Sashe 48
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*Katsina*
"Shin Sallama ake ko fito? (whistle) inji Nene, daga bangaren shi ya buga tsaki da yaji muryan Nene, ji yayi kamar ya koma, don dai zuciyar shi na tunzura shi yazo ya ga Seebi da ya juya wlh, don Wulakanci ya daddage yayi Sallama amma sai tace yana whisir? Wannan tsohuwar na da damuwa, be bi ta kanta ba ya sake Sallama cikiciki, tace "Shin, an amsa maka ka shigo mana" tsaki yayi ya nufa cikin gidan, sanye yake da 3quarter, Nene na ganinshi ta chanza fuska tace "Touuu, nidai ince, nasan za'a rina naji sallama kamar fito, ashe su dunkum ne dangin tsaka" Ya kalleta sosai yayi kamar be jita ba, tace "ka tsareni da ido, to ai sai ka zauna ga tayani gulma nan" ya tsaya yana mata kallon rashin fahimta ta nuna mai kujera tace cewa nayi ga kujera ka zauna, guntun tsaki yayi ya zauna, yana kallon saitin dakin su, yana jiran yaga fitowar Seebi, Nene ta zauna kan tabarma kusan minti 15 be ce komai ba, da taga shirun yayi yawa ta daure tace "ina Malush?" shiru be amsata ba, a ranta tace ko dai be ji ni bane? Ta bude murya ta sake cewa "Nace ina Malush?" shiru ya mata, Nene ta bude baki cike da mamaki tana kallon shi, chan k'asa taji yace "Yana Kano" Lallai kawai tace tana jinjina kai. Shiru ya sake giftawa har fiye da na dazun, kusan minti 20.
A karo na uku (3) ya sake jin K'arar waya, tun dazun wayar ke ringing tana katsewa, k'arar wayar na damunshi, kuma shi yak'i tashi ya tafi, dan guntun tsaki yayi ya kalle ta yace " Wai ba karar Waya nakeji ba?" Nene ta hau salati, tace "kai don Manzon Allah? Wai wayace? Yo tun Shekaran jiya nake jin irin k'arar nan banyi zaton waya bace, wai ashe wayar Nasiba ce" be dai ce da ita komai ba har wayar ta sake ruri, cigaba da surutu tayi tana bashi labarin yanda takejin k'arar wayar kullum, ta ma mance rashin jituwar su, yace "ai sai kije ki dauko ga wayar chan an sake kira" da gudu ta ruga daki, amma kafin taje ya katse, kan Wardrobe ta ciro wayar, tun randa Nasiba ta bata wayan ta aje a sama ba ta sake bi ta kan shi ba, ta fito da wayar a hannu ta mika ma Rafeeq "kaga dunkum, duba min kagani waye? Kamar bazai amsa ba, sai da ya gama kallon wayar a hannunta kafin ya amsa, ya jujjuya wayar a hannun shi, a ranshi yace "Tecno, sai k'arar tsiya" ya bude wayar, 34 Missed Calls ya gani, accordingly ya duba Missed Calls din, Abbina Uncle Zaid, Ummina, Ya-Maalesh Miemee, Usheey, Hamma na, a ranshi yace Hamman ta? Messages ya duba, Daga na Uncle Zaid, sai na Maalesh sai wanda ya mata, a sama yaji muryan Nene, inda take cewa "Shin zaka gaya min wanda ya kira ko sai ka gama latse latsen wayan, ko no engilish? Guntun tsaki yayi, da kyar yace "wai Abbi" tace "Mahammadu ne, baban Nasiba latso min shi" a ranshi yace wa ya tambaye ki? Ya mata dialing numbern, ringing daya suka dauka, cike da doki tace "Halo, Mahammadu ya kuke? Yanda Nene ke waya zar takaici, kamar bakauyiya, hakan yasa shi mikewa don tafia, ya kalleta yanda take daria, a hankali yace "kina da matsala" karaf kan kunnen Nene, tace "da wa kake? Ni ke da matsala? Matsalar ubanka?" be tsaya bi ta kanta ba ya fice daga gidan, ta bi bayanshi har zaure, "tsaya mana, rasa kunya beran kitchen, da ba don ina kunyar Zaidu bawan Allah ba yau da sai na maka mugun duka, in maka lagalaga, in kuma kai ka Asibiti, yanda kayi jiyyata nima inyi jiyarka dan banten uba" kwatakwata ta manta da wayar da takeyi. Su har sun gaji da Magana sun kashe. Ta dawo ciki tana mita, ta kafa waya a kunne, Hello, daidai nan Seebi ta sake kira da wayar Abbi, a firgice Nene ta cire wayar daga kunne don k'arar ya cika mata kunne, ta latsa wayar ta kafa a kunne, tace "hallo Mahammadu" Seebi tace "Nene na nice" cikin masifa Nene tace "to dan kece sai ki dod'en kunne da kira?" Nasiba ba ta damu ba tace "ke da wa kike fada, naji kina ma wani masifa?" nene tayi tsaki tace "ni da wannan dunkum dangin tsakan mana, wai ni zai kalla yace ina da matsala" Seebi ta gane da Rafeeq take, da Sauri tace "shi yazo?" tace "tun tafiar ki kullum sai yazo, ya tasani gaba yayi ta kallo kamar Tb, shine zai ceman wai ina da matsala, ai wallahi da ya tsaya da sai na bubbuge shi" Nasiba ta shiga tunani a ranta tace "Allah sarki Hamma, ni yake nema, i made a mistake da ban sanar dashi zanzo Kd ba" Nene tace sai ki man shiru? Dallah bani Uwar taki mu gaisa" da sauri tace "Ahh Nene ga Ummin ba sai kin zaga man Uwa ba". Daria Ummi keyi ta amsa wayar suka gaisa da Nene. Seebi kuwa ta tashi ta fada gidan Mami.
