← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 95

Sashe 67

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asslam Alaikum, Ina mik'a Godia ta ta musamman ga dukkanin masoya KE ALHERI CE, Ina Godia Matuk'a Ga Adduar Samun waraka da kuka tayi ga Mahaifiya ta, Allah ya bar Zumunci ina kuma me farin cikin sanar daku cewa Tana ta samun Sauki, Allah ya saka maku da ALHERI masu kirana ta waya da masu turo Sak'onin su Via Sms da ta Whatsapp da ma wanda basu samu daman hakan ba, Allah ya bar Zumunci. #grateful #1love.

A big Thank You to Aunty Sis❤ Thank you for comforting me through my rough days.

This Page is For You Sister Fatima Wada (Maman Meema)💘💘💘

Pg5⃣2⃣

Tashin Hankali Saude ta shiga don ganin Dakin Marigayiya Rafee'ah Daddy ya basu Nasiba, ta hade hannayaenta saman K'irjinta tana neman Mafita. _Boka na kan tudu_ ya fado mata a rai, ta tuna haduwar su ta k'arshe basu wanye lafiya ba har tayi ikiirarin ba zata sake neman shi ba, yanzu dole ta neme shi tun kafin dare yayi mata don tasan shi zai share kukanta.
Haka ta daddafa ta kai Washegari da su Nene a cikin rumfa guda tayi ma garin Kano Asubanci tafiar da ko Aneesa bata san tayi ba.
Daddy ya kalli Nene yace "Ya k'arfin jiki ya kuma Bak'unta?, tace "Alhamdulilah, ni dama ba abunda kr min ciwo" Nasiba ta gaida Daddy ya amsa mata, Daddy yace toh Nene ni zan fita gurin Aiki, akwai kalaci a Parlorn k'asa ku sauka ku ci abunda ranku keso" Nene tace to shikenan Zamu sauka, Allah ya biyaka da Alherinsa, ya amsa da Amin, har ya dan juya zai bar dakin yace "Nene ince ba wani abunda kuke buk'ata ko?" shiru tayi Tana nazari, chan tace "akwai, ina da bukatar kudi" a razane Nasiba ta kalleta, kallon Haba Nene, bayan sun tanadar musu da komai na bukata, mesa xata tambayeshi wani abu kudi ma for that matter, ba tare da bin ba'asi ba Daddy yayi saurin sa Hannu Aljihu ya bata 15k yace ga dubu sha biyar sun isheki? Tace "sunyi yawa ta amsa ta zari dubu takwas ta mik'a mai sauran kudin yace ta barshi a hannunta bazai amsa ba, tace " Kai Amsa, dubu takwas ya isheni" hannu ya sa ya amsa, ya tashi zai fita tace " ko ta wurin Filin Samji zaka ka dan ajiye ni wani gu?" Nasiba ta dafe kai cike da takaicin Nenenta, yace "Muje sai a ajiyeki, da sauri ta suri Hijab dinta ta bi bayan Alhaji ba tare da ta kula Nasiba ba. Nasiba ta juya kai cike da jin haushi.
*****
Sunyi dan tafia kadan gaba da Filin Samji Daidai Asshifa Medical Center tace "yauwa aje ni nan, yace da direba yayi parking, yace "Nene Asibiti zakije daba akai ki na Dr Dara ba?" tace "kaini nafi gane na Hausa, barin shiga, daga nan sai in taka inje 'Yarkutungu in siyo Zogale" "A siyo Zogalen dani" ya fada yana daria tace "toh sai kadawo Allah bada Saa" ya amsa ta juya ta shiga cikin Asbitin Musulunci da suka shahara gun magance abun da ya danganci 'Jinnu, Sihiri, Ciwon K'ashi da makamancin haka'.
*******
Zaune take gaban Malamin, tace "dama nace maka zan dawo, yanzu shine ya ajiyeni anan ma" Mallam yace "to da baki shigo dashi mun mai yan tambayoyi game da matar tashi ba don mu samu saukin Magance lamarin" Nene ta nisa tace "ai Mallam baka gane ba, Zargin matarshi nakeyi, kuma ban sanar da kowa ba, shiyasa na ke so a ban maganin da Asirin ta zai tonu, don Wallahi ban yarda da wannan Sauden ba" Mallam yace " toh shikenan, kamar yanda na gaya miki kudin Kwanaki dubu 7 da dari takwas ne" tace "toh mallam, ta bude 'yar pos dinta ta ciro dubu takwas ta mika mai, Mallam ya bata chanjin dari 2, ya dauko wani dan galan, da abun cikin be wuce rabin galan din ba, yace " Wannan hadin magunguna ne kalakala, a dinga mai amfani dashi wurin girki, InshaAllah gaskia zata baiyana, zai tunano komai in ma an batar mai da saninshi ne, Nene tayi godia ta mai Sallama ta fito ta wuce Kasuwar 'yar kutungu a siyo Zogale har da sansamin Zogalen tace "zata shuka a gidan A.Habibu tunda ta lura yana son Zogale, kawai in yayi tsawo sai a dinga katsa ana dafa mai yana sha har ruwan Zogalen tunda maganine.

