← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 95

Sashe 17

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aneesa na nan har Maalesh yayi dropping Rafee'ah daga School, Kallon rashin Sani Rafee'ah ta ma Aneesa. Aneesa na ganinta tace sannu da zuwa sis" Rafee'ah tace "yauwa sannu" tana kallon ta, don somehow taga suna kama da Aneesa, Rafeeq yace Aneelurv, bari na miki introducing wannan, She's Jaki head, Diyar House Help din gidan mu ce" Rafee'ah ta bata rai tace "Hamma mana, wallahi sai na gaya ka da Uncle Hafiz" Rafeeq ya dinga daria, Aneesa tace share Yaya Rafeeq, kowa ya san kin fi karfin diyar house help, muje ciki ki rage kaya" Rafee'ah ta harari Rafeeq suka yi ciki ita da Aneesa, sai da ya bisu ciki, don idan Rafee'ah na gida baya barinta, yana son tsokanan ta. Tun daga rannan, Aneesa ta maida Gidan su Rafeeq gidan zuwanta, tana shishige musu, don Aneesa akwai ta da son 'yayan masu kudi, ga shi son Rafeeq ya kamata, yana hankalce da ita, bata san Rafeeq ba irinta yake so ba, a cewar shi son yara yan Secondary School ChildAbuse ne, kuji dan rainin wayau, ko shi din nawa yake?.

Tazo shiga parlorn, shi kuma ya fito hannun shi dauke da Plate din abinci, suka ci karo, Shinkafar da ke plate din ta zube, Aneesa tayi saurin durkusawa tana tattarawa, yace "Oh Sorry, wallahi ban gani ba" Hafiz ya dago kai don ganin wacece da muryan nan, defintely ba Rafee'ah bace, Haka kurum sukaji gaban su ya fadi dukkan su, suka kura wa juna ido, k'okari Hafiz yakeyi ya tuno inda ya san fuskar nan, don defintely ya san wannan fuskar, amma da yayi la'akari da wannan ba zata wuce shekarun Rafee'ah ba, yace a ranshi kila kama ne, to da wa? Oho!. Yace "karki damu, zan sa a share", tace "thanks" yace ke kawar Rafee'ah ce? tace "noo yaruwata ce" a ranshi yace no wonder suke kama, dama ina tunanin inda na san fuskar ashe don kamar da sukeyi ne da Rafee'ah nake ganin kamar na santa, kila dangin Mami Aisha ne. Da haka ya wuce part dinshi ita kuma ta shige cikin Gidan.

"Attention Everyone, this Is Hafiz Lema, yau zai fara aiki a wannan Company din,zaiyi Serving as General Manager, ina fatan zaku bashi hadin kai da goyon baya kamar yanda kuke bani" Director kenan Aisha Lema ke sanar da Co-workers dinta kan sabon Manager da aka samu, ta nuna ma Hafiz Office dinshi, ta shige nata. Waya ta kira reception, take tambaya har yanzu Secretary ba ta zo ba?" aka ce "eh bata zo ba" tace ina ne manta immediately ta na zuwa" yes madam.

Da sauri ta shigo Office din Madam, tace "Madam kiyi hakuri, Wallahi-" Hajia Aisha Lema ta katseta ta hanyar daga hannu, tace "Issokay, dama ince miki anyi sabon GM, kije kiyi filing credentials dinshi, and kiyi documenting Account dinshi, and ki bashi Constitution of his Office" Cikin ladabi Secretary tace "yes Ma" ta amsa files din daga hannun Madam, ta karanta Sunan da ke jiki 'Hafiz Ibrahim Lema' a tsorace ta dago kai ta kalli Madam dinta, hajia Aisha na lura da ita tace "yadai, Secretary?" ta k'irk'iro murmushi tace "bakomai", ko kina mamakin Sunan ne? Ba abun mamaki bane, Hafiz kanin mijina ne, Yayan Zaid ne, yayi dan tafia ne sai yanzu ya dawo. Murmushin da be kai zuci Secretary tayi, tace "i'll go ahead" ta fita, tayi kan desk dinta.

Hannu bibiyu ta dafe kanta, tunani ya cika mata k'wanya, Hafiz lema ya dawo? Hafiz lema zai bata mata shiri, Hafiz lema zai wargaza mata duk wani Plan din da zatayi kan Lema Family, kaii ba zata yarda ba, tana da advantage kan shi, she'll use it against him, zumbur ta mik'e ta harhada files, tayi Office din GM.

Sai da ta k'wankwas kafin ta shiga da Sallama, a yayin da Hafiz ke waya da Zaid, be dago yaga ko wacece ba. Wuri ta samu ta zauna tana karantar Hafiz, Ya Chanza, yayi kyau ya kara haske da sanin da mishi a da.

