← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 95

Sashe 46

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*This is for y'lls Members of Miemee Bee 👄Novels, You guys are Simply the best, I see lotta _™Nasi-Feeq_ , lotta _™Nasi-Zaid_, too bad no ~™Nasi_Lesh~ , lols😂 ILY'lls❤❤❤ Together we keep it moving💋 *#1love*

Pg4⃣2⃣

"Oh shit" ya fada da ya tuna abunda yace, yau shine da cewa please? Kuma ba amfanin shi ba, sai na wanda ya ce ma wa? Lallai in har bata shiga motar nan ba zai tafi kuwa ya barta, a 6angaren Seebi kuwa, kalmar 'Please' ta maimiata cike da mamaki, Yau Shi R-,Lema ke cewa please, aah akwai cigaba, akwai nasara, amma me tasan in ta tsaya jan aji tafia zaiyi ya barta, kuma ba lallai bane ya dawo a wannan karon, a sakwan da be wuce iku ba Rafeeq yayi shawaran tafia, sakwan da be wuce biyu Nasiba ta fada motar, be tsaya jira ba ya hau kan titi, ko kallon shi batayi ba, shima bai kalleta ba, har suka zo Makaranta, ya kawo ta bakin Department dinsu, ya na parking ta fita tayi banging door shi kanshi ya firgita, ya bi ta da ido yana mamakin Wannan bak'uwar Halin da shi be san da ita ba, to ko dai tana da damuwa ne? Saboda ya san ta kullum ta shigo Motar shi sai ta gaida shi, in ko yayi dropping dinta sai ta zabgo mai addua tana mai Godia, amma yau ba Sannu bare Nagode. Tsaki ya ja yana fadin "Matsalar ta, i dont need her thanks, greetings whatsoever" ya ja motarshi yayi gaba.

Zaune take kan lallausan Rug dake kusurwar dakin ta, jingina tayi kan luntsuma luntsuman throw pillows da aka wa bangaren ado, Grapes take ci a k'asaita ce, Meema ta shigo ta zauna kusa da 'yaruwarta, ta daga kai sama tana kallon POP din dakin, da Walpaper, da wakeken gadon ta, ga madubi shak'e da turarruka masu yawa. Ta dafata tace "Meema, ji yanda kike kallon dakin kamar yau kika fara shigowa" Meena tace "Hmm Sis, ina mamaki ne, rayuwa na gudu, a wani lokaci, ko gidan kanmu ba mu da, ba mu da Sanaar da ta wuce saida Abinci, amma in one time, God has buttered our Bread" Sauda tayi saurin cewa "You mean My Bread?" daria sukayi gabaki daya, tace " Tabbas ke mai sa'a ce, don kuwa duk abunda kika sa a gaba, ba makawa sai kin cimma sa, ga ki da hangen nesa da kuma hikimar magance Nesa tun kan tazo kusa" Saude tayi wani shu'umin murmushi, tana jin dadin yadda kanwar ta ke k'oda ta. Meema ta cigaba da cewa "saidai wannan karon na rigaki hango nesan da zata iya kawo miki cikas, da sauri ta gyara zamanta tace "yi magana Meema" Meema ta gyara zama tace " kin taba tunanin yadda Rayuwa zata kasance miki idan Alhaji Habib yau ya fadi ya Mutu? Tace "Da sauri tace "bangane ba Meema, yi min bayani dalla dalla"
Ina nufin yau in Alhaji ya mutu, in banda tumunin takaba ba abun da zaki tsira dashi? Kina da labarin Yau Alhaji ya mutu tsinke ba za a ba Aneesa ba? Don bata da Gadon shi? Komai zaa tarkata a ba Rafeeq, be fi a baki kaso daya cikin takwas ba, sauran kuwa na Rafeeq ne, shi zaa ba komai" tace Meema ina son Habib, ba na ma tunanin mutuwar sa, kuma ni bazan kashe shi ba sabida Gadon sa be dameni ba" Meema tace "ai ba ina nufin ki kashe shi bane, ina nufin in ta Allah ta kasance ya mutu yau, da me zaki tsira, ai bana tunanin zaki tashi da abun azziki, gashi diyarki bata da gadon sa balle a sa rai zaiyi yawa" Saude tayi zuruuu tana nazarin Maganganun Meema, tabbas tayi Magana kuma abun a duba ne "toh Meema yanzu, meye abun yi?" Meema tace kawai sawa zakiyi ya Mallaka ma Aneesa wasu k'adarorin sa, da dukiya" Saude tayi Murmushi tace "i know what to do, bari ya dawo daga tafiar nan".

