← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 95

Sashe 33

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga nesa ya ga Rafeeq, da sauri ya k'arasa gunshi, "Rafeeq thanks for coming" Rafeeq be ce mai komai ba illa binshi da yayi da ido, alamun ka min bayani, Zaid kuwa yak'i cewa komai don ya san Halin Rafeeq, yana iya ce mai wata zaiyiwa Assignment yace ba zaiyi ba ko kuma yace be iya ba k'arshe ya tafi ya barshi, shiyasa Zaid be ce komai anan ba, k'ila idan a chan ne yaji kunyar Nene da Nasiba ya mata, duk da ya san ranshi sai ya baci, yace "please ka biyoni, ganin asarar cewa ina zamu?ko me zanyi? Yasa Rafeeq bin Zaid a baya ba tare da ya ce uffan ba, har Soron Gidan Nene, Zaid yayi Sallama, cikiciki Rafeeq yayi Sallaman shima Nene ta amsa, Zaid na gaba Rafeeq na biye dashi kan shi a k'asa, Nasiba na ganin R-Lema tayi Zumbur ta tashi tsaye, Nene tace "Lahh Zaidu Bawan Allah, wanene wannan me kama da kai?" kallo ba ta ishe Rafeeq ba, Zaid yace "Rafeeq ba ka gaida Nene ba" ba tare da ya kalleta ba yace "ina wuni"ciki ciki Nene ta amsa tana mai wasa, dauke kai yayi ya sauke shi kan Nasiba, kallo daya ya mata ya dauke kamar be taba ganin me irin halittar ta ba, Rafeeq da ya k'osa yaji me ye amfanin zuwan shi gidan nan ya kalli Zaid cikin tuhuma, Zaid ya k'i yarda su hada ido, don yasan shi yake kallo, ba tare da ya kalli Rafeeq ba yace "Son, Assignment ne ya gaggari Seebi, nima na gwada tawa fasahar na kasa, nasan you are in good in Calculus, shine nace bari in kiraka ka taimaka mata DonAllah" Waiyo Allah kuzo ku ga bakinciki kwance kan fuskar Rafeeq ji yake kamar ya dora hannu a kai ya sa ihu saboda takaici, wai me ya sa Uncle Zaid ke mishi hakane? Zaid kuwa har yanzun ya ki kallon Rafeeq din balle ya san halin da yake ciki, "I am sorry" ya furta a hankali don ya san Rafeeq din shi yake kallo.
(Readers me kuke ganin Rafeeq zaiyi? K'ila tafiar shi zai yi ba tare da yace musu komai ba, don da Alamu Uncle Zaid ya gama kashe Rafeeq)

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg3⃣4⃣

Kusan Mintinu Biyu Rafeeq na tsaye, shi be ce komai ba shi be tafi ba, Nasiba ba tayi mamaki ba, don ta san halin Rafeeq na shariya da k'yaliya, Nene kuwa ido ta sa ma Rafeeq ta kasa gane me ke shirin faruwa, har Yanzu idon Zaid na kallon Gefe, Rafeeq da takaici ya gama rufe shi ya hau tunani, tabbas da wani ya mai abunda Uncle Zaid ya mishi da ba abun da zai hanashi barin gurin, Amma Uncle Zaid ne, ya fi K'arfin Wulakanci a gunshi, ajiyar zuciya yayi ya mik'a ma Nasiba hannu kamar me rok'o, Nasiba tace me zan baka? Rafeeq ya dan yi guntun tsaki, Zaid yayi saurin kallon su yace da Nasiba "bashi question Paper din, da sauri ya dauko ta bashi, ya amsa ya karanta, a ranshi ya yi tsaki yace Question din is straight forward, i dont knw why some people are dumb, ba su san komai ba, ji wannan simple Question din,(ni bibi nace ba kowa bane kamar ka ba dan rainin wayau) wata zuciyar tace harda Uncle Zaid fa, a ranshi yayi dariya, amma a baiyane fuskar nan tamk'e tamau.
Kan tabarman ya hau, ya ciro biro cikin wandon shi, ya duk'a ya fara solving question din, tunda ya fara rubutu be dago ba sai da ya gama, yana gamawa kuma ya mik'e ya zira takalman shi ya bar Gidan. Zaid ya bishi da sauri, Nene da Nasiba suka bishi da ido, ita Nene Mamakin Wannan yaron Zaidu BawanAllah take, a ranta tace ko kurma ne? Nasiba kuwa Mamakin da takeyi yanda tafi Awa 5 tana kokarin yin wannan Assignment din ta kasa, amma shi cikin mintinan da basu wuce 7 ya gama komai, lallai ta jinjina mai, shiru-shirun shi ba a banza ba tunda ya san abunda yakeyi, haka kurum taji Rafeeq ya burgeta, ta durkusa ta dauki Papern, rubutunshi ta bi fa ido, neatly kamar irin rubutun Computer, tabi steps din da yabi, taga abun very clear, kawai sai ta tsinci kanta da Murmushi a hankali ta furta R-Lema. Nene da ta zuba mata ido, tace "Toooooooh, ke kuma gamo kikayi? Nasiba ta fashe da daria.

Ko da ya fito har Rafeeq ya kai bakin motar shi, Zaid yace "Rafeeq" chak ya tsaya ba tare da ya juyo ba, Zaid ya iso har gabanshi yace "ka saurareni, nasan na maka laifi, na maka karambani, kayi hak'uri" dan guntun tsaki Rafeeq yayi ba dan komai ba don Zaid zai sa shi magana yace "ka isa da ni ne, bakomai, stop apologising" ya shige mota ya ja ya bar Zaid tsaye, Zaid kuwa dadi ne ya lullube shi, lallai Rafeeq is improving, shi a zaton shi fushi zaiyi dashi, amma Rafeeq ya bashi mamaki kuma yaji dadi, a ranshi yace"Allah ka kawo ma Rafeeq Sauyi" ya juya ya koma gidan Nene. Ya na shiga Nene ta tare shi da maganar Rafeeq, "Nace Zaidu Bawan Allah, shi wannan fa?" Zaid yace "Dan Yaya na ne" Nene tace baya magana ne? Ko kurma ne? Zaid yayi murmushi yace "yana Magana" Nene tace "to ya na ganshi haka kamar wani Zararre, ji uban gashin da ya ajiye, ko ni Mace ya fini, shi ko bai da lafiya ne?" Nasiba ta kasa kunne don jin me Zaid zaice don ta na san sanni meyasa Rafeeq yake haka, Zaid yace "haka yake, miskili ne" Nene ta jinjina kai tace "Lallai kam naga Alama, Shekaru na 68 ban taba ganin Miskili kamar shi ba, ya ci a bashi Sarkin Miskilai" Daria sukayi duka, Nene tace "Bari in tashi in zubo maka Tuwon Masara miyan kuka da na dafa maka" Zaid yayi murmushi yace "yauwa Nenen mu ni da seebi kadai".
_Bayan kwanaki Biyar_.

*UMYU Katsina*

"Nasiba Muhammad, MCB 1220" Gabanta ya buga ya fadi a lokacin da Course Tutor ya sake kiran sunanta a karo na biyu, a hankali Miemee tace "Seebi ke fa ya ke kira" jikinta ya hau rawa sosai, idonta ya ciciko da hawaye, ai ba inda zataje, kuce bata zo ba tunda ba sani na yayi ba, cikin karaji lecturer yace "Where is Nasiba1220?" bata san lokacin da ta mik'e tsaye ba saboda ya firgita ta sosai, yace "are you Nasiba?" kai ta daga alamun eh, yace come down here, gabanta ya tsananta faduwa, bata san me tayi ba, k'ila batayi assignment din ta da kyau ba, jiki na rawa take tafia, all eyes on her, haka ta daure ta karada gaban stage, karo na farko da ta fara missing Nikabin ta, ta tsaya gabanshi, ya mika mata Marker bayan Yayi copying Question din da ya basu, yace "solve this"Nasiba tayi Adduoin ta ta fara rubutu kan Board, dama tayi mastering Solution din da Rafeeq ya mata, har sai da ta gama komai, Lecturer ya ciro scripts dinta ya mik'a mata, ta amsa ido ta zaro, *20/20* tagani murna ya ziyarce ta, yace "give her a round of applause" Aji ya kaure da tafi raf raf raf. Yace shes the only one that scored 20/20 apart frm her none of you made it to 15/20, am proud of you" A hankali tace "thank you sir" ya zaro 2000 a aljihu yace "have this" da sauri tace "no sir, you dont have to This" ya tsare ta da idanuwa ta amsa tayi godia, aji suka tafa mata, kamar ance ta lek'a window, tana lekawa ta ga Rafeeq ya zo wucewa, ta kalli Lecturerr tace "excuse me please sir" da murmushi yace Goon my dear, da sauri ta fita daga Ajin, sauri sauri, gudu gudu ta cimma shi don ta san ko kiranshi tayi ba zai juyo ba ga idon mutane a gurin, sai da tazo gab dashi ta mai Sallama, kamar ba zai tsaya ba ya tsaya tarw da juyowa, suna hada ido cikin in ina tace "Erhm, dama ina son yi maka Godia ne, anyi Marking scripts kuma nikadai naci 20/20" ta karasa tare da mika mai takardan hannun ta, ido ya tsareta da shi, ba tare da ya kalli papern ba ya juya zaiyi tafian shi, da sauri tace "Nagode Allah ya saka da Alheri, Allah ya kara basira" Chak ya tsaya, ita kuma ta juya ta ta fi, da sauri ya juyo amma har tayi gaba, ya dade rabon da yaji shi cikin Wannan yanayin, a hankali ya furta *"Me ke faruwa*?"

*MAFARKI*

"Baiwar Allah", taji wata zazzakar murya tayi kiranta, Nasiba ta juyo ta kalleta,sanye take da fararan kaya masu alfarma, fuskarta sai kyalli, tace "donAllah taimako nake so ki min, idan kika taimaka min Allah zai taimake ki, Nasiba tace wani irin taimako kike so in miki? Tace "wallah, bashi naci a wani Shago, wata rana na je siyan lemo lacasera, na bada dubu aka ce ba chanji, in tafi idan na samu na kawo, toh har yau Allah beyi na kai ba, yanzu kuma nayi nisan da ba zan iya dawowa in ba mai shago hakkinshi ba, ki taimake ni ki kai mai Nera 120, kinsan Allah na yafe hakkin komai banda hakkin mutim, Nasiba tace " bakomai, a wani shago ne?" tace " Masanawa Supermarket,Umaru Musa" toh InshaAllah zan biya miki, to ya sunanki? Don yanda zanma mai shago bayani" tace karki damu, kedai kawai ki bada da niyyar ni ki ka biya ma wa, hakan ya wadatas" Nasiba tace "Zanyi hakan InshaAllah " tace nagode". Nasiba ta muskuta daga baccin da tayi, don ta jima batayi mafarki ba, ta koma bacci.
Chapter 33 · 0% Book details