← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 95

Sashe 20

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baba ina kwana?" Sauda ta gaida baba mai gadi, Cike da faraa da rawan jiki ya amsa da "Mun tashi Lafiya Hajia?" tace "Alhamdulilah, dama dan Ganyen Latas (lettuce) ke so ka siyo min" yace "toh toh ba matsala, barin samo yaro ya siyo don ba a bar gate din haka ba ba kowa" "aa baba kai zaka je ka siyo, sauri nakeyi" tace a dan fusace, ya danyi shiru sai yace "to, barin in yi sauri in je" nan ta tsaya har sai data ga ficewan shi, ta lek'a taga yayi nisa. Ta hango motar mak'ale daga nesa ta kira shi a waya yace "hello baby?" tace ka shigo mak'ale" yace "toh gani nan".

Tare suka shiga cikin gidan, parlo ta tsayar dashi tace ina zuwa, lek'awa dakin Aishatu tayi taga tayi daidai kan Gado tana sharar bacci. Murmushi Sauda tayi, ta janyo laptop din tayi shut down, ta maida cikin jakkar ta ajiye kan side drawer, ta kwashi sobon ta da cup ta fita dashi, ta dawo ta dinga bubbuga Mami Aisha, amma ko shurawa batayi ba, kamar matatta haka take kwance. Saude ta danyi ihu taga ko zai tada Aishatu, amma ko ta motsa, Sauda ta saki murmushi tace things will go as planned.

Bayan Minti Talatin(30 mins Later)

Bakin Gate Hafiz ya dinga Horn, ba alamun Baba mai gadi, to ko ina yaje? inji Alh Habib, daidai nan Rafeeq ya danno motar shi kwanar Gidan, ya k'araso, Ganin Motar Uncle Hafiz tsaye ya sa shi fitowa daga nashi motar, zuwa yayi ya k'wank'was kofar side din Uncle Hafiz, yayi winning "Sannun ku da zuwa Uncle Hafiz, Daddy Sannu ya hanya? Bamu san yau zaku dawo ba" Suka amsa mishi gaisuwan su, Uncle Hafiz yace "mu kam Rafeeq bude man gate dinnan, Bansan inda Baba yaje ba" Rafeeq ya kalli Gate din yace "to ko ina yaje? Its unlike him" ya karasa tare da shiga gidan don bude Gate, Uncle Hafiz ya shigo da motar sa, Rafeeq ma yaje ya shigo da tasa. Sauda na jin dirin motar su ta fara tsalle, ta gyara zaman kan kujera tarw da rafka Uban tagumi hannu bibbiyu.

A tare su 3 suka shigo parlorn, Alhaji Habib na ba Rafeeq labarin Bussiness trip din su, suka shiga da Sallama, Ta dago ta amsa a sanyaye, Sannun ku da zuwa Alhaji, Hafiz sannu" "sannu ya gidan? Rafeeq yace "Auntyn mu lafia naganki haka?, u look disturbed" tace "Rafeeq, wallahi Mami ce naji ta shiru, tana daki tun da na tashi, na kwankwasa na kwankwasa shiru, na zata ma ta fita ne amma baba maigadi ya bani tabbacin kai kadai ka fita yau" Rafeeq yace "toufa, its unlike her baccin Safe, This is just 12:30" Sauda tace "nima dai haka nagani" Hafiz maybe she needed the sleep, shes just sleeping" Alhaji Habib da yaji Hankalin shi ya ki kwanciya, yace "kaii Rafeeq, je ka tado ta, Azahar ma ta kusa" Rafeeq ya haye sama, Sauda ta cigaba da cewa "tun dazun da mukayi waya da kai na lek'a don in gaya mata dawowan kuamma shiru na jita wallahi".

K'wank'wan "Mami kina ciki?", ya murda k'ofan sai dai damk'e ya jita, yace "mammy, ki bude Rafeeq ne, ko duk baccin ne haka? "Mammy mana, ki bude Daddy ya dawo" nan ma shiru, duk ya rude ya shiga k'wankwasa kofar iya karfin shi.

Alhaji Habib ya dan daga murya yace "Rafeeq Har yanzu ba ta bude ba?" daga sama Rafeeq yace "Daddy ba ma ta magana, kuma kofar is Jammed" da Sauri Alhaji Habib ya mik'e ya hau Saman, su Hafiz suka rufa mai baya. Shima knocking ya fara yana cewa "Shatou na, kina ciki? Are you okay" Shatou taso ki bude mana k'ofa" Sama sama sukaji a na magana, da suka kasa kunne sukaji muryan namiji ne na cewa, "Mun shiga 3, Aisha ki tashi, tashi maigidan ki ya dawo, Haba Aisha duk gajiyan ne, ai ya kamata ki tashi daga baccin nan haka, ki tashi ki nemo min hanyar fita"

Rudani da firgici ya ziyarci zuciyar Alhaji Habib, kirjin shi kamar ya tsago daga rigar shi ya fado don tsoro, hannu ya sa ya toshe bakin shi don wani kuka da yaji ya zo mai, yana k'okarin lalibo adduar "Innalillahi wai inna illaihir raji'un"
"Allahumma arjirni fi museebati wa akhlifni khairin minha.

