← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 95

Sashe 61

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

_Bibilicious Biebee,_
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg5⃣0⃣

Zaid ya daga hannun shi alamun ban hak'uri, yace "Nenen mu DonAllah kiyi hak'uri" Inaaa sam Nene Hankalin ta yayi nisa ta ba ta jin abun da Zaid ke cewa, haka ta cigaba da kilar su, Zaid yayi saurin cewa "Nene kin ta6a cewa idan ina son wani abu a gunki, kar inya shakkan sanar dake, ko menene zakiyi min shi, in har befi karfin ki ba, Nene wannan ne abu na farko da na fara tambayanki Nene DonAllah, ki bar su haka, kiyi hakuri, sun ladabtu, na tabbatar ko me suka miki sun gane kurensu" Kallon Zaid tayi tana nazarin shi, chan kuma sai ta yada Chazar tace "Wallahi, sunci darajar ka, kai kadai ka isa ka hanani wlh, don ko Mamman ya dawo duniya yanzu sai mun kai ruwa rana kafin zan hakura wallahi" Zaid yayi murmushi yace "Nagode Sosai" Saude ta tashi tana kakkabe jikinta, Aneesa da Meema ba su bar gurnanin kuka ba Saude ta tuna cewa ba abunda Tsofin mutane ke tsoro kamar Yan sanda, tace "Wallahi Yan sanda zan kawo miki, sai kinyi nadamar ta6a Lafiyar jikin mu" aiko Nene ta tunzura tace "YanSanda? Naciii uwar Yan sanda, naci uwar hukumar jami'an tsaro dukkansu, Kinci uwarki idan baki dauko mun 'yan sanda ba, ke bari ma in k'ara laftar ku yanda zaki dauko mun su da hujja" ai ko Nene ta wawuro chazar ta, haba zo kuga relay tsakanin Miemee Saude da Aneesa, har suna tura junansu ko wannen su na rigerigen fita daga gidan Nene, a wannan karon ba Rafeeq ba hatta Zaid sai da ya dara.
Nene tace "kina iya fitowa me tsoro kamar farar kura" Simi simi Seebi ta fito daga dakin rungume da Ayman da ta ci kuka ya gaji, Rafeeq yayi k'okarin amsarta Ayman tak'i yarda sai dai Babanta ya amsheta ya sakata kan kafada, don yau taga tashin hankalin da bata taba ganin irinshi ba.

Zaid ya nisa yace "Wai me ya faru ne? Me ya kawo su Meema gidan nan?" Nene tayi charap kamar jira take ta shiga karanto ma Zaid abubuwan da suka faru tun bayan shigowar su Aneesa, ran Zaid ya 6aci matuk'a sai ya fi ganin laifin Rafeeq cikin 6acin rai yace da Rafeeq "why didnt you stop them da suka fara zagin Nene? Meyasa baka hana su ba? Kamar bazai amsa shi ba, sai dai ya daure yace "Saboda i know she'd handle them in her ways, which she did" ran Zaid ya 6aci zai sake magana Rafeeq yayi saurin cewa "Look Uncle i tried to warn them, i even told them to leave, but they didnt want to listen so i let them be, ko ba haka ba Neh-neh?" kamar ta san me ake cewa tace "Hakane Zaidu Bawan Allah" nan Zaid ya dai bata hak'uri ya ba Nasiba Hakuri, ya kalli Rafeeq ya galla mai harara shi kuwa ya dauke ido yayi kamar be ganshi ba, Nene tace "ka bar hararan shi, ai ni yau Dunkum ya burgeni, kasan shi ya mik'o min Chazar, kuma ya fassara min abunda suka ce" Rafeeq yayi dan guntun tsaki kamar ba shi ya gama daria dazun ba, Nene tace "Su dunkum ashe ana ganin hak'oran ka? Wato kai mugun abu ne abokinka ko? Sai kaga abun mugunta kake daria, ai da nasani da na shafda maka a gadon baya sai kayi darian da kyau" Zaid da Seebi sukayi daria shi kuma ya daure fuska.
Chapter 61 · 0% Book details