Kwanci ta shi ba wuya gun Allah, su Seebi Semester ta ha, don yau suka fara hutun Mid-Semester break, haka kurum taji ita ta na son Zuwa Gida gun Iyayenta. Dama Safiyyar Yau Hajjo ta koma gida, don Nene tace ta koma bakin aikinta ta ji sauki, Nasiba ta shiga gun Nene, "Nene barka da hutawa" Tace "yauwa Seebin Nene" tace "mun dan samu hutun kwana 7, shine nace mu shirya mu tafi Kaduna mu dan chanza guri" Nene ta yi Kamar bata ji ta ba, Seebi ta sake maimaita mata, tace" KE nasiba ki fita ido na, shin ni tsarar kice? Nasiba ta kalli Nene da mamaki, tace me nayi? Nace wani abu da ba daidai ba? Nene tace ki kalle ni ki ce man in zo muje Kaduna hutu, ni yar firamare ce? Sai inje in ma Uwaki zaune cikinem gida, yan unguwa su tacewa Uwar miji ta tare Gidan D'a to ba haka nake ba, in ma Mahammadun ya aiko ki to shima zan gamu dashi" Nasiba ta kalli ta Nene cike da mamaki, shin me yayi zafi haka? Girgiza kai tayi tace "Wallahi you are always out of point" Nene tace "Eh baturen ma yaci kutumar ubanshi, nan gani nan bari" Nasiba ta shige daki tana mamakin Nene, ita in anyi gabas to yamma zatayi, ta gurgiza kai ta hau hada kayanta.

WasheGari
Tun da farar Safiyya Nene ta shiga kasuwar 'yar kutungu, tayo ma su Ummi Siyayya, su garin Alkama, Sansamin yaji, Kuka, busasshan kubewa, daddawa da dai sauran su. Sauri take ta dawo gida, tana shigowa taga Nasiba na kalaci, ta sauke ajiyar zuciya, tace lafiya Nene? Nene tace "Allah Allah nake kar ki tafi, don nasan ki da d'oki, tace "ya zanyi in tafi ba muyi Sallama ba?" Nene tace "yo nasani? Da kin tafi da sai kin raina kanki wallahi" tayi daria, "Me zai faru da na tafi" tace "Wallahi mota zan shiga in biki har kadunan, in lakada miki na jaki, sannan in juyo in dawowa ta Katsina" me Nasiba zatayi in banda daria, daria har da hawaye, Nenen ma Dariya tayi.
Tayi shirin tafiya, Nasiba tace da Nene "kinga ki shirya mu tafi, ya zaayi ki zauna ke kadai a nan, hajjo ba ta nan, DonAllah Nene nah" Nene tace "Shin in tambayeki, Shekaru 21 da daya da nayi nikadai cikin gida me ya cinye ni? Me ya kama ni? Eyi? Nasiba tace " Wanchan Unguwar akwai mutane, kina jin motsin mutane, wannan fa? Tace "Ke ni rabani, ba fa inda zani, Ina nan kinji Nenen Seebi? Allah ya kaiki lafiya ya dawo mun dake lafiya" Amin Nene na, tace to Nene ga wayata nan zan bar miki, sai mu dinga gaisawa muna jin lafiyar Juna, ba musu ta amsa, sukayi Sallama har tasha Nene ta raka Nasiba gaban ta suka tashi. Ta musu fatan Allah sauke su Lafiya. Ba ta bar tasha ba sai da ta ma wani Conduster tatas don yace mata "Hajiya tafia ne?" tace "aa uwarka ce". Tunda ta fara masifa bata yi shiru ba, wai ya mata rashin kunya yana mata maganar Yan tasha, Da k'yar wani mutumi ya lallabata ya Ya fidda ta waje ya sama mata Napep ta wuce Gida.

