Sashe 27
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Saude ce ta nufa gun Rafeew ta na kururuwa, tana fadin yau mun bonu "Shima ya mutu" Zaid dake tsaye tun dazun ya kasa motsi sai hawayen da ke bin kumatunshi, ya tuna inda Rafee'ah ke rok'on shi ya barta ta bishi Malumfashi, da ya hanata binshi da duk sai yaji ya tsani kanshi, ya share hawayen shi, ya taka har toilet din Rafee'ah ya dibo ruwa a cup, yazo ya yayyafa mai, Zumbur Rafeeq ya tashi, Saude mamaki ya lullubeta, ya akayi Rafeeq ya tashi? Daman be mutu ba?, Rafeeq ya fashe da kuka, tare da Rungume Zaid, "Uncle Zaid, Rafee'ah ta tafi ta barni, Rafee'ah ta mutu, she was in my room yesterday, telling me she loves me, Uncle Zaid why didnt i tell her i love her back? Ina sonta wlh Sosai, ta dawo, i so much hate myself right now" duka dakin suka fashe da wani irin kuka mai tsumma Rai. Hafiz ne yayi karfin halin cewa sai ayi Gaggawar kaita makwancin ta, barin je in sanar a gidan Radio, karfe Goma Za'ayi jana'iza, Alhaji Habib kamar mace kai kadai ya daga. Zaid yace da Hafiz "donAllah ayi prolonging dinshi zuwa Azahar" Hafiz yace saboda me? "Ai gwara a kaita gidanta na gaskia" Zaid yace "ina zuwa" ya fita da Sauri, be tsaya ko ina ba sai gidan Baba Tj, nan ya shaida musu Mutuwar, yace "Allahu Akbar" Zaid yace "Baba, so nake ka kira Mami ka gaya mata, Iliyasu ya dauko ta ita da Safiyya, ba zaa kai Rafee'ah ba sai Mami tazo ta mata addu'a, Ba musu ya lallubo ta a waya, ta dauka da Sallama, Baba "ina kwana?" ya amsa, yanda taji muryan shi ta tabbatar ba lafia, gaban ta ya tsanan ta faduwa don tun ran da Rafee'ah ta tafi taji jikinta yayi sanyi kalau. Yace "ki shirya ke da Matar Zaid direbanshi zai dauko ku ya kawo ku Katsina" cikin daburcewa tace Lafiya Baba? Waye be lafia? Mama ce?" yace aa Mamarki na chan daki kalau take" to baba Gaya min na san tabbas ba lafia" Yan nasihohi Baba ya fara mata kan daukar K'addara, nan ta dago mutuwa akayi, cikin rawar murya tace "Baba, Rafeeq ya rasu ko?" yace "aa, ba Rafeeq bane, Yaruwar sa ce" wasu zafaffen hawaye na tashin hankali suka soma kwaronyowa daga idaniyarta, a hankali tace "Rafee'ah" Baba yace "itace, Aishatu" _Inalillahi wa ina ilaihirrajiun, Allahumma Ajirni fi Musibati wa akhlifni khairin minha_ jikinta ya fara rawa. Ta zube kan kujera, "hakuri zakiyi Aishatu, yau da safe ta tashi da Amai" da kyar tace "Baba yanzu Safiyya zata taho, ni ba zan zo ba, ayi gaggawar kai ta makwancinta, _Ubangiji Allah ya yafe ma Rafee'ah, Allah ya gafarta mata, Allah ya sa chan ya fiye mata nan, Allah ya sa Aljanna firdaus ce Makomarta_ *Ameen* dif ta datse wayar.
Zaid yace " Baba, ya tace? Tace a kai Rafee'ah a rufe ta, ba za tazo ba" Zaid yace "aa Baba, ta zo donAllah, barin sake kiranta" Baba ya dakatar da shi "Aa Zaid, ka barta, chan din zai fiye mata kwanciyar Hankali a bata Space, shes a mother". Ba dan Zaid ya so ba ya rabu da ita. Suka tashi suka tafi Gidan Lema.
Mami ta iske Safiyya a Daki, tace "Safiyya sai ki shirya ko? Tafiya ta kama ki katsina" yanda Matar Zaid ta ga Mami ta san ba lafiya duk da ba kuka take yi ba" tace "Mami Lafiya?" tace "Rafee'ah ce ta Rasu" Inalillahi wa ina ilaohir rajiun tace ta pashe da kuka" Mami tayi saurin fita daga dakin. Sai da ta ci kukanta ta gode Allah kafin ta kira Mijinta Zaid, ya tabbatar mata da Mutuwar yace yanzu ma Wanka zaa mata, karfe Goma zaa yi Janaizar ta. Ya tambaya "ya Mami?" tace "gata nan dai, Allah ya dora mata Tauhidi, tayi tawakkali" yace "Allah sarki Mami, to ke ki lallaba ki shirya, Iliyasu ya kawo ki Allah ya kiyaye hanya tace "Amin".
Bayan tafiyar Matar Zaid Mami ta fito Parlor, ta zauna ta shiga tunani, Allahu Akbar daidai nan Suka rabu Shekaran Jiya, ta tuna Yanda Rafee'ah ke ta nannukarta tun zuwan su Kaduna, yanda bata yarda tayi nesa da jikinta, ta rungume ta ta kwanta kan cinyarta, ko toilet zata shiga sai ta rike hannun Mami ta jata har bakin toilet din ashe duk na bankwana ne? Ta tuna lokacin tafiar ta har ta fita ta dawo da gudu tace Mami kice Allah ya min Albarka, " tayi daria tace Allah miki Albarka Rafeeah, Allah baki miji Nagari, wanda zai kula min dake" tayi daria tace "Ina sonki Sosai Mamina" "nima ina sonki Sosai Rafeeah ta" muje in rakaki Uncle Zaid dinku na waje yana jira. Nan mami ta fashe da kuka mai tsumma zuciya. Allah ya gafarta miki Rafee'ah, na yafe miki duniya wa lahira, Allah ya hada fuskokin mu a Aljannah firdaus..