Hafiz kuwa take Ran shi ya bashi wannan makircin Sauda ne, ya kai duban shi ga Sauda yana mata kallon tuhuma, da ta lura da kallon da Hafiz ke mata, ta girgiza kanta alamun ba ruwan ta, tayi saurin kawar da kanta daga duban shi.

Rafeeq ko da be fahimci komai ba ya cigaba da k'wank'wasa kofar, "Mami na Open up please, you are making us worried" ji yayi an taba k'ofar, ya matsa baya yana murmushi ya kalli Daddyn shi, yace "Dad, she's opening up, she's fine". Bawan da yace da shi komai, sai k'ofar da suka tsura wa ido.

Mak'ale na cire key ya murda kofar ya danna a guje har yana buge Alhaji Habib da ke kan hanyar shi, duk suka bishi da ido, Hafiz yayi yunkurin binshi da gudu Alhaji Habib yayi karfin halin rik'o Hafiz, ya girgiza mai kai alamun rabu da shi, Rafeeq cike da alamun tambaya yace "Daddy waye shi?" Alhaji Habib be ce komai ba face hawayen da ke zuba daga idanun shi, ya matsar da Rafeeq gefe yaym shiga dakin Aishatu, burin shi ya ga Aisha ta ce mishi "mafarki yake, this is not true" don so yake ya tashi daga wannan mummunan baccin da yake, Hafiz ma ya bi bayan shi, sauda ma ta rufa musu baya suka kutsa dakin Mami Aisha.

Rafeeq da shifa kwatakwata k'wak'walrshi ta dode, be gane komai ya bi su a baya. Hafiz yayi saurin dauke kanshi daga duban Aisha, Sauda kuwa daura hanayenta tayi guda biyu a kai, Alhaji Habib ya zame k'asa tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma rai, Rafeeq da ke tsaye kamar mutum-mutumi (Robot) don duk wasu daurar da ke aiki a k'wak'walwar shi ta dauke dif, sakamakon abun da ya gani. Mahaifiyar shi ce Kwance Zindir ba kaya haihuwar Uwarta. Rafeeq da karfi yace "Mammmmmmmiiiiiiiiiiiiiiiyy" firgigigit Mamy Aisha ta tashi.

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg2⃣5⃣

Da karfi Mami Aisha tace "Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, ne zan gani haka?" ta fada tare da neman abun da zata kare jikinta dashi, da sauri Sauda ta bude Closet dinta ta ciro mata zani da hijab ta bata, ta amsa da sauri ta suturta jikin ta. Ta bisu da kallo daya bayan daya, ta fashe da kuka, me ya faru dani? Aljannu suka shige ni ko? Suka min tunbur? Kumin magana" Sauda ta fara kukan munafurci tace haba "yaya, ya zaki ce haka? Kwarto fa kika kawo cikin daki, amma yanzu kina neman cema na ba kisan me kikayi ba? Zurum ta zube a kasa, don kafafuwan ta sun gaza daukar ta, a ranta tace kwarto? Ta dago taga yanda Alhaji Habib ke zubar da hawaye da sauri ta rarrafa gurin shi, ta rik'o hannun shi, Kamar wanda shocking ya taba, yayi saurin janye hannu shi tare da mik'ewa, ya nuna ta da yatsa yana kuka, "Aisha, kin cuceni, kin haince ni, kin ci amana ta, was it hard for you to wait for me?" kuka take yi sosai, ta kasa cewa komai sai girgiza kanta da takeyi, da kyar tace "kayi hakuri Habibullah" wannan magana da tayi ne ya sa shi tabbatar da zance, shikenan Aisha ta ci amanar shi, ta kawo kwarto har cikin dakin ta da tsakar rana, ba tsoron Allah. Da kyar yace "Aisha na sake ki saki daya" ya fice daga dakin, Sauda ta hau kururuwa ta bishi a baya "haba Alhaji be kamata kayi haka ba, be kamata ka yanke hukunci kana bacci ba, Alhaji ka maidota yanzu pls" tsawa ya daka mata yace "Saudat, kina so ki bita kenan? Da sauri tayi shiru kar daga neman kiba ta nemo rama. Ba ta ji dadin saki dayan da Alhaji ya mata ba, duk a zaton ta saki 3 zai mata, amna dayan ma ba laifi, zata tabbatar Aisha ba ta dawo gidan ba har abada.

Hafiz ya kalleta cike da tausayi tabbas wannan aikin Sauda ne ya rasa me zaice shima ya fita ya rage daga Rafeeq sai Mami, har yanzu tana nan duk'e inda Habib ya barta, Rafeeq ko na nan tsaye, ya kasa motsi, abubuwan ke dawo mishi kai, ya kasa yarda da Abun da idon shi yagani, da ya runtse ido Mami yake gani zindir, Mami ta dago kai a hankali ta sauke su kan Rafeeq, da jijiyoyin kanshi sun mimike, fuskar