Kusan a tare suka iso gidan, Nene daga ina hakan, har kinji sauk'i kin fara fita? Zaidu bawan Allah, kasuwa naje, ya kalli Galan din hannunta, zaiyi magana yayi shiru a ranshi yace "k'ila jik'on su ne na tsofi" suka k'arasa ciki, yace "ai ni yanzu Kaduna zan wuce, gwara in koma hakan, Mami tana ta mitar a maido mata diyarta, Nene tayi daria, tace " ai ta ma yi k'ok'ari, ai da nasani na dan yi mata 'yan siyayya a 'yar kutungu" yace "ah haba bakomai" Nasiba ta lek'o tace "Uncle Zaid ina kwana? Yace "Ahh, na zata kin tafi School ai" tayi murmushi tace "sai 12 nake da lectures" ya kalli agogo yace ai is almost 11, in kin shirya sai inyi dropping dinki daga chan sai mu wuce" ta dan kalleshi, ina zaku wuce? Nene tace "Kaduna zasu koma yau ta fada tana murmushi" ba tare da ta kalli Nene ba tace "Allah sarki har an gama hutu, ina Ayman din?yace tana chan gidan Baba Tj daga nan sai mu biya mu dauketa sai mu wuce" Meema ta shigo Dakin jin muryar Zaid "Uncle Zee, kazo gidan baka neme ni ba? Ya dan rausayar da kai yace " Yanzu na shigo ya kike? Tace " living with some lunatics, i cant be fine" Nene ta tsargu ta hade girar sama da ta k'asa, tace "Ina fata ba dani akeyi ba" da sauri Zaid yace "Aa nenen mu, ya kawar da maganar da cewa Nasiba je ki shirya" Nasiba ta shiga ciki Nene ta rufa mata baya, ya maida duban shi ga Meema, ina Aneesa? Aneesa ta tafi School, Aunty fa? Tace ta dan je ta dawo. Ta zauna kusa dashi, ta sausauta murya tace "Uncle Zee ba zan fasa rok'onka ba, DonAllah give me a chance in nuna maka kalar son da nake maka, ina sonka, tun ina 6oyewa har na kasa, ina sonka sosai, ka aureni, ni zan zame na Ayman Uwan da ta rasa, zan dauketa kamar ni na haifeta, please ka taimakeni" ta karasa maganar kamar zatayi kuka, Sosai Zaid ya tausaya mata, ba zai bata hope ba tunda be son ta ko ծis, kuma be som ya mata k'arya, gwara ya fito mata k'arara ta san matsayinta, ya dan kwantar da murya yace "Meema, kiyi hak'uri, i only love you like a sister, no strings attached, and i'll take care of you kamar yanda zan kula da loved ones dina, please ki bar maganar aurena kinji? Allah zai baki me sonki wanda ya fini komai kinji? Kuka ta fashe dashi, Zaid beson kuka ko kadan ya hau lallashinta yace "kiyi shiru, i am sorry, i dont want to lie to you" da sauri ta mik'e ta fita daga Parlorn.
*******
"Wai wannan fushin da kike tayi na uban meye? Wani abun aka miki kike ta faman nuk'ura? Nasiba ta kalli Nenenta tace " Haba Nene, saboda me zaki amsa kudi gun Daddyn su Rafeeq? Bayan wurin kwana da suka bamu, sun biya mana duk wata bukkatun mu, don me zaki ce ya baki kudi? Nene ta tsura ma Nasiba ido, tace "kin gama? Wai ni Seebi me kika daukeni ne? Makwadaiciya ko wacce bata da godiar Allah eyi? Kin tsaya kinga dalilin da ya sa na amshi kudi gunshi, to in ma kallon kwadaiyaya kike man to ki chanza tunani" kinga wanchan galan din, ta nuna gallon din da hannunta, Magani ne ciki, maganin karya duk wani sihiri da ke jikin biladama da yardan Ubangiji, ina da tabbacin akwai shiri jikin Uban Rafeeq, kwanaki na je wurin me Asshifa na fada mishi zargi na yace akwai Maganin da zai hada mai na dubu takwas, duk sihirin jikin mutum zai kare, to ni ina naga Dubu8, ai ko hakora na na saida ai bazasuyi dubu3 ba, yanzu gaya min laifi ne don ya bani kudi na siyo mai magani? Naga ai shi zai amfana " Nasiba ta sauke Numfashi, tace "kiyi hakuri Nene, nayi zaton wani abun ne, kuma ai da kin bari don yana zuwa amsan Magani gun Mai Arriyadh" tace "ke ni rabani, ai ba laifi bane in an raba k'afa, Magani ai dace ne, Allah sa a dace Amin" "barin shirya kafin Uncle Zaid yace in fito".

*Wudil*

"Yau na shiga uku na, na kan tudu ya mutu?" a rude Saude ke maganan, matar ta dafa kafadunta tace "Hajia, ai in gaya miki, kusan wata 7 kenan da mutuwar na kan tudu, Bukkar shi ta kama da wuta, ko tokan shi be tsira ba, da na kanzo gunshi, amma tunda na ga Na kan tudu yayi mutuwar wulakanci na koma ga Allah, Kema ina baki shawara ki koma ga Allah, abunda Allah zai miki Boka be isa ya miki ba Wallahi, Saude tace ke dalla rufa min baki ba waazi nace ki min ba, ni ba ragguwar mace bace, ni jaruma ce, i dont give up" matar ta ta6e baki, bata fahimci turancin ba tayi gaba ta bar Saude tana jimamin mutuwar Na kan tudu, yanzu take tambayar kanta, meye abunyi?.

*UMYU Katsina*
Chapter 67 · 0% Book details