Sashe 60
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
wulakanci, ta chakare dankwali gaban goshi, hannunta kan k'ugu, Meema da Aneesa na bin bayanta, ashe Aneesa taje ta gaya musu k'arya da gaskia, Nene tayi saurin mik'ewa shi ko Rafeeq tunda ya musu kallo daya ya dauke kai ya cigaba da cin Abincin shi, Nasiba tuni ta fara kyarma, Aneesa tace "Ya Rafeeq me kakeyi a nan?" kallo bata ishe shi ba, Saude ta kalli Nene galala tace ke tsohuwa, nazo in ja ma wannan kilakin kunne, amma tunda gaki to gwara in miki sai ki ja mata kunnen da kyau, Wannan karamar kilakin na bibiyar Mijina, tana bibiyar k'anin mijina, Kuma tana bibiyar dan mijina don ga zahiri nan, ta nuna Rafeeq, har ta isa ta daga hannu ta mari diyata? Ta sa k'awayenta su mata duka? Wannan 'yar iskar har ta isa? Meema ta chafe "ni ai kamar na so in gane wannan tsohuwar, Anee ba ita bace ta taba tsaida mu a hanya ta bamu waya ko mu kira mata Uban wa? Matsiyaciya, Asiri suke ma mutane dube Rafeeq da be ko kallon pampon gida ya zage ya bude ciki yana cin Abinci, dubi kayan jikin ta komi irin na Anee, Asiri suka ma UncleZee ya siyo mata irin shi, banzaye matsafa kawai. Har yanzu jikin Seebi be bar rawa ba, Nene ko sai dai ta bi wannan da kallo ta bi wannan da ido, sai da ta gama karance su tsaf. "Ke Aneesa dauko Ayman mu ta fi gida, idan na k'ara minti 1 anan zan iya sik'ewa don nan ko gidan Karena Albarka" Aneesa ta dauki Ayman, Ayman ta 6are baki, sai a sannan Rafeeq ya dago, da rinannun Idanunshi yace "Let her Go" be san meyasa ya kasa tanka su Saude da suke cin Zarafin su Nene ba, "Saboda mene Rafeeq?, mune fa dolen ku, baku da kowa, mune yanuwanku ba su ba, You are not related by any chance" cikin tsawa yace "I said let her go" da sauri Aneesa ta direta, ta tattaka ta nufa Nasiba ita kuwa ta kasa daukarta, don gudun abunda zai dawo, Rafeeq yace "duk abunda zakuyi ko zakuce kuce, but dont you dare touch this Soul" Saude ta kalle su ta watsar tace "ku taho mu tafi, tsayuwan mu nan is useless, ke dai Na gaya miki ki jama jikar ki ne ko diyarki kunne, in ko ba haka ba to sai zaman Katsina ya gagareki" Nene tayi murmushi tace "nidai tambaya daya zan muku, donAllah kune kuka taran ma Nasiba jiya da daddare?" Aneesa cike da Rashin kunya tace "Eh mune, yanzu ma ba ita ba har ke sai mu taran mawa" Nene tayi daria tace "Alhamdulilah MashaAllah dama amsar da nike son ji kenan" ta kwance dankwalin kanta ta daura a kai, ta kalli Nasiba tace ke dauki Aymana ku shige daki kar ki sake ki fito, Nasiba ta san Nene ba Alkhairi zatyi ba tace "Nene DonAllah--" Nene tayi saurin katse ta da cewa "dan Ubanki ku shige daki nace ko, zaki dauketa ko sai na fara da ke? Jiki na rawa ta dauki Ayman ta shige daki, Meema tace " What is she trying to do" Aneesa tace 3 against 1" sukayi daria duka.Nene ta k'ulu ga turanci sun yi, sun k'ara da6awa ta kalli Saude tace " Uwarki ce Ogan kilakai, cikin dakin kwarto ta mutu, ke kuma randa na baki waya nace ki kira min, ai baki tsaya kinji wanda nace ki kiramin ba, Ubanki nake so ki kiramin a lokacin, cikin ku wa ya fara taba fatar Seebi? Saude da ta gama harzuk'a da zagin da tsohuwar nan ke musu tace "Nice nan" bata ankara ba taji Nene ta buggan mata Baki, bata ankara ba taji Alamun gishiri gishiri a baki Aneesa tace "Laaaah Jini? Kika fidar ma Mom dina Jini? Tayo kan Nene gadan gadan, nene ta kwashe ta da Mari, Marin da ta ga Stars na walkiya, tace "ga Marin Da kika ma Nasiba,Yo ni Allah na tuba Ai Ba Uban da ya isa ya sa Zaman Katsina ta gagareni, naci uwarki in baki hana zaman katsina gagarata ba" Rafeeq yayi murmushi yace "Interesting! Thats what i'm talking about" ya kwashe plate da cup dinshi ya kai kitchen, ya fito yana daria yace dasu "You all can leave while you still can, this the only opportunity you have, is now or never" Saude ta dago ta kalleshi cikin masifa tace "I never back down from a fight, this woman will regret doing this to us" Rafeeq yayi murmushin mugunta yace "in that case, i'll sit back and Watch" Nene tace "Uban me kake ce musu? Yayi Daria yace "ce musu nayi su fita shine tace wai ba zasu fita ba sai sun koya miki hankali, wani abu ma da tace ba zan iya fada miki ba saboda yayi nauyi da yawa" Nene tace "kayi wa Allah ka gaya min? Girgiza kai yayi, Nasiba daga ciki take cewa "Hamma stop, its not funny" Nene kuwa cewa tayi ''in kika fito sai kinci ubanki Nasiba" ta damk'o wuyan Saude ta chusa ta a hammata, ta matse, Meema tayo kanta,Nene ta wurga Saude kamar kayan wanki Saude ta buge da bango, Nene ta ci nasarar damk'o gashin dokin Meema ta dinga ja, Meema sai ihu takeyi, Nene ba ta bar Meema ba sai da tsinka kitso daya, kan Meema sai jini itama ta yadata k'asa, ta cicibo Aneesa da har yanzu bata gama kukan marin da ta sha ba, Nene ta buge bakinta tace ke me bakin rashin kunya ko? Ni kikeyi wa turanci? ta waiga ta hangotayizar da ta dauko jiya don dukkan Rafeeq, ta waiga taga Rafeeq na darian mugunta harda rik'e ciki, tace "kai dunkum mik'on Chazar chan" da sauri ya dauko ya mik'o mata, ta dinga shauda ma Aneesa, Aneesa na ta ihu, Saude ta taso don cetar diyarta ita ma bata tsira ba, Nene ta hau shauda mata itama, Meema kuwa lafe wa tayi chan baya, dafe da kanta, Saude Ihu, Aneesa Ihu, Rafeeq Daria harda Hawaye, jin Alamun zaa shigo yasa tace "kai dunkum maza kaje ka rufo gidan nan" Rafeeq harda tuntube gun fita don tsabar dariya, nan suka ci Karo da Zaid, cikin tashin hankali yace "Feeq ihun me nakeji haka?" Rafeeq daria ya hana shi magana sai nuna baya yake tayi, Zaid ya shiga da sauri, ganin Nene na laftar Saude, Aneesa da Meema kamar Allah ya aikota ya sa shi cewa "SubhanAllah, Nene me zan gani haka?" ba ta fasa laftar su ba tace "Wallahi Zaidu bawan Allah ka matso gurin nan sai na Lafta maka kaima". (Toufa Readers, shin Hankalin Nene Daya?)