Sashe 56
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Bayan yan mintuna Ayman tayi motsi, Zaid yana kan darduma yana Sallah, Rafeeq ya k'i matsawa ko ina, yana ganin tayi motsi yayi saurin daukarta yana "Angel, kin tashi?" a hankali ta ware ido, ganin fuskar da bata sani ba ya sa ta 6are bakin ta tana kuka, Rafeeq ya rungume ta yana "shhh Angel, shh Hamma is here for you" ina sam yarinya bata sausauta ba sai kara 6are bakin da tayi, gashi bata ji dadin rik'on da Rafeeq ya mata ba, don ko rik'e yara be iya ba, cikin marairaicewa kamar zaiyi kukan shima yace "Ayman kiyi shiru please, you are making Hamma worried" cikin kukan yaji tana cewa *Mamiii* wani gululun bakin ciki yaji ya taso mai, wai me Mami takeyi ne da kowa ke sonta, basu san cewa ita Musa a baki Firauna a zucci bace? Har wannan yarinya ta san tayi kuka ta nemi Mami, dogon tsaki ya buga, Ayman kuma bata fasa kiran Mami ba, cikin muryan kukan Yara take cewa "Mammmiiiii" cikin tsawa Rafeeq yace "Shut the hell up".
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
_Nagode da Adduoin ku, masu kirana da masu min message a Whatsapp da Sms Ina godia, ina muku Albishir da naji Sauk'i sosai, kuma zaa cigaba da yanda akeyi InshaAllah. Allah ya bar Zumunci.
Pg4⃣8⃣
Duk suka bi bayan Nene, Rafeeq na gannin baban shi a ranshi yace "Interesting! Daddy a gidan Nene" shi kuwa Zaid cewa "yayi Yaya me kakeyi anan?" nan Nene ta gano bakin Zaren tace "touu Alhaji Habib Lema ne, gaya min, da saninka ne Matarka da 'yayanta suka ma jika ta mugun bugu?" Alhaji Habibi duk ya daburce, be taba ganin tsohuwa me masifa haka ba, yace "kiyi hakuri Wallahi ba da sani na bane, ni ne na kar6eta" Nene tace yo abun azziki kayi? Dalilin wa aka bugeta? Nace dalilin wa? A hankali yace "kiyi hakuri a dalilina ne, hakan bazai sake faruwa ba" tace "k'warai kuwa, hakan ba zai taba sake faruwa don yau watna cin ubansu ya tashi, har matarka" tayi hanyar fita da sauri Seebi ta rik'ota, duk suka shiga bata hak'uri tana cicijewa banda Rafeeq da ya koma gefe yana Murmushi, ya tabbatar Nene yar daru ce, da k'yar suka shawo kanta don tana ganin kimar Zaidu dan Albarka, ta dawo ta zauna kan kujera, Nasiba tace ma Daddy kayi hak'uri, shez always like this" murmushi ya mata yace "karki damu" ya zauna kusa da Zaid dake kan tabarma, cikin gunguni Rafeeq yace "ai da kun kyaleta taya zata je gidan mutane ta buge su?" ashe ta ji shi cikin fada tace "Ai da kun bari naje sai ka ga ta yaya naje har na musu dukkan tsiya, sai ka tantance, kaima bawai k'yaleka nayi ba" Uncle Zaid yace "Feeq quiet!".
Zaid yace "Yaya wai ne ya faru? Wani Sak'o Nasiba ta kai maka? Ajiyar Zuciya Alhaji Habib yayi, ya fayyace musu komai tun haduwar su a Gun mallam, har zuwa yanzu da ta kawo mai magani, Zaid ya jinjina kai yace "Ashe ba nikadai nake ganin Nasiba kamar marigayiya Rafee'ah ba" Nene tace "kama sukeyi ne wai?" Alhaji Habib ya bata amsa "basa kama anma yanayinsu iri daya komai" Rafeeq dai be je komai ba, sai kallont yakeyi, ita kuma hankalinta baya nan yana gun Aymana da ke rik'e a hannunta, hayaniyar Nene ya hanata bacci, Zaid yace "Yaya to maganin dai ka sha su yanda ya kamata, don ka daina jin Yanda kakeji Allah ya sa a dace" yace "Amin" Zaid yace "Feeq ka je gida ka kwaso kayan Ayman, dare na k'ara yi" a zucciye yace "Seriously shes sleeping here? Cikin daga murya Zaid " Yes Rafeeq, shes sleeping here" kamar zaiyi magana ya fasa ya wuce fuuu kamar zai tashi sama, Nasiba ta bishi ido a ranta tace"why? Yana da matsala ne don zata kwana nan?" ta ta6e baki.
"Engr. nace baza ka kai Rafeeq gun Malamin nan me magani ba, yana maganin Sihiri ko asiri, ko aljannu, da masu taurin kai, abunda ya sa na yarda Mallamin, ba dan tsubbu bane, kuma be aiki da Aljannu, da kalmar Allah da Adduoi da suek a cikin Kurani da Hadisi ya ake amfani, ba a san inda zaa dace ba, wannan zucciya ta Rafeeq na bani tsoro" Zaid yace "Duk da akwai Chanji a halaiyar Rafeeq zan kai shi a duba shi, Nasiba kin san wurin ai? Idan kim dawo school gobe sai ki rakamu, Nasiba tayi gyaran murya tace "da akwai abunda baku sani ba Uncle, Rafeeq Yana na magani already, ko yau da Daddy ya ganni a gun Mallam Ruwan maganin shi na koma an so mai don wanda aka bashi da farko ya k'are, Ruwan Adduoi ne, ya maida shi ruwan sha, in kuma a gidannan zai ci Abinci, to da ruwan maganin ake mishi dahuwar, sai kuma Wani maganin hadin magunguna, shigen naka ne Daddy, shi maganin zai sa mai hakuri da dangana a zuciyar shi, to Alhamdulilah an fara samun Nasara".
"Allahu Akbar" inji Daddy, "Engr. Ka lura da wani abu game da Rafeeq bayan dawowan ka?" Zaid yayi murmushi idonshi kan Seebi, duk ta gama tafiya da imanin shi tsaf, maganarta yanayinta, komanta y bureshi, yace "eh Yaya, Rafeeq is somehow changed, naga chanji wallahi, ashe akwai silar chanjin shi" Nene tayi magana, tace "ai da Mahammadu yazo ne ya mishi wuriwuri har ya amso mai magani ya kuma tilasta mai sai ya sha, yanzu ms zai dawo in bashi na yau" Daddy yace "abunda bangane ba, shine Zaid dama kun san su Nasiba? Ya abun yake?" Nene ce taba Daddy labarin daga farkon haduwan su Zaid har zuwa yau, Daddy ya jinjina kai dama akwai irin mutanen nan? Masu maida damuwar wasu nasu? Kuma tsakanin su da Allah? Ba don wani abu ba? Kai su Nene ba abun yadawa bane, mutanen Arziki ne, ashe sune Silar saukowan da Rafeeq keyi yanzu, Allah ya musu Albarka, Lallai su Nene *ALHERI NE* a rayuwar su.
Daddy yace "Inna Mungode k'warai da wannan karamci naku, ba abunda zan iya biyanku dashi, amma ina so in dauki Nauyin karatun Nasiba, wallahi a sanda na fara ganinta na fara Sonta, irin So din da na ke ma diyata Rafee'ah, donAllah ku bani wannan damar" Nene tayi darian murna tace "Ai jahili ke maida kyauta, an baka dama,Allah ya bar zumunci" duk suka amsa da "Amin" ya cigaba da cewa, "My daughter, ke kuma daga yau if you ever need anything, come straight ahead and tell me, dont hesitate to tell me, zan baki number na, you can easily reach me" tayi godia Sosai. Nan Rafeew ya shigo da Sallama, suka amsa mai, Akwatin Ayman ne sai kayan wankan ta, sai kwandon Abincin ta, Seebi ta taimakeshi ta shiga da kayan cikin dakin Nene, tana jerawa bayan ta kwantar da Ayman kan Gado ta sakar mata Net don kar soro su cijeta. Nene ta kalli Rafeeq ta tuburne fuska tace "ai sai kaje ka dauko maganin ko?" bakin shi ya turo ya mik'e yana gunguni, dakin ya shiga saman wardrobe inda ake ajiyewa ya dauko ya kalli Nasiba da take ta ririita Ayman tana bacci ya ta6e baki ya fita da robar maganin, kitchen ya shiga ya zaro chokali, Daddy da Uncle Zee suka bishi da ido, yanda yakeyi kamar yaron da ke tsoron magani, duk sai ya basu daria suka gumtse. Kawar da kai yayi ya mik'a mata, ita ma ta kawar da kanta ta amsa, su a dole basa shiri, ta bude ta tsiyaya mai, kamar kullum ta toshe hancin shi ta dura mai, tare da gumtse bakinshi har sai da ya hadiye, guntn tsaki yayi yace "kina da matsala" ai ko igiyar chajin radion kusa da ita ta wawuro ta shauda mai a baya "Ouuuuchhhh!" ya fada yana sosa baya, da Daddy da Uncle Zaid suka tuntsire da daria, ya kallesu yace "Its not funny it hurts" Nene ta mik'e tace kana so in k'ara ma ne? Ba na hanaka turanci a gabana ba? Tsaki yayi ya kalle su duka yace "I'm outta here" ya juye ya fita, tana daria tace "ai da ka tsaya mana, kai karatun ka iya Najiriya, da ka tsaya nasa Zaidu bawan Allah shi da yaje Ingila ya turance min kai, ya kafirce min kai da turanci" ai kam Daddy dariya harda rik'on ciki, Zaid ya kalli Nasiba da ke daria k'asa k'asa, yace "are they always like this?" tace "Yesss, they are always like this like all the time" Nene tace "Au kuma turancin ne?" duk suka sa Daria, Daddy ya mik'e yana daria yace "Nene da jikokinta baza ku kasheni ba, nayi Gida" Sukayi Daria har Gate suka rakashi, suka mai Sallama, a waje suka ga Rafeeq zaune kan mota au ashe be tafi Ba inji Nene "kema dai ki barshi donAllah" Daddy yace "R-Lema, mu tafi kaji kar Nene ta sake dukkanmu kai" Rafeeq ya lura duk daria suke mai, to meye abun daria, guntun tsaki yayi ya murtuk'e fuska, ya sauko daga kan motar, ya mik'a ma Zaid mukullin motar shi ya bi bayan Daddynshi, Nene tace "Guznight gaye" kallonta yayi ya buga tsaki tace "Auu, Dunkum dangin Tsaka". Duk suak fashe da daria.