*Malali Kaduna*

Karfe Hudu saura minti 10 (3:50pm)Nasiba ta shigo Unguwar su,m, a Lokacin ana ta kiraye kirayen Sallahr Laasar, da ta hangi Gate din Gidan su taji wani sanyi ya ratsa ta, ta biya mai Napep kudin shi ta fada gidan, tun daga Gate take kwada Sallama.

Ummin da ta yi Rakiyya tace "Muryar wa na keji haka kamar Seebin Nene? Bata ankara ba taji an fado mata a jiki "laah itace ashe", ta rungume diyarta suna Daria, daga Katsinar? Ina Nenen? " tana chan ta k'i yarda ta biyo ni" tayi daria tace "ba ki gaida Mamin Ayman ba" tayi daria tace "sorry ban lura ba" Seebi ta juya ga inda matan da Ummi ta rako ke tsaye, ga Mamakin ta, matar ita take kallo, ta shagala da kallon ta, Nasiba ta tsurawa matar ido tana son tuno inda ta san fuskar, ta dai daure tace " Ina wuni? Shiru, Ummi ta dan dafa Mami tace "Mamin Ayman wannan diya tacw na ce miki tana karatu a Jamiar Katsina" Firgigi tayi kamar wanda aka tada daga bacci, tace "Allah Sarki" ta juya ga Seebi tace "Lafiya lau, kin dawo Lafiya?" "Alhamdulilah" ba ta jira sunce wani abu ba tace "barin koma gida kafin Ayman ta tashi" to a gaidata inji Ummi, suka juya cikin Gida, Mami ta tsaya bakin gate ta juyo tana kallon bayan Seebi, a ranta tace "Allah mai iko, meyasa nake ganinta kanar Rafee'ah?".

Murna gun Abbi da Anan ba a magana, kamar sun yi shekara basu ga juba ba, nan Nasiba ta dauki wayar Ummi ta kira Nene, har tayi Ringing ta gama bata dauka ba.

*WasheGari*
Tun da Safe Nasiba ta shirya Anan, ta raka shi har Makaranta, ta dawo gida ta ciro Garin Alkaman da Nene ta siyo musu ta tankade shi, Abbi ya fito daga daki, ya ganta sai aiki tankade takeyi, yayi Murmushi yace "Sarkin aiki, kin fa dawo kenan, to me za a mana yau?" tayi daria tace "Barka da fitowa Abbi, Alkubus zan mana" yace "Ahh kice yau zamu kwashi Gara" tayi daria, ta cigaba da aikinta, ko da Ummi ta fito tace zata sa mata hannu cewa tayi "Ummi ki bari, aiki na ne" haka ta zage ta kwaba Alkamar nan, ta yi hadin Alkubus, da kanta ta fita tayo cefane, tazo ta gyara kayan miya da kabewa ta yanka Alaiyahu, ta hada da kifin gwangwani, sai da Kwabin Alkamar ya tashi kafin ta zuba a madanbacci, nan da nan gida ya kaure da k'amshi, bayan ta gama ne ta zuzzuba a Cooler, Ummi tace "Ki saka ma Mamin Ayman, na san zataji dadin shi" Wannan matar da kika rako jiya? Tace "eh ita, tana da kirki, ba su dade da dawowa nan Unguwar ba, ta girmeni amma tana mutuntani" Allah sarki inji "Nasiba" Ummi tace "kiyi wanka ki mik'a mata, tunda Anan ya tafi Makaranta" Nasiba tace "toh".
Chapter 46 · 0% Book details