Sashe 10
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kai Bahba akwai damuwa fa" Anas yace haba miloniya, wace irin damuwa? Me zai dameka Hafiz yce Wallahi kudin sigari na neman gagarata, gashi yarinyar nan Sofy na bina bashin eh yane har 250k, ni ban san yanda zanyi ba wallahi" Anas yace ba dai kudin nan sun kare ba? Hafiz yace "tas, komai ya ware" Anas yace "to kaii, ai gidanku da masu shi kawai ka tambaye su" Hafiz yace "kai tsaya Anas, nifa ina da kunya, ba a kai shekara 3 da naje gun yayana na mishi rashin kunya kan Gado na, ya dauko ya bani, Kawai yanzu saboda ta bare dani sai naje na tambaye su? Kasan bansan raini, ko a min wani gani gani, balle wurin kane na Zaid, kawai ka samo min mafita" Anas yayi daria yace bigboy no raini, to abun da nake gani kawai ka dan zaro kudin ba tare da sanin su ba, tunda kasan ma'ajiyar" Hafiz ya bude baki yace kaii, duk iyarshege na ba ruwana da sata, ba ma zan iya ba, kai ni ko barawo naga an kama ji nake kamar na harbe shi balle ni in dauka kai samo min wata mafitar, Anas yace "kai fa dan kauye ne, waya ce ma sata ne? ai ba sata bane, ai Baban ku daya, kar fa ka manta abun bros na bros ne" Hafiz ya sheke da wata mahaukaciyar dariya ya na nuna Anas da hannu yace bad boy, kuma haka ne ai, gaskia ka fada, Abun bros, na bros ne..
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg1⃣2⃣
Anas ya cigaba da cewa "Ka same su kace su baka hakkin ka kana da bukatar su, duk yanda zasu so shawo kanka ka fandare musu ka bada ma idon ka toka, duk inda suka bullo maka to ka bulle musu" Hafiz ya jinina kai, yace "toh, bari zan gwada bayan bikin Yayan sai na bijiro musu da bukata ta" Anas yace "bayan biki ai ya gama bushashar sa, yanzu ya kamata kaje ka sake sa" Haifz ya mike yace "bari inje" Anas yace Allah bada sa'a kar ka manta, sai ka nada ma idanuwan ka toka".
"Yadai Hafiz?" naga kamar bakinka akwai magana? Ya akayi ne?" Habib ne ke tambayan Hafiz da tunda ya shigo dakin yake ta kame-kame. Hafiz yayi ta maza yace "Yaya, Gado na nake so a bani in rike a hannuna, a bani hakki na" Habib cike da mamaki yace "Lafiyar ka Hafiz? Bakaji me baba Tijjani yace ba? Sai kun gama Jamia za'a baku, Hafiz ya fandare ido yace "shidai a bashi yana da buk'ata"
Habi yace "to shikenan Hafiz zan yi shawara da Baba Tijhani".
Hafiz ya dan yi ysaki yace "Yaya, Gado na ne ko? To nace abani kayana ban son ajiyar, ina da hankalin da zan rike abu na, banga dalilin yin shawara ba, tunda dai shi da kanshi ya kira a ka raba Gadon nan, toh ni dai nace a bani kaso na"
Yanda hafiz yake magana ya ba Habib Mamaki, zuciya taci Habib ya mike yace biyoni, ko kunya Hafiz be ji ba ya bishi, a waje suka ga Zaid, da sauri ya taro su yace "lafiya? Yana ga fuskar ku ba walwala? Habib yace "kaima biyo mu" ya fada motar sa ya bar gidan hanyar Bank yayi. Zaid da Hafiz mota daya suka shiga, a hanya ne Zaid ke tambayan Hafiz" Bros, wai ya naga yaya haka? Me ya faru? Hafiz ya dan tabe baki yace" ba fa abin da ya faru, kawai don nace yaban Gadona a hannuna ba sai ya ajiye min ba, ni zan aje abu na da kaina shine ka ganshi haka"
Cike da mamaki da takaici Zaid ke kallon shi yace "Hafiz kasan me kake cewa kuwa? Me zaka yi da Gadon ka haka? Idan wani bukata ne dakai ka sanar dashi, shi me iya baka ne ba tare da ka taba Gadon ka ba, Haba danuwa na" da sauri Hafiz ya katse Zaid ta hanyar daga mai hannu yace "in kai yaro ne, ni ba yaro bane, ina da damar da zance a bani hakki na, idan kao ba za ka amsa naka ba, to ni zan amsa nawa, so please spare me the lecture"
Kasa magana Zaid yayi har suka zo Safe din babansu, inda ya ke ajiye kadarrorin sa, Tuni Habib ya haye sama, suka bi bayanshi, Cikin Lokaci kalilan ya tattara duka Gadon su, da ma a kashe suke, ya kalle su yace "tunda, baba ya rasu ban taba daukar ko sisi ba nayi amfani dashi, duk kudin da kuka ga na taba to kudi na ne, hakkin gurin Aikina ba na Gado ba, to yanzu Hafiz ka bukaci Hakkin ka, ni Musulmi ne na san hukuncin wanda ya danne ma wani hakki, nikuma bana daga cikin masu dannewa mutane hakkinsu" ya tura mai wani dan safe box yace "Wannan Miliyan hamsin da hudu(54) ne, a ciki akwai filaye 3 da location dinsu, da gidaje 2 a garin Katsina" ya juya ya kalli Zaid yace kai kuma ga naka hakkin Miliyan hamsin da--" da sauri Zaid ya katse shi ta hanyar cewa "Haba Yaya? Me zanyi da kudin nan? Ni bank'i a sadakar da su Allah ya Jikkan su Baba, ba abunda zanyi da su, shi da ya ga zai iya ai Shikenan ka bashi hakkin sa" a fusace Zaid ya tilla ma Hafiz key din mota ya juya ya bar gurin rai a bace.
