Sashe 93
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa harda Auren Maalesh da Miemee, Auren da ya sa su Rafeeq zuwa tun Sati 2 kafin Biki, Rafeeq da Seebi sun taka rawar gani a bikin Maalesh, Maalesh ya na nan zaune a Kaduna inda yake Aiki a NNPC, ya kuma samar ma Miemee transcript tana nan aji Biyu a nan Jamia'ar Kaduna KASU, suna matuk'ar son junansu kuma suna zaman Lafiya.
Usheey fa? Usheey itama tana nan an Sa Mata biki nan da wata Biyu zasu sha Biki da Faisal abokinsu Maalesh, anan Katsina yake aiki.
Rafeeq ya gama MSC dinshi a Biotech, dama shekara Daya ne, Ba yanda Seebi ba tayi ba da Feeq ya dawo Naija yayi Service amma yak'i, ya kan ce ba zai iya barinta ita kadai ba, kuma ba zai yanke mata karatu ba, so zai jira sai ta gama Karatunta sai su koma gabaki daya suyi Service din a tare. Kasancewar Rafeeq akwai shi da k'okari da k'wazo ya saye zuciyan Professor Nicklaus, Saboda k'warewar Rafeeq a harkar Biotechnology, Professor Nick yayi mai hanya lokacin da zaayi wani project, don he believe zaa samu good outcome daga Feeq, aiko it was Successful daga nan *World Bank Assisted Project* suka dauke shi aiki kan fannin
*DNA Vaccine on Tryponosomiasis.
Aunty Zee ta haifi danta Namiji inda yaro yaci Sunan Yayan Babanshi wato Hafiz, Abunnan ya ma Alhaji Habib Dadi, nan take ya Mallaka ma Hafiz Zaid Lema Gidan shi na Kaduna. Aneesa na son Hafiz Sosai, Ayman tayi wayau sosai har an sakata a Kindergarten, Mamarta kuma ta gama Housemanship dinta yanzu Service takeyi nan Kaduna.
'Yan Biyun Mami kuwa sunyi bulbul dasu gwanin shaawa, ga Yan biyu da farinjini, Amma kyaunsu ya shahara, sai da Nene ta fara tofa musu ruwan Addua saboda bakin mutane.
Daddy ya shawarci Abii da su dawo Katsina da Zama, tun bayan Bikin su Rafeeq, yanzu Abbii da Ummi suna nan Gidan Nene, Abbi ya zama dan kwangila, dama Da Iliminshi na Architecture, shike Contract din wasu Zane zanen Gwamnati, yanzu shima ana damawa dashi.
Nene kuwa tana Gidan Lema, Mami ta rok'i Abbii da su bar mata Nene, Abbii kance ai Nene ta kuce, idan kuma su Feeq suna Waya idan ta isheshi sai yace "ta tafi gidanta, tana takura ma K'annenshi da hayaniyarta" sai tace "in kaga na bar Gidan Lema, toh cema Maza akayi gani" Sai ya kalli Seebi cike da rashin Fahimtar don be gane Hausar Nene, Seebi sai tayi daria tace ta na nufin "Sai dai a fitar da gawarta, In otherwords suna nan tare Mutu ka raba" tabe baki yakeyi kawai.
*** *** ***
"Zaid Lema Wallahi dagaske, nakeyi, ka sa min Mata, kasan ni tun bayan Rasuwar Halima(Matar shi) Aure ya fitar min akai, Mama tayi fadan tayi Nasiha amma shiru, har tana cewa ko Aljanna ta Aureni" Daria Sosai Zaid keyi, yace "Bawani Aljanar da ta Aureka, kawai dai ka fi maida kanka Wurin Bussiness dinka da Aiki, gashi Kudi sun ma Yawa kai ba d'a ba Mata" Daria Sosai AbuSadik yayi yace "Ai shikenan yanzu na baka wuk'a da Nama, ka zaba min Mata Daidai da ni" Zaid yace "wai dagaske kake?" Abu Sadik yace"Wallahi dagaske Nakeyi" Yace "Toh shikenan, na baka Diyata Aneesa, Ajin ta Biyu a Jamia," ya ciro wayarshi ya nuna mai hoton Aneesa, nan da nan Abu Sadik ya Ji Aneesa ta mai, suna kama da Zaid abunka da Jini, AbuSadik ya ba Zaid hannu suka Kashe, Allah nawan? Kaii wannam ta hadu wallahi, ta min, amma Yarinya ce" Zaid yayi Murmushi yace kai dai kawai ka shirya muje Katsina Wannan Jumaar.
Haka UncleZaid da Abu Sadik suka je Katsina ran Jumaa, sai da Zaid ya gabatar da AbuSadik a matsayin Abokin Aikinshi, kuma ya na so a bashi izinin neman Aneesa, Daddy yaji dadi amma yace "A nema So wurin Yarinya, idan ta Amince shima ya Amince ba zai ma diyarshi Auren Zumunci ba".
