Sashe 44
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Seebi na zaune bisa kujera yar tsugune, tana yi wa Nene tsifa, i Nene da Hajjo na kan tabarmar k'asa, Sallama suka ji, da sauri Seebi ta zaro Mayafin ta kan Igiyar Shanya, Nene ta daura dankwali tare da Amsa Sallama, Maaleah yace "donAllah nan ne Gidan Nene?" da sauri tace Eh Yaro Shigo, nice nan Aminene, yace toh ina zuwa, Yara ya samu ya sa su kwasan kayan ya ce suka shiga gidan nan, Mamaki ya rufe su Nene, ana haka ne Maalesh ya bi bayan su ya shigo, yana ganin Hajjo ya bude baki "Laaaah Hajjo, kece nan?" tace "Maalesh yaushe a gari?" yace "jiya na shigo, na tambayi Mom kina ina tace ba kya nan" tace aiko dai gani anan, ya durkusa ya gaida Nene, ta amsa mai cikin Fara'a, yace "kece Nene daga gani" ta nuna kanta da Yatsa tace "Nice nan Aminene Yar Mamman, duk duniya ba wata Nene sai ni" ta nuna Nasiba da hannu tace "Nenen Seebi kake ji" ya juya ga wacce aka cema Seebi, ya ga shi take kallo, tsaf tagano shi, shine wanda kwanaki da zai basu Lift yace sai ta cire Nikab, kuma Shine Abokin R-Lema, ta dai maske ta gaishe shi, "Lord have Mercy" inji Maalesh, tuni Nasiba tayi gaba da Imanin shi, da kyar ya amsa mata fuskar shi cike da Annashuwa.
"Hajjo tace Maalesh wannan kayan fa?" yace "Uncle Zaid yace a kawo" Nene ta chafe "Allah Sarki Zaidu Bawan Allah, Allah shi biyaka ya saka da Alheri, Malush kaima Nagode maka" Yayi daria yace Nene "Maalesh nake ba Maalush ba" duk sukayi daria, na da nan Maalesh suka dinke da Nene, k'wank'waman su iri daya na surutu, sai yi suke tayi yanda kasan sun dade da sanin juna, dama shi Maalesh saurin Sabo ne dashi, nan Hajjo ta zubo mai Burabusko ya kwasa kamar ba gobe, sai kallon Nasiba yake tayi, ita kuwa sai smilling take tayi tana jin diramar su da Nene, har kusan Laasar be da niyyar tafiya. Wayar sa tayi k'ara, ya ciro daga Aljihu ya duba, ya kalli Hajjo yace dan gidan ki ne, tayi murmushi tace "Rafeeq Ho" ya dauka "my guy howfa?" kusan sakwan 3 beyi magana ba chan yace "kana ina? Nazo gida baka nan" Maalesh yace "Wallahi gani ta wurin gida Uncle Zaid ya aikoni" tsaki Rafeeq yayi yace "ina jiranka" ya kashe wayar, Nasiba ta tsura wa wayar Maalesh ido, kamar tana jiran Rafeeq ya fito daga ciki, Nene tace "Wannan uban Yan k'asaitan ne ko?" Maalesh yayi daria yace "Nene kinsan Rafeeq ne?" ta ta6e baki tace "ai wannan sai kun hada mai da tofi" yayi daria yace barin je, sai na dawo ya musu Sallama ya kalli Nasiba yace "Bye Beautiful" ita kunya ma ya bata ta rufe fuskar ta da tafin hannayen ta.
Yana shiga Dakin shi ya ga Rafeeq kwance kan Gado, ya bubbuga mai k'afa, kamar ba zai tashi ba, ya mike sukayi side hug, Maalesh cike da doki yace "I met her, Wallahi naganta yau" da k'yar Rafeeq yace "Who?" Maalesh yace "The love of my life, Seebi, Uncle Zaid ya aike ni Gidan su yanzu in kai ma Nene sak'o" a dan tsorace Rafeeq ya kalleshi, kamar zaice wani abu sai ya fasa, be damu da Rashin Ansashi da Rafeeq yayi ba, Maalesh ya cigaba "Shes beautiful, ai kasanta, ta hadu ko? Zamu dace? Haka ya ishe Rafeeq da maganar Nasiba, yace " Guy do you think she'll like me? Wallahi ina sonta, kawai ganinta nayi gefe na kamar an jefo ta, ina ganin ta naji She's the one, wannan shi ake kira "LOVE AT FIRST SIGHT" cikin kufula da daga murya Rafeeq yace "Will you Shut the f**k up?
