Sashe 70
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Toilet Saude ta fada ta je ta tsatso wankan ta, tare da sa wata rigar bacci, ta duba agogo taga k'arfe 9 saura lokacin shan Tea din Alhaji ne, dabara ta fado mata, tunda ruwan tea din sai an sa kayan k'amshi kamar su citta, kannanfari, na'a na'a da green grass sai lipton, to me zai hana ta dafa mai ruwan nan ta watsa kayan k'amshin ciki ta kaima ya sha tunda ba ganewa zaiyi ba? Haka ta dauki gallon dinta ta nufa kitchen ta tafasa wannan ruwan ta zuba kayan k'amshin ta juye a flask, ta dauki dan guntun mug tayi dakin Alhaji Habib. Ta shiga da Sallama, zaune yake yana kallon News Line a NTA, ya dago ya kalleta, haka kurum yaji be don ganinta, da k'yar dai ya amsa Sallamar ta, ta janyo dan guntun table ta ajiye flask din da cups, tace "Alhaji Na ina wuni?" ba yabo ba fallasa ya amsa mata,yace "ina kikaje Saude? Duk yau ban ganki ba? Ta fara indainda, wai tana cikin gari, Mamar kawarta ta rasu, shine taje zaman makoki" ban isa ki gaya mim inda zaki bane? Ni fa ke aurenki Saude, bazan dauki fita irin haka ba, duk inda zakije daga yau sai kik nemi izini na, no matter how urgent it is, am i clear?" Mamaki ya baiyana fuskarta, abunda bata taba gani ba, a ranta tace komi zai zo k'arshe once ka sha ruwan nan" ta marairaice face dinta tace "Am sorry Alhaji na, kayi hakuri, ba zaa kara ba" ga night Tea dinka kasha barin tsiyaya maka" kafin yace wani abu Sallamar Nene ta doki kunnuwansu, Alhaji ya amsa mata, Saude ta murtuk'e fuska, Daddy yace Nene har kin dawo? Tana washe baki tace "Ai na gaya maka abun ba wuya, gashi har na hada ta ajiye flask dinta nan kusa da flask din Saude, Saude ta kalleta da mamaki tare da murtuk'e fuska tace "miye wannan?" Nene tace "Shayin buzaye ne" Saude ta dauke flask din Nene tace "Alhaji baya shan irin shayin nan, baya buk'ata" "Aa ni nace mata ina so, inaso in sha yau, tace min irinshi take sha, shiyasa bata ciwon jiki, shine nace nima ina so wataran in sha, ta shaida min tana da abun hadin, nace aa tabarshi don nasan sai an hura garwashi, bayanda ban yi da ita ba tace ita sai ta min, ashe har ta hado, kai amma Nenemu nagode sosai" Alhaji ne yayi maganar. Nene ta chafe da cewa "ai nagaya ma ba wahala, ina sauka k'asa naga wutan da yan baya sukayi abincin dare ba be mutu ba, na dan dibo na dinga rurawa, daman na siyo mangal (kaskon karfen) a kasuwa jiya don duk dare sai na sha" ran Saude in yayi dubu ya 6aci tace "Alhaji, you cannot take this thing, i made your Tea for you, you dont know what ingredients she used, they might be bad for your health, dont forget you are allergic to such things" yace "Saude it would be very bad if i dont take this, she used her strength and energy to make it for me, i dont want her to feel bad" Nene ta hade fuska, uban me suke cewa?, ita zaa yo wa turamci daga abun azziki? Harda Shi Alhajin k'aton banza, Ta mik'e fuu zata kwashe flask dinta, da sauri Alhaji yace "Aa Nene ki bar min donAllah zan sha" "aa kadai sha na matarka kar ta sake turance ni" yace "Aa Nene DonAllah ki bar min, naki zan sha" nan ta fara Fara'a ta ahiga tsiyaya mai Tea dinta da ya sha Magungunan Asshifa, Ran Saude a 6ace ta mik'e fuuuu ta bar Parlorn.
Sosai Alhaji Habib yaji dadin Shayin buzayen, ya kumayi santi, jin haka ya sa tace gobe zata mishi da sassafe don ya sha yayi godia sosai, suka danui fira kadan kafin ta mai bankwana ta tafi daki don yada k'afada.
Da takaicin Nene Saude ta kwana, Tsohuwar na ci mata tuwo a k'warya, amma bakomai, gobe rana ce, gobe Dole zai sha ruwan magamin nan don Da kanta zata shiga kitchen ta mishi Lunch kasancewar gobe Weekend.
*Mafarki* _2:45am_
"Ubangiji Allah kadai zai saka miki abun da kikayi ma Family dina, ke da kakarki Alheri ne a garesu, Abu daya ya rage kiyi, ina So ki shiga dakin Daddy, akwai wani gagarumin sihirin da akayi a cikin dakin, shine dalilin da ya sa Auren su Mami ya dade a rabe, ina da tabbacin in kika ga wannan Asirin komai zaizo k'arshe, Asirin na nan a----" Jijigar da Nene ke yi wa Nasiba ne ya katse mata mafarkin da takeyi,Nene ke famar fadin "ke Seebi tashi, ina kika ajiye min tochila na?" Nasiba ta buga tsaki da k'arfi, ji takeyi kamar ta rufe Nene da duka, saboda bata karasa jin Umurnin Rafee'ah ba, so tayi ta tambayeta ta hanyar da zata bi ta shiga dakin Daddy ba tare da sanin kowa ba, amma Nene ta shiga tsakani, pillow kawai ta daga ta ciro ma Nene torchlight ta ajiye mata ba tare da tace mata komi ba don takaici, ta juya tare da jan bargo tana me rok'on Allah Allah ya sa ta sake Mafarki da Rafee'ah.