Hafiz ya katse wayar ya juyo da kujerar sa, da murmushi ta kalleshi tace "Good Morning Sir" zumbur Hafiz ya mike cikin firgici ya nuna ta da yatsa yace "Saudah" tayi murmushi ta mik'e tana fari da ido tace "Don Hafiz Lema feezoboy, its good to see you again" Hafiz ya dan sausauta murya yace "Sauda what are you doing here?" ta daga kafada tace "i work here" yace "Sauda what are you upto?" tace "nothing much, i just want to give our daughter a proper life?" a rude Hafiz yace "What?, me kike cewa? Tayi darian 'yan duniya tace " Our love bore fruit, da ka tafi ka barni, ka barni da cikin diyarka, yanzu kuwa ta zama 'yar budurwa cos she's 18 now"

Darian takaici Hafiz yayi, yace ke Saudah, na sanki da duniyanci, i wont let you blackmail me, ko kina so kice min ko a lokacin da nikadai kike tarayyah, kar kiyi tunanin na manta ko ke wacece, ina sane dake" tace "nasan zakayi tunanin hakan, amma ina da proof Aneesa diyarka ce" ta ciro wayarta fa lalubo hoton Aneesa ta mika mai, tace "gashi duba kagani, duk wanda yaga wannan ya san Jinin Lema ce, don ba ta da maraba da Rafee'ah Lema. Hafiz cikin rudani ya amsa ya kura wa Hoton Aneesa ido, ya gane ta, itace ya gani a gidansu kwanakin baya, tabbas wannan gudan jinin shi ce.

Ya dago kai yace "tasani?" tace "aa bata sani ba, she believes you are dead" yace "Sauda, gaya min gaskia, what are u upto? me kike shirin yi?" tace "its simple, So nake Habib Lema ya aureni, and you going to help me da taimakon ka zan shiga Gidan shi matsayin matar shi"

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg2⃣3⃣

Hafiz ya Sauke Numfashi me nauyi, tunda yazo Office ya kasa tab'uka komai, yana tunanin Zancen su da Sauda na jiya, ya na tsoron ta fito masa ta bayan fage,ya na gudun ta ma 'yan uwan shi wani mugun abun, har ranshi yana shakkun Sauda, be gama tunanin shi ba ta turo k'ofa, da Sallama, firgigit ya amsa, zama tayi a kujerar da ke fuskantan shi, tace "Good Morning Baban Aneesa, da fatan kayi baccin da ka dade bakayi ba" Hafiz yace "Sauda, ki bar wannan maganan, i'll pay u ko nawa kike so, just disappear from our lives" tace "sam, hakan ba zai faru ba, Dole ka dau responsibilityn diyar ka, dole ka bata rayuwan farin ciki, dole ka inganta mata rayuwar ta, idan ba haka ba, wallahi ba zaka ji da dadi ba" a dan tsorace yace "me zakiyi" ta yi daria tace "zan kaita gaban Yayan ka, ince ga diyar Hafiz lema, shekaru 16 da suka wuce kayi min fyade, ka ga ko zaka koma gidan jiya, yanuwan ka za su kara tsanan ka, su tsangwame diyar ka, niko ina iya hallaka duk wanda zai tsangwami diyata ko yayi gigin kiranta da Shegiya".

Zufa ya shiga keto ma Hafiz, ba zai so Sauda ta tona mai asiri ba, yana tsoron Sauda ta ma Yanuwan shi wani mugun abu, jikin shi duk yayi sanyi, ya karaya sosai. Hafiz ya ja goron numfashi, yace "Sauda, ni zan aure ki, muyi rayuwar mu da diyar mu tare ba tare da kowa ya san diyata bace, Muyu aure Sauda please" ta fashe da wani mugun daria tace "Hafiz, na fi karfin ka, Wallahi ni ba tsarar ka bace yanzu, yayin ka ya riga da ya wuce, ni Habib Lema nake son aure" Hafiz yace "wai Sauda mesa kike haka ne? Bawan Allahn nan be miki komai ba" ta mik'e tace shikenan, tunda kaki yarda da deal din da na maka offering, bari inje in sanar da su gaskian lamarin, barin fara da uwar dakinku Aisha Lema, tana cikin Office ma yanzu haka"

Cikin zafin nama ya damk'ota yace "aa dan Allah Sauda, kar ki min haka" cikin daga murya tace "ka sake ni" a hankali yace "OK, i will do what you want" tayi murmushin cin nasara tace yauwa ko kai fa, zama tayi tana mai duban shi cikin yanayi na yaudara, ta ciro wani kullin takkarda daga cikin jakkarta ta mik'a mishi, tace "ka sama yayan ka a abinci ko abun sha, make sure ya ci ko ya sha" ya kalleta cikin rashin fahimta, tace Amsa mana ko kana tunanin zan yi poisoning din shi ne? Son shi fa nakeyi, idan ya mutu ya zai aureni? Ba zan taba kashe shi ba coz ina sonshi, so cire wannan tunanin a kanka" ya amsa yace "Sauda, i dont want anyone to get hurt" ta mike ta dauki jakarta tayi hanyar fita, har ta kai bakin k'ofa ta tsaya ta dan kallo shi, tace "noone is getting hurt, i promise".
Haka Hafiz ya dinga juya maganin nan, ya na sak'e sak'e a ranshi.

Daily Tea din da Alhaji Habib ke sha da daddare Mami ta kawo mai, yana karatun Jarida, yace "thank u Shatu na, u ar d best" tayi daria, tace "kafin a min amarya ko?" yayi daria yace "ke kinsan ba wata bayan ke" tace "ahhh bansani ba" ta mik'e tace bari inje in dafa ma Rafeeq ko indomie ce, nasan Rafee'ah ba zata dafa mai ba" "Indomie kuma? Ba abinci ne? tace "kasan yau Taliya akayi" "Assha, ni wannan abu na Rafeeq bangane mai ba, zai ci indomie amma ba zai ci Taliya ba? Toh meye maraban Dambe da Fada?" tayi daria tace ai kai ka shagwaba shi haka" yayi daria yace barin min first Son dina" tayi daria ta shige kicin".
Chapter 17 · 0% Book details