Hafiz ya duka ya dauka key din motar da murmushi a fuskar sa yace "Nagode Yaya, hakika kai uba ne a gurin mu,tunda har ka san Hakkin dan Adam baka tauye ni ba, Nagode Allah ya bar Girma" mamaki ya hana Habib Magana. Hafiz ya dauke Safe din ya fita.
Sai da ya kai Safe din Bankin da Baban su ya bude musu kafin ya kira Anas a waya, tunda suka hadu da Anas, Anas ke faman kuran ta shi" The multiple Millionaire, yanzu za a dama da kai, ina dukiyar? Hafiz ya dan bata rai yace ba ruwanka da inda suke" Anas yayi daria yace to shin kai filayen nan d gidaje me za kai dasu? Ai kawai kasa su a Kasuwa ka ci kudin su, in yaso in Ka tashi mallakar Gida sai ka gina Uban uban su".
Da wannan huduba na Anas Hafiz ya sa gidajen shi da filayenshi kasuwa, a ka siyesu a wulakance ba tare da sanin kowa ba, Hafiz ya zama wani tauraro cikin abokan shi, yayi ta musu bushashar kudi.
Baba Tijjani yayi fada sosai da yaji abunda Hafiz yayi, amma ya fi ba Habib laifi akan biye mishi da yayi, Habib yace "Baba ya zanyi dashi?, tutiya yakeyi Hakkin shi ne, ba wanda zai danne mishi, baba naga nima wannan nauyi ne ka sa mun, shiyasa na sauke nauyin, shi Zaid da na mika mai naahi kin amsa yayi yace ba abunda zai yi dasu, ina ga kar ka daga hankalin ka, kowa yayi da kyau zai gani. Baba ya jinjina kansa yace "Allah shi kyauta" Zaid "yace Amin".
Bayan Sati daya
Aka sha bikin Habib Iro Lema da Amaryar sa Aishatu Tijjani Masanawa bisa sadakin Naira Dubu Dari. Biki ne wanda ya amsa sunan biki, ba a tsawalla ba, ba ayi karya ba, ko lefe akwati 6 yayi a cewar Baba Tijjani Albarkar aure akeso.
Ran da akayi dinner Hafiz ya taka rawar gani, don sai da masu Kida suka san da zaman shi, don dubu dubu ya dinga likawa, Suko sai kara kudashi suke suna cewa "kanin ango hafiz mai naira" shi ko kanshi sai kara girma yake yi ya cigaba da rawar sa yana ruwan liki. Da yawa cikin mata sun kyasa Hafiz don a cewar sa yaro da kudi sai a bashi ya sha. Habib zaune a high table yana kallon Hafiz na barin kudi. Hafiz ya koma wani abu daban, kamar ba kanin shi mai kunya ba, amma ji lokaci daya ya fandare ya zama mara ta ido, ya tuna satin da ya wuce inda hafiz ya sameshi a parlo yace "Yaya Ya shirye shiryen biki?" Ba yabo ba fallasa Habib yace "Alhamdulilah Hafiz muna tayi" Hafiz yace "Allah taimaka, yaya ga gudummuwa ta bikin ka" ya ciro wani da case, ya bude mishi, sarka da yan kunne ya mika mishi, Habib ya sa hannu ya amsa, Habib baki bude, yace Hafiz me zan gani haka kamar sarkar Zinari? Yayi daria yace Zinari ce yaya, a matsayina na kanin ka shine na ga ya dace na baka gudummuwa, ka hada a lefe" Habib ya bude baki da ya kara kallon Sarkar, ya tsorata da lamuran Hafiz, yace Hafiz wannan sarkar da kake gani Jiya da naje Siyayya a Shoprite a Kano na tayata, wallahi exact sarka, kasan nawa nagani? 450,000. Tsadar ya hanani daukarta amma tayi kyau, naga dai akwai Zinari a lefen da na sa shisa na barshi, Hafiz meyasa ka kashe makudan kudi wurin siyan sarkar nan? Hafiz yayi dan daria yace "yaya kenan, toh kare da kudin sa sai ya sha lahaula" so nake nima na taka rawar gani a bikin yaya na mai sona, shisa na cire kudi har haka na siya maka, kuma ko da ya fi haka zan siya, don su san cewa ba Tsiya a dangi Lema, saboda haka yaya gashi" Habib yace shi sam ba zai amsa ba, Hafiz ya bata rai, yace don ba maman su daya ba shine ya ke nuna mai wariya, da Zaid ya kawo mishi abu amsa zaiyi, amanar da baban su ya bashi kenan? Nan da nan Habib ya rude yace"haba Hafiz ya kake magana irin wannan? kasan da kai da Zaid daya kuke a wurina" yace toh idan haka ne ka amsa, Habib ya amsa yace toh "Nagode"
Habib ya kai kallonshi kan Zaid da ke zaune a gefe yana kallon mutane, shi ko dancing floor din be shiga ba, a ranshi yace Allah ya shirya Hafiz. Haka aka gama taron biki aka kai Amarya Gidan ta da ke Layout.
(Amarya Aisha Allah bada Zaman Lafiya)
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg1⃣4⃣