Sashe 77
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Safa da Marwa Alhaji Habib ke tayi a tsakar dakinsa, Wannan wani irin musiba ce, ya zaayi Saude ta iya wannan cin Amanar? Ta yaya Saude zata musu haka? Taya zata Aure shi bayan tasan cewa Hafiz ne Baban 'yarta, Mami ta shigo ta dafa kafadar shi "Habibi, donAllah ka kwantar da hankali, daure ka sha ruwa gashi nan" Alhaji Habib yace "Shatu Sauda taci Amanata" "Shhh, ka sha ruwan nan, everything is going to be fine InshaAllah" ya karba Cup din hannunta ya kurba, "Sakinta zanyi, ba zan iya zama da ita ba wallahi" "DonAllah dont make any descision yet, you are Angry, kar kayi abunda zakayi dana sani" "da nasani? Shatu da nasani fa? Don na saketa? I never loved her, God i didnt even know why i got married to her, itama kwadayi ne yasata Aurena, idan ba haka ba meye zata dinga maganar Gado, gaskia ba zan iya zama da matar nan ba, ta zalunceni, Sakinta Zanyi, and Hafiz? How could he do this to us? "DonAllah ya isa Habibi, Hafiz ya rasu, please dont say bad about him, Allah ya gafarta mishi ya rahama mai, and if you have the slightest respect for me, ba zaka saki Saude ba, zaka cigaba da Aurenta ko don Aneesa, diyar k'aninka" "Shatu kar ki man haka" Mami ta rungime Mijinta tana shafa kanshi kamar k'aramin yaro tace "Please Habibi, do it for me, Please".
*******
A daren Ranar, Saude, Aneesa, da Daddy ba su samu sun runtsa ba, Washegari Aneesa ta ki bude k'ofa, Mami tayi kwankwasawr duniar nan, amma taki ta bude.
K'arfe 11:30 Uncle Zaid ya shigo gidan, Tun daren Jiya Daddy ya kirashi ya sanar dashi, abun ya firgita Zaid Sosai, amma beyi wani mamaki ba, ya Umurta duka 'yan gidan Su hallarci Parlorn Daddy, har su Nene karere, bayan Meema ta gunguro Saude kan Kujerar guragu, Duk ta fita hayyacinta, kafar nan ta faara rubewa, ga wani wari, Zaid yace "Ina Aneesa?" Mami tace ta kulle k'ofa tun jiya" Zaid ya mik'e ya wuce Dakin Aneesa ya shiga kwankwasawa, "Anee open the door, Uncle Zaid ne please" "Go away i dont want to see anybody" Anee Please kizo ki bude mim k'ofa, nine Uncle Zaid, K'anin Babanki" a hankali ta bude kofar tare da Rungume Zaid, be hanata ba, kuka take tayi sai da tayi me isar ta kafim ya jata har toilet ya wanke fuskarta kafin ya rik'o hannunta har Parlor inda suke Jugum jugum kamar Gidan Rasuwa.
*******
"Uncle Zaid bana son ganin wannan Matar a rayuwa ta, Na tsaneta, na tsaneta, tayi Zina ta haifeni, ni bazan zauna rumfa daya da ita ba" Aneesa ta fashe da kuka me tsuma rai, duk sai ta basu tausayi, Saude ta gungura kekenta gaban Aneesa, tace "ki yafe min, ki sani whatever i did, was because of you, i did it for you to have a better life, i did it because i Love you" cikin tsawa tace mata "k'arya kikeyi, Makaryaciya, you never loved me, coz if you do, you wouldnt have given birth to me, you were a slut, and thanks to you, i'm a bastard" ta juya zata bar Parlorn da gudu Saude tayi saurin mik'ewa zata bita, ta turgude ta fadi, wani ihun wahala ta sake Mami, Meema da Seebi sukayi Kanta, Daddy Dauke kanshi yayi, Rafeeq dama latselatsen wayan shi yakeyi, Zaid yace "Feeq je ka fiddo mota, mu kaita Asibiti" Feeq yayi kamar be ji ba" Zaid ya sake cewa "Rafeeq Lema, i said je ka dauko mota zaa kaita Asibiti" Rafeeq ya mike tare da zare earpiece din kunnen shi, ya kalli Zaid yace "No Uncle Zaid, ni ba zan dauko Mota akai any bitch Asibiti ba, besides I never liked her" ya wuce ya bar Parlorn, Zaid yayi saurin Kallon Alhaji Habib, Shi ko ya daga kafada alamun be damu ba, shima ya mik'e ya shige daki, Zaid ya kalli Mami yace "barim dauko mota, kuyi k'okarin sauko da ita".
Bayan Sati 2
Cikin kwanakin nan Sha hudu, kallo daya zakuyi wa Saude ku san cewa tana cikin Azaba da Musiba, don k'afarta ya gama Rubewa, har aiki akayi amma kamar an jangwalo wani abun, don kafar tayi damadama, ko so daya Daddy be zo ya dubata ba, kullum sai sunyi Fada da Mami kan sai yazo dubata amma yak'i, Aneesa ma idan ka mata maganar dubota sai ta hau Zage zage, Mami ce d a Seebi ke kula da ita harta Meema tayi watsi da lamuran Yayar tata, sai ta ga dama take zuwa Asibitin, Mami kuwa ko so daya bata taba gazawa da kula da Saude ba, Zaid ne ke Biyan duk wasu kudin da aka kashe a asibitin.
Dr ya kira Mami Office dinshi yace "I am so sorry to tell you, k'afar Sauda Ya rube, bai da wani amfani, idan aka barshi a hakan zai yi causing trouble to the other leg ne, So ina ba da Shawarar a yanke kafar, ayi mata Aiki me kankat" Mami ta dafe k'irji tace "A yanke k'afar fa kace" Dr yace "Its the best solution, ana iya samata k'afar roba, amma kuje kuyi Shawara".
**********
Waya ta kira Zaid ta shaida mai yace" Ba matsala amma ta tuntubi Sauden, shi yana wani aiki ne idan ya samu sarari zai lek'o Katsinar" ko da ta tuntubi Sauden da maganar Sosai ta firgita, taci kukanta harta godewa Allah, wai yau ita Saude me ji da kanta, me takama da duk abunda take so sai ta sameshi ko ta halin k'ak'a wai ita ake cema zaa yanke ma k'afa, lallai Duniya Budurwar wawa, to ya zatayi idan bata amimce ba zai shafi dayan kafar, ga wahalar da take ci, gwara kawai a yanke, tana hawaye tace "Yaya a yanke kawai zan ma fi samun kwanciyar hankali, nagaji da wahalar da kafan nan ke bani".
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
A GURGUJE
Bayan An yanke k'afar Saude ta dan yi kwanaki a Asibitin ta dawo Gida, an bata Crutches na tafiya, har yanzu Aneesa ba ta sauko ba, Daddy ma ba ruwanshi da ita, sai da Mami tayi dagaske kafin ya lekata so daya, shi bek'i ya saketa ba, don ya mugun tsanarta, Mami ta shaida mai Ai don Diyarta zaiyi.