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg4⃣1⃣
Maalesh ya kalleshi da mamaki yace "Guy, Calm down" Rafeeq yayi guntun tsaki cikin yanayin shi yace "ban ga dalilin da zai sa ka dinga min maganar wata yarinya ba, duk ka bi ka ishe ni" Maalesh cikin doki yace "Feeq ba zaka gane ba, Wallahi ina sonta, sosai fa" kamar ba zai ce komai ba yace "She's Innocent, dont hurt her" da sauri Maalesh yace "Wallahi i wont, shes not like the rest of the girls i'm with, Wannan ta dabance, guy bani shawara ya zanyi?" chan cikin mak'ogaro yace "Tell her" "bansan mesa ba i lost the courage, ai da tun dazun na gaya mata" Rafeeq yayi shiru ya cigaba da latsa wayar shi be ce komai ba, Maalesh ya yi rigingine kan Gado, Rafeeq ya dora wayar shi kan cikin Maalesh, Maalesh ya tashi da sauri ya dauki wayar Rafeeq ya duba, kan Screen din ya ga Message ya karanta, ya kalli Rafeeq don neman k'arin bayani, guntun tsaki Rafeeq yayi yace "The girl's Number" wani irin super Maalesh yayi ya duro, ya rungume Rafeeq, donAllah numbern ta ne? Kai Nagode Breh, naji dadi Wallahi" Shi dai be ce dashi komai ba, Maalesh yayi copying number din yayi saving a wayanshi.
Tana tsakiyar su Nene suna fira, wayar ta yayi ringing, ko da ta duba New number ne, ta dauka da Sallama, Muryarta yafi komai dadi inji Maalesh, ya amsa yace "Hello, Beautiful" wani ajiyar zuciya ta sake ta amsa da Ina wuni don ta san me muryar, yace "kingane me magana ne? Cikin jin kunya tace "eh" to waye? ta yi Murmushi tace "Ya Maalesh ne" Waiyo dadi, Ya Maalesh, karo na farko bayan Rasuwar Rafee'ah yaji an kirashi ta wannan sigar, yace "Seebin Nene, you are a Blessing, kinji Voice dinki kuwa?" kunya ya bata sai bata amsa shi ba, yace "are u there? Kinyi shiru?" a hankali tace "i'm here" "Seebi will you be my friend?" Daria kawai tayi, ya kike daria? "Ba kya so in zama Abokin ki? A hankali tace "Aa" yace "Aa mene? Kina so? Will you be my friend? A hankali tace "yes" Darian jin dadi yayi yace "let me warn you, my friends usually say i'm a Sweet Soul, abun nufi shine Wata rana Abokantakar mu na iya rikidewa ya koma Soyayya" Daria kawai tayi, nan suka sha fira don Maalesh akwai Zance, sun dade suna waya inda ya shaida mata zaizo Gobe don Jibi zai wuce Kano inda yake Service.
*Washe Gari*
K'wank'wasa k'ofar yayi, sai da ya kusa minti 3 kafin yazo ya bude mai, hararar shi Maalesh yayi ya ra6a ta gefen shi, ya shige cikin Dakin, Da k'yar Rafeeq yace "Sorry i missed your call" Maalesh yace "and you cant call back?" Guntun tsaki Rafeeq yayi yace "I said i'm sorry didnt i?" Maalesh ya k'ulu ya mik'e zai fita da sauri Rafeeq ya rik'o shi, kasa magana yayi ya girgiza kanshi, Maalesh ya dawo ya zauna, Rafeeq yace "Look, wannan Aneesar banzan ce take takura min, shisa na kulle k'ofana, coz duk abunda zan mata bazata yi zuciya ba, so da ka kirani i thought itace shisa ban dauka ba" Maalesh ya girgiza kai cikin takaici, ya akayi sunana da na ta yayi kama, har da ka zata itace?" a takaice yace "ban duba wayar ba" "Oh lord have Mercy" Inji Maalesh da sauri Rafeeq yace "Kayi kyau Sosai, ina zakaje ne haka?" Don dai ya 6atar da zancen don yasan Maalesh da mita kamar Nenen Seebi. Murmushi Maalesh ya sake yace zanje Gidan Nene ne, zanje musu bankwana, Tsaki Rafeeq ya sake "Do you really have to go there?" Maalesh ya amsa da sauri "Yes My other Half is there" wani Mugun tsaki Rafeeq ya sake tare da kwanciya kan Gado, Maalesh ya mik'e yace "Feeq, barin je sai na dawo" da sauri Rafeeq yace "Wait" da Mamaki Maalesh ya kalleshi, Rafeeq ya dauke ido be so su hada Ido da Maalesh yace "I'm Bored, i'm coming with you" be jira cewar Maalesh ba ya fice daga dakin, Maalesh da mamaki ya maimaita "He's Bored?" Sabon Salo, gemu a kafada, yau Rafeeq yake cewa he's bored, shida be k'i ya kulle kanshi a daki ba, be komai, lallai kam, toh K'ila ya fara Chanza halinshi, Allah ya sa don sai nafi kowa Farinciki, ya fita tare da kulle dakin da Mukulli ya bi bayan Rafeeq.