11:00am.
Rafeeq kwance kan Gadon Asibiti, don a Mak'abarta ya sume yayin da aka Birne Rafee'ah, daga Gidansu zuwa Makabarta yayi suma kusan kala 5, da ance a maida shi gida sai yace shi be yarda ba dashi zaayi Janaizar Kanwar shi, kafin a rufeta ya suma, bayan an rufeta ma haka, Maalesh ne yace da Hafiz, Uncle Hafiz barin kaishi asibiti, ya samu hutu a chan, Hafix yace "kayi dabara Mahmud".
Haka Rafeeq yayi ta zaman Asibiti har sai da aka gana Zaman makoki, da ya tashi ya fara sambatu zaa mishi Alluran bacci.
Bayan Kwana 3 Rafeeq zaune cikin dakin shi, Maalesh na gefen shi, dawowan su kenan daga Asibiti, Maalesh ya k'ura wa Rafeeq ido, kallo daya zaka mai kaji ya baka tausayi, Mutuwar Rafeeah ya mugun girgiza shi, idan an lek'o yi mishi gaisuwa har mutum ya zauna ya gama maganar shi Kallo be ishi Rafeeq ba, Maalesh ne ma dai ke amsa gaisuwar, Bayan an watse Maalesh ke cewa "kai Rafeeq abun ka fa k'ara gaba yakeyi, muma fa duk mun girgiza da mutuwar Fee'ah, barin ma gaya maka abunda baka tab'a sani ba, Ina mutuwar Son Rafee'ah, na sota kamar raina jira nayi lokaci yayi in baiyanar mata da son da nake mata, nayi dakkon sonta da dadewa, amma ta tafi ta barmu, nayi Alhinin mutuwart amma Sai naga ba abunda ta fi buk'ata da ya wucei Addua, sai na dau k'addara ya kasance ko da yaushe ina mata addua, toh idan addua take buk'ata, har mutane suzo don taya ka Addua ka gaza ce musu Amin? Haka akeyi?" kamar Rafeeq zai yi magana sai kuma ya fasa, ya mik'e don fita daga dakin, ganin haka Maalesh yayi saurin mik'ewa yace ba sai ka bar min dakin ba, dakin ka ne, nine zan fita" ya fice ya bar Rafeeq tsaye, yana so yace mai ya dawo amma ya kasa.
Meema da Aneesa kanwar Sauda zaune cikin Parlor, tun randa akayi rasuwar sukazo, Zaid ya shigo ciki, Aneesa ta mik'e da sauri, tace "Uncle Xaid ina wuni?" ya amsa da murmushi lafia lao Aneesa, kinsha hutu ya kano?" tace Alhamdulilah, ya k'arin hakuri? Allah ya jikanta, ya Amsa da "Amin" Aneesa sai zungurin Auntyn ta Meema take tayi, tun shigowar Zaid parlo ta sandare daga zaune, don farat daya taji Son Zaid ya mamaye mata Zuciya, Sai da Aneesa ta takata da karfi kafin ta dawo hayyacin ta, da sauri ta gaida Zaid tare da mai gaisuwa, ya amsa ta tare da cewa "barin hau sama gun Yaya". Ya haye Sama. Meema ta kalli Niece dinta tace "Omg, Wallahi naga mijin aure, ina sonshi, kuma sai na same shi ta halin k'ak'a waye shi? Aneesa tayi daria tace " Kanin Daddyn su Rafee'ah ne, kuma yana da mata" tace "ba mata ba ko Matan sa hudu sai ya aureni". Aneesa tace "muje dai ki gaya ma mommy".
Sama Suka hau dakin Sauda, Meema tace da yayarta "Sis, nayi new catch cikin gidan nan, kuma ance K'anin Mijinki ne, nidai na samu mijin Aure" Sauda ta zaro ido a ranta tana Allah ya sa ba Hafiz bane, karaf Aneesa tace "Uncle Zaid ne" Sauda ta sake Ajiyar zuciya tace "Ke wannan ya miki nisa, yana da mata" Meema tace nidai na samu miji, sai ki min hanyar samun shi" Saude tace "sai ki ja hankalin shi ta hanyar Kissa" tace "Ahap sis har sai kince, kar fa ki manta wacece ni" sukayi shewa tare da chafe wa, Aneesa tace Kinga ni in auri Rafeeq, ke ki auri Uncle Zaid, mummy na auren Daddy, kinga shikenan duniya zata sanmu as Rightful Heirs to the Lema's property. Duk sukayi daria, Meema tace "shi kuma Rafeeq din wayei? Aneesa tace "haba Aunty Meema, so nawa zan gaya miki Rafeeq dan Mijin mommy ne, kuma love of my life, don shi zan aura " Saude ta kalli Diyarta Aneesa, ta san yanda take son Rafeeq, kuma ba za taso yin magana gaban ta ba tace "Aneesa je ki duba yanda Rafeeq yake, m sure he needs someone to talk to" tace "eh wallahi bari inje" ta fita da sauri..