← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 95

Sashe 24

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun Iso Katsina Lafia, tunda suka shigo Haraban Gidan taji Gabanta ya fadi, ta kalli Uncle Zaid tace "Uncle Zaid gaba na ke faduwa, kamar wani abu na shirin faruwa" Zaid yace "kin fara superstitious beliefs din nan naki ko, ba abunda zai faru kinji Rafee'ah?" tace "Allah ya sa, i cant wait to see my Mami and my troublesome Hamma Rafeeq" Damm gabanshi ya fadi, ana wata ga wata sai yanzu ya tuna Rafee'ah bata san wainar da ake toyawa ba, ba ta san me ya wakana ba tun bayan Zuwan ta kaduna, ko da ta ishe shi Kan tana kiran wayan Mamin ta a kashe sai yace taje India Medical Checkup, kuma Dr ya bata rest so ko waya bata amfani da shi, ta yarda dashi don ta san be mata karya, kafin yace wani abu tuni ta fita daga motar, ta na kiran "Hamma Rafeeq i'm home" da karfi ta ke maganan, Gaban Rafeeq ya fadi jin muryar Rafee'ah, be san lokacin da ya shige toilet ba ya wanke fuskar sa don kar ta ga damuwa itama ta tada nata hankalin.

Cikin gida ta shige ta na fadin wai ya na ji Gidan shiru ne? Ba kowa ne? Alhaji Habib ya fito yana Oyoyo Baby, hajia Sauda tana biye dashi a baya, da sauri Rafee'ah taje ta rungume Daddyn ta tana "Daddyna i've missed u" daga ta yayi sama yana juyi da ita kamar wata baby ita ko tana ta daria. Ya direta yana "i missed u more my angel" taje ta rungume Sauda, Sauda na ta murmushin munafurci tana "haba ai gwara da Zaid ya dawo da ke, tunda ya dauke mana ke gidan ba dadi" ita ko Rafee'ah sai k'yalk'yala daria take yi, tace ina Aneesa? Sauda tace tana chan BUK wurin kanwata, zuwa k'arshen wata zasu dawo" Daddy yace ya Safiyya(Matar Zaid)? Rafee'ah tace "Daddy ta na nan lafia, ta kusa haihuwa ma" Allah ya raba lafia. "Daddy wai ina Uncle Hafiz da Hamma Rafeeq?" Daddy yace Uncle dinki na Yobe na aike shi, Rafeeq kuma na Dakin shi. Tace "Ohh yana jina yayi shiru ya kyale ni ko? Barin je in iske shi" ta sauka k'asa tayi hanyar dakin Rafeeq.

Tunda daga waje take kiran "Bigbro Rafeeq, wai ba zaka fito ka ganni ba? ta kutsa kai cikin dakin, turus ta tsaya ganin Rafeeq zaune kan kujera sanye da Bak'in Gilashi, mamaki ya baiyana fuskarta, da sauri ta je ta rungume shi, ganin yanda ya mata ne yasa ta dagowa da sauri, "Hamma na, baka ganni ba? A hankali yace "naganki, Rafee'ah" baka yi murnan gani na bane? Shiru ya mata, ta dinga mishi tambayoyi be bata amsa ba, Ga mamakin ta sai ganin hawaye tayi ya gangaro kan kumatun sa, cikin rudewa tayi saurin zare Gilashin idonshi, tace "mai ke faruwa ne? Baka da Lafia ne?" Daidai nan Zaid ya fito daga toilet din dakin yace "Rafee'ah, ki rabu dashi, be da lafia ne, kuka ta fashe da tace be da lafia? Wani irin rashin lafia ne wannan? Uncle Zaid ko kallona fa beyi ba, Hamma da kullum ya ganni burinshi ya takura min, ya nemi tsokana na, tunda na tafi Kd be kirani ba, idan na kirashi beya dauka, and yanzu kuma na dawo irin welcome din da zai min kenan? Ko kallo ban ishe shi ba? Ina mai magana ko tanka ni beyi ba? Uncle Zaid ko wani abu yace "na mishi?" da sauri Rafeeq ya rungume kanwarshi ya na kuka itama tana kuka ama ya kasa ce mata komai, sun ba Zaid tausayi, da sauri ya rabasu yace "fee'ah tashi ki shiga ciki" ba musu ta fita daga dakin tayi sama, Zaid ya kalli Rafeeq, yace "if you really dont want her to find out, then be yourself" yana kaiwa nan ya kabbara Sallah don ya san bazai samu amsa daga bakin shi ba. Yana idar da Sallah ya kalli Rafeeq yace "muje cikin Gida" Rafeeq ya dago ido ya kalleshi zaiyi Complain amma maganar ta mai nauyi, Zaid yace "ina jiranka" yayi gaba ya bar shi Zaune be da niyyar motsawa".

Aunty Yaushe Mami Zata dawo? Kafin Sauda tayi magana Zaid dake shigowa Parlorn yace "nace miki sai taji Sauki, Dr ya bata bed rest, soon zata dawo" ya karashe maganar yana me kallon Sauda yana mata inkiya da ta goyi bayanshi, sai a yanzu ta gane dalilin da yasa dazun Rafee'ah ba tace ima mamar ta ba, wato sun boye bata, aiko ba zai sabu ba, sai ta samu hanyar fallasa mata. Zaid yace "Aunty ina Yaya?" tace "yana nan Office in kusa da dakin shi" Zaid yace da Rafee'ah "ki shiga ciki ki kwanta ki huta" ta mik'e ta nufa daki. Sauda tayi Parlorn Alhaji Habib, Zaid ya rufa mata baya.

