← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 95

Sashe 72

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Tunanin ta ta Ina zata fara shiga dakin Daddy har ta soma bincikar dakin bata tare da an ganta ba? Dabara ta fado mata ta mik'e ra shiga parlorn Daddy da Sallama ta ganshi Zaune da Nene suna Karin kumallo, k'osai ne da koko, Seebi na mamakin Nene yanda tayi katokato tayi kanekane tayi kakagida da kula da Abincin Alhaji Habib kamar itace matar shi, ta girgiza kai ta gaidasu, ya amsa mata cikin sakin Fuska, tace "Daddy ina fatar kana jin dadin Weekends dinnan" yace "Sosai ma, Nenenki tana cika da Abinci, baki ga har na fara tumbi ba" Nene ta chafe ai ni nan da ka ganni, ba daga baya ba na iya kula da mutane" Seebi ta kawar da Zancen kafin Nene ta 6allo musu ruwa tace "Daddy grant me the priviledge to make your room for you,i've been doing nothing ever since our stay, please dont say no" Nene tace "Uban me kike cewa? Ta danyi yak'e tace cewa nayi ya bani dama in gyara mai daki tunda yau Lahadi ba abunda nakeyi" Nene ta yashe hak'ora tace kinyi tunani" yayi murmushi jin dadi yana ganin Nasiba kamar Rafee'ah, yace "Seebi, you are my Daughter, like Rafeeq, kina da damar shiga inda ranki yakeso da sanda kikeso a gidan nan, balle dakin Daddynki, ki shiga ki gyara mun kinji?" Nasiba tayi murmushi ta shiga tana godia ga rabbi.
"Oh Allah make it easy for me, Allah ka taimakeni ka nuna min abunda nake nema, ta shafa adduarta" nan ta fara da kewaye ta wanke toilet din tas, bayan ta duba duk lungu da sak'on Kewayen bata ga Komai ba, ta dawo daki, bata tsammani za a saka Wani abu a cikin Wardrobe, nan ta hau neme neme daga nan daga chan jawo nan, jawo chan, wayam, har ta fara gajia ta shiga gyaran Gado, haka kurum hancinta ya jiye mata wani wari, ta shiga shinshine shine, tayi Imani warin nan daga k'ark'ashin Gado yake, da k'yar ta samu ta daga katifar gadon me nauyin tsiya, gabanta ya fadi da ta hangi wani yar k'aramar tukunyar k'asa da aka daure da wasu zare, jikinta ya hau rawa, ya zatayi yanzu? Nan ta shiga karanto adduar da ta shigo bakinta tana k'arafafa ma kanta guiwa is now or never, Dole tayi jihadin dauko ko menene, nan ta samu wani kwarin guiwa tayi bismillah ta dauko tukunyar nan,da k'yar ta samu ta maida katifar tayi laying dinshi duk hankalinta baya jikinta, tayi saurin saka tukunyar a dustbin din dakin ta fita, har yanzu suna Zaune inda ta bar su, baki na rawa tace barin je in dauko zubar da bolan nan sai in kunno turaren kamshi, Daddy yahi murmushi yace "Bless you My Child" Kallo daya Nene ta mata ta san bata cikin hayaccinta batayi yunkurin binta ba, Hijab tayi sauri ta saka ta fita daga cikin gidan, jiki na rawagudu gudu sauri sauri ta bar gidan, ko lura da Baba maigadi batayi ba, ta samu Keke Napep. Da k'yar ta lalubo magana "Arriyadh Islamic Medicine zanje" yace "ki shigo" suka hau titi jikinta be bar rawa ba, cikin ikon Allah isarta tayi daidai da zuwan Mallam Usman, ya kalleta yace "Nasiba lafiya naganki da sassafen nan? Ince dai Rafeeq lafiyar shi lau?" bata iya bashi amsa ba sai dai ta mik'a mai dustbin din hannun ta, yana lek'awa ya shaidi Tukunyar nan ta tsafi ne, ya kalleta yace "ki kwantar da hankalinki Nasiba, you are safe, no harm may come to you here" Ajiyar Zuciya ta sake me k'arfi, mai gadi ya bude musu Asibitin suka k'arasa tare, wani daki ya shiga bayan ya umurce Seebi data tsaya waje, Mallam yayi 'yan adduoin shi tare da sakin wannan tukunyar kasa, nan take tukunyar ta fashe, wani ruwa me doyi tare da wasu kadangaru suka gani guda bakwai, kandangarun masu rai, k'okarin guduwa sukeyi Mallam ya shiga Karatun kurani mai girma, amma idan yayi nan sai wasu suyi chan a guje, be so su bar dakin, don in suka bar dakin akwai Matsala, Tun Mallam na fafatawa da kadangarun nan har ya fara gajia, ya dan bude murya yace "Mallam Salis dauko mun recorder din nan ka kunno ta ku ku're volume" jiki na rawa Mallam Salisu ya nufi office din, ganin kamar zai bata lokacine mallam ya vigaba da karanto Amanar Rasulu, Wani k'arfin guiwan da bata taba ji ba yazo mata lokaci daya, bata san lokacin da ta bude dakin da Mallam Usman ke ciki ba ta shiga tana karanta Ayatul kursiyy da karfi, tana kaiwa k'arshe ta bi Mallam da karatun Suratul Jinn suka hada baki wurin karatun nan, cikin ikon Allah K'adangarun nan suka fara wani irin ihu, chan suka fara fashewa sai kuma suka fara ci da wuta, Mallam da Seebi basu bar karatu ba, har sai da suka k'one kurmus ko toka ba'a gani.
Daidai lokacin da Alhaji Habib yaji kanshi ya mai nauyi ya mike tsaye tare da rik'e kai, Ya fara ganin Nenen bibbiyu, dakin na juya mai, abubuwan da ya mance su yake tunanowa chan kuma ya zube k'asa, kuma sai ya tashi a zabure Dda k'arfi yace "AISHATU".

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg5⃣5⃣
Chapter 72 · 0% Book details