1:00pm *A hanyar Kaduna*
Maalesh ya gangara k'asan Titi sakamakon taka k'usan da yayi, kiris ya rage ya k'arasa Zaria, gashi be da Spare tyre, ya rasa yanda zaiyi, ya koma cikin mota ya doka tagumi yana tunanin ya zaiyi.
Daga nesa ya hango motar Lesh, mamaki ya kamashi, to me ya keyi a nan? Kd zaije ko Abj? Dan guntun tsaki yayi yace "thats non of my bussiness" niyyarshi ya tafi ya barshi a gun don be son yi mishi magana, amma wata zuciyar ta hanashi yin hakan, don be san me ya tsaida shi ba, ya gangara yayi parking baya motar Maalesh, idan shi ya kai ga Tayan baya da yake a sace, guntun tsakin ya sakeyi yare da bude bayan booth dinshi ya ciro wani spare tyre, ya dauko kayan aiki duk cikin booth dinshi, ya gangaro dasu daidai tayar, daga cikin motan Maalesh ya ji ana kwance taya, yayi saurin lek'owa ganin Rafeeq ya sa shi dauke ido, don har yanzu yana fushi dashi, R-lema ya cigaba da cire wannan tayan, ya chanza dayan, ganin wannan ya mai tauri yana bukatar taimako ya sa Maalesh karasawa gunshi ya taimaka suka murde tayan ba tare da sun kalli juna ba, don kowa cike yake da danuwanshi, Rafeeq ya mik'e ya kakkabe hannunshi, cikin backseat din motar Maalesh ya hango bottle water ya bude ya dauka ya wanke hannun shi ya koma motar shi ba tare da yace komai ba ya ja motar shi yayi gaba, Maalesh ma be bi takanshi ba ya sa Tayan a Booth da kayan gyaran ya shiga mota ya bi bayan Rafeeq a guje.
A tare suka iso Kaduna, Maalesh ya kira Uncle Zaid yace "mai ya iso, gashi zai k'araso gidanshi" Uncle Zaid yace"Aa Mahmud bana gida, ina Gidan Maminku, kasan Malali ai? Yace "eh" "to in kazo ka kirani" yace "toh" ganin Rafeeq yayi hanyar Malali ya san cewa chan ya nufa ba tare da ya kira Uncle Zaid ba ya bi bayan Rafeeq har suka iso gidan Mami.
*******
A tare suka shiga gidan Mami tafito ta hadesu duka ta rungume, tana me murnar ganinsu duka, Ta ja hanayensu har parlo ta zauna, ta kallesu tace "Ayman na bacci kafin ku isheni da tambaya" murmushi sukayi a tare.
Zaid ya iso ya gaisa dasu ta hanyar musabaha, yace "ya akayi ka gane gidan Mahmud? Ya danyi shiru sai yace " na bishi a baya ne" Mami ta gabatar musu da abincin da ta dafa musu, nan Rafeeq yafara narkewa wai yayi tuk'i hannun shi na ciwo,sai dai ta bashi a baki, haka mami ta biye mai ta dinga bashi abincin a baki, Zaid da Maalesh sun saba ganin haka a gunsu kafin abubuwan su rinchabe, har suka gama.
Zaid ya kallesu duka yace "Ku saurareni, na son kuna mamakin dalilin da yasa nake nemanku ko? To lemme go straight to the point, ina lura da kalan kallon da kuke wurgar junanku dashi, ina sane da ba kwa magana, ina so ku sanar dani meye damuwar ku? Meye matsalar ku? Meye dalilin da ya sa abunda bakuyi shi a yarinta ba kuka fara shi da girmanku? Ina nufin meyasa kukayi dambe jiya? Ku bani amsa" Mahmud me ya hadaku? Maalesh ya kalli gefe yace bakomai Uncle Zee, ya juya ga Rafeeq ya tambayeshi, sha amsar kenan da ya bashi, ba yanda Zaid be yi ba don ya ji musababbin yin fadar su amma sunki bashi dama, sunki gaya mai komai. Mami tace "Ina ga tunda sunk'i magana ba sa son mu san meke tsakanin su ne, they chose to leave it to theirselves, nidai abu daya zance muku, you guys grew up together asif you're Siblings, dalilin ku Families din mu suka zama best of Friends more of relatives, and now kun dauko wasu halaiyar da ba naku ba? Bansan meya hadaku ba, bansan waye yafi gaskia a cikinku ba, but what ever it is, Fix it, kar in sake ji, kar in sake gani, idan na sake naji kun sake Dambe kai ko chachar baki ne zan sa6a muku sosai, kunsani ni ba bakuwar ku bace, i wknt take this, ina so ku shirya kanku right away". Ta tashi ta shige daki, Zaid ya zira key dinshi shima ya fita waje ya rage su biyu ne kachal a Parlorn.