaya da ke" Nene tayi shewa tace "Kamar kinsani, duk samarina sun sha masifata, Kakan ki kadai ne ya kasa ya tsare yace sai Aminene" ta girgiza kai tace "Allah ya ji k'anka Mallam, ka cika masoyi na hak'ik'a" Nasiba tayi daria, Nene ta cigaba da bata Labarin kalan Soyayyar da sukayi da Kakan Nasiba.

Ashe yana binshi a baya har ya isa gida, yana jin duk abunda ya faru tsakanin Rafeeq da Nene, yanda ya fito daga gidan rai a bace ya sa shi binshi a baya har ya banka gate din gidan su ya shiga a fusace, Baba maigadi ya mik'e yana cewa Rafeeq Lafiya? Banza yayi da shi yayi hanyar dakin shi, Sallama Abbii ya ma Baba Maigadi, suka gaisa a mutunce, yace "gun Rafeeq nazo" Baba Maigadi ya kalleshi yace "Anya zaka so gannin Rafeeq a halin da yakr yanzu? Yanzu ya shigo gida rai a bace" Abbii yace "ba damuwa, ka min izinin ganinshi" Baba maigadi yace "Indai nine bakomai, yaro kana min kama da wata Aminiyata Aminene" Abbii yayi Daria yace "Ni ne Autan ta" Baba Maigadi yace "Haba biri yayi kama da mutum, kaind Mahaifin Nasiba ko? Ga kama nan wallah" daria yayi yace "barin ga Rafeeq" ya nuna mishi dakin Rafeeq da yatsa, kai tsaye Abii ya nufa dakin.
Chapter 52 · 0% Book details