_Malali Kaduna_
Haka Nasiba zata zauna tayi ta ba Mami labarin Rafeeq, wani zubin taji tausayin shi wani zubin tayi daria, kamar yanzu Nasiba ta bata labarin Dramar Nene da Rafeeq, Mami tayi dariya harda k'walla, tace "ai Nene ce daidai shi" tana burgeni, Seebi tace "ai haka mutane ke cewa, wai Nene na na burge su, don dai basu zauna da ita bane, da tuni ta gudire su, Nene is very Annoying Wallahi, don dai kawai tana da ban daria, amma kwana daya zaki yi da ita duk zakiji ta isheki" Mami tace "ba wani nan, ni dai ba zata ishe ni ba" Seebi tace "hmm, wallahi Mami ba zaki gane ba" wayar Mami tayi ringing, Nasiba ta je ta dauko mata kan dining, Zaid England ne ya fito a Screen, Nasiba tace "Mami ga Uncle Zaid" Mami tace dauka mu rudar dashi" Seebi ta dauka wayan "Assalam Alaikum Uncle Zaid" da sauri Zaid ya duba Screen din wayan ya ga dai Mami ya kira, to ya yake jin muryan Seebin Nene? To ko kiran ya yi roaming ne ya koma numbern Seebi? Tambayoyi da dama, da k'yar ya Amsa Sallama, yace "Seebin mu nida Nene" tace "lahh ya akayi ka gane?" "your voice is always on my head, ba zan taba manta da voice dinki ba" taji kunyar maganar shi amma sai tace "arent you suprised? Ba number na ka kira ba fa? Zaid ya tashi zaune yace "Noo way" tace "Yes Way, bari ma ka gani" ta mik'a ma Mami wayan ta mata alama da bara taje gida ta dawo, Mami ta amsa tana Daria, yace "Mami how is this possible? You met Nasiba?" tace "Ehmana, what makes you think i wont find my Sister Inlaw? Or ince daughter na, don diyata ce, kai ne siriki na" yace "shhh Mami kar ta jiki" tace "kar ka damu ta je gida, mak'otan mu ne, Yayan Anan" da mamaki yace "dama Nasiba yayan Anan ce?" tace "iko na Allah" yace to Mami ya akai kuka saba da juna haka? Mami ta kwashe labarin da Nasiba ta bata duk da briefly ta bashi, labarin da shi kanshi Zaid be sani ba, ya jinjina kai, Mami tace "Wallahi Zaid baka ga yanda take son Ayman ba, yanzu haka tana bayanta ta goya ta" Dadi ya lullube Zaid, duk me son shi, to ya so Diyar shi, nan ya ba Nasiba wani matsayi a zuciyar shi, Mami tace "Allah ya sa yanda take son Ayman ta so babanta, ko da yake dan k'anina haծaծծe ne, ba macen da zata k'i shi" daria Zaid yayi yace "easy dai, sai na dawo zan sanar da ita _sirrin dake raina_" tace "sai ka dawo, yanzu sai yaushe?" yace "don sun raina mu sun k'ara mana additional 2weeks, sai next month in Allah ya yarda" toh Allah ya yarda, nan sukayi fira sukayi Sallama.