Yana zaune, Zaid ya gaishe shi, Alhaji Habib yace "Engineer har an iso? Ya hanya? Ina aka tsaya ne sai dai na ga shigowar yar gidanka? Zaid yace "Alhamdulilah, Ina Dakin Rafeeq ina Sallah" Alhaji yace "hmm lamarin Rafeeq sai gaba yake k'arayi, bansan me na mishi ba" Zaid yace "ba ka mishi komai ba, lokaci kawai yake buk'ata maganar shi ce ma nake so muyi" kamar an jefo shi ya shigo parlorn, yayi Sallama amma Zaid kadai ne ya fuskancin Sallama yayi, ya samu wuri ya zauna kusa da Zaid, Zaid ya tsura mai ido yana mai nuni da ya gaida Mahaifin shi da Auntyn su, fuska yayi yaki kallon side dinsu. Zaid dai ya san bazai tanka ba ya juya ga yayan shi yace "Rafeeq dama na kiraka ne nan gaban Ubanka mahaifi, shawara zamu baka, ba mu da gatan da zamu maka da ya wuce Addua da Shawara, kai Baligi ne kasan ciwom kanka, kasan abun da yake daidai kasan wanda ba daidai ba, kasan fari kasan bak'i, Rafeeq Abun da ya faru ina so Ka dauke shi a matsayin kuskure, Kaddara, ka rungume kaddararka, Kai musulmi ne, ba wai nace ka yafe ma mahaifiyar ka bane, so nake ka gano gaskia ka gane kurenka dukda ba laifinka bane, shisa kaga na daina takura maka da maganar ta. Alhaji Habib da matarshi dai ba su ce komai ba Zaid ya cigaba da cewa " Well this is not about your mom. Its about you, ina so ka maida hankali ka fara last semester din nan naka da kyau, yanda kowa ke Alfahari da kai kar ka bamu kunya, kamar yanda kake yi da, make us proud like always, ka fita da first class dinka that you truly deserve kajih?" Rafeeq kallon window kawai yakeyi, be tanka Zaid ba.

Don dai ya sa Rafeeq Farin ciki Zaid yace "kuma zan siya maka mota son ranka, ka fadi wanda kake so Gobe ka ganshi a gidan nan" nan ma be ce komai ba, Hakan yasa Alhaji Habib yace "toh nima Uncle din Yara baza a barni a baya ba, nima ina da kyautar da nakeso in ma Rafeeq" ya mik'e ya fita duk suka bishi da ido gaban Sauda ya fadi tana ta tunanin meye kyautar da Alhaji zai ma Rafeeq, Jim kadan sai gashi ya dawo da wasu files ya zauna, yace "Sauda da Zaid kuyi shaida, Kafin a samo Shaidu, Companyn Tie and Dye na Sokoto, da Hide and Skin na Keffi na Mallaka ma Rafeeq, ko na mutu ba su a cikin Gado, kuma da ka gama Service, komai na other Companies dina zasu dawo k'arkashin ku kai da Rafee'ah, Zaid ya washe Bakih yace kai MashaAllah, Angode Allah ya k'ara girma" Sauda kuwa Ba tasan duniyar bakin cikin da ta lula ba, kiris ya rage ta fashe don ta kumbura, ta kasa boye bakin cikinta da hassadar ta.

Amsa Rafeeq, Alhaji ya miko mishi Files din, Zaid ya mai Alama da ya amsa, kamar ba zai karba ba ya sa hannu ya amsa a hankali yace "nagode" Daddy yace tashi kaje ka adana. Kamar jira yake ace yatashi ya tafi ya mik'e da sauri, Files din ya mik'a ma Zaid, Zaid ya sa hannu ya amsa, yana bashi ya fita daga Parlorn. Zaid ko Farinciki yake tayi. Sauda kuwa ta na hada hanya don ta daina gani saboda bakin ciki ta fita.

Daki ta fada ta fashe da wani irin ihun takaici, ta daura hannu a kai, na shiga uku, Alhaji har ya fara rarraban kamfanonin ka? Be sakani cikin lissafi, wato daya gama Sabis zai maida komai karkashin sa shi da kanwar shi, ni kuma da tawa diyar oho, wallahi ba zai sabu ba, sai inga ta inda zai gama makarantar balle yaje service din har ya zama wani tsiya , ita kuma Rafee'ah sai ta tsani kanta, don boka na kan tudu zan sa ya Sa Rafeeq ya mata Fyade, ko kuma ta zama karuwar Yayanta, sai in ga ta inda zasu zama abun Alfahari ga mutane. Sai kowa ya tsanesu, shima Alhaji ya tsine musu ya koresu daga gidan shi, su shiga duniya, sai ya rage daga ni Sai diyata sai muci karenmu ba babbaka ta sa shewa kamar wata zararriya da sauri ta ciro wayarta ta latso number Boka na kan tudu ta labarta mishi plan dinta. Yace "Saude wannan magana ba ya waya bace ki zo Gobe kawai sai a duba" tace "to na kan tudu, ka tsumayi zuwa na gobe, da Asubar fari zan taho".

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg2⃣8⃣
As promised, This page is for you Aunty Baraka❤❤❤

Washegari Alhaji Habib yace da Sauda zata raka shi Kano, haushi kamar ya kasheta don tayi niyyan zuwa gun boka na kan tudu yau, haka suka tafi Kano ba don taso ba.
Chapter 24 · 0% Book details