Aneesa na zaune a daki tana chatting Nene ta shigo tace " Anusa, tashi kimtsa ga bak'o kinyi" Anee ta zaro ido, tace bak'o Kuma? Tace "ke dallah yi sauri tare suke da AnkulZaidun ku" Jiki Sanyaye Aneesa ta yafa gyalenta, tazo wucewa taji Mami na kiranta, ta karasa gunta tace "ki kwantar da hankalin ki kinji diyata, InshaAllah Alheri ne" gyada kai tayi, ta nufa Parlorn k'asa, Zaune ta gansu daga chan gefe ta durkusa ta gaida su Uncle Zaid yace "Zo nan Daughter, zauna nan" ta matsa ta zauna kusa dashi yace "ba tare da bata lokaci ba, Aneesa, kar ki manta nace miki ni Zan zaba miki Mijin Aure, ba wai don ke ba zaki iya zabar ma kanki abin da kike so ba, ba kuma don ke baki da samari ba, zan zaba miki wanda ya dace dake, wanda zai kular min da ke, you are my Responsibility, in kin yarda da hakan toh Gashi na kawo miki shi, Abubakar Sadik, Abokina ne, wurin aikin mu daya, nasan kingan shi lokacin Bikina, he's my trusted friend kuma na san zai kula dake, ki bashi hadin kai kinji diyata?" kai kawai ta gyada mai, Zaid ya mik'e ya fita don basu damar tautaunawa. Sun danyi maganar ganin bata sake dashi ba, daki ta koma. Mami ta bi bayanta, tace "Daughter ya dai? Mami Tsoho ne fa Shekarun shi 40, nidai gaskia yace ya bani time inyi tunani nidai banaso" Nene ta shigo tace "Ke dallah, Magidantan basun fi iya kaunar ba? Sun fi sanin darajar Mace, sunfi kula dasu, ki gwada ki gani zakiji dadinshi" Mami ma ta kara kwantar mata da hankali tana bata shawarwari har ta Amince. Magana ta kai gun Daddy, har ya sake kiranta don jin ta bakinta ta nuna mai ta Amince. A hankali A hankali ta fahimci AbuSadik wanda danyi ne shima, ya iya soyyaya kamar Chewinggum boys, son sji takeyi sosai, shima yana sonta, Daddy yace ya turo, dama jira kawai yakeyi don danginsa a shirye suke, nan da nan ya turo su, aka kawo kudi har rana aka sa biki wata 5.
Biki ya Matso Gata Aneesa ta samu, ba nuna wariya ko kyariya, haka Mami ta samar musu Visa to Dubai don yi ma Anee kayan Kitchen, Kasancewar Shafeeq da Shafee'ah na cin Abinci Sosai, Mami ta yayesu.
Biki ya matso su Feeq suka taho Naija Bikin Aneesa.
Mami ta shirya ma Bikin nan, haka aka sha shagalin biki aka daura Aure, aka dauki Amarya zaa kaita Kaduna, rannar ta sha kuka kamar ranta zai fita, ta rungume Mami da Daddy ta na musu Godia, don duk duniya bata da wanda suka fisu. Haka aka kaita Tamfatstsen gidan ta da ke Unguwar Dosa.
Bayan yan biki an watse Nene ta ja Seebi daki, tace "wai ya Seebi? Banji ba banga bayani ba?" Seebi ta kalleta cikin rashin Fahimta, tace "bangane ba" tsoki Nen ta buga tace "Ciki Mana" Seebi ta girgiza kai tace "Banda komai Nene" Nene ta kara buga tsokin, tace "ai nasan baki da komai din ai, sai zuba ido nake tun Wata 3bayan bikin ki shiru, Seebi kar dai Dunkum ya miki wayau ya na dirka miki maganin Daukar ciki, ku ga turawa yace be son haihuwa sai kin gama Makaranta" da sauri Seebi ta tashi, tace "Subhanallah, haba Nene, Haba Nene wani irin magana kikeyi haka, wallahi kar ki dauki Alhakin bawan Allah, Nene Allah ne be kawo haihuwar ba, shi ke bada wa, Wallahi kiyi istighfari ba daidai bane" Nene tayi shiru tasan bata kyauta ba, tace "kiyi hakuri, na damu ne, na zata kin biyewa Zamani ne kice ba zaki haihu ba sai kin shana, kar ma ki tada hankalinki kinji Seebin Nene, ai ana hakan, wasu ma sai sun kai shekara 10 da aure kafin suke haihuwa, balle ke yar shekara 1 da watanni, kar ki damu" Seebi tayi Murmushi tace dama banda mu ba, don Na san Allah na sane da mu" "to Allah ya kawo masu Albarka" ta amsa da Amin". Karo na Farko da yaji Nene ta burgeshi, tayi laifi an gyara mata kuma ta dauki Corrections. Allah sa ta daure,ya juya ya fasa shiga dakin yayi dakin Yan Biyu don musu Wasa.
BAYAN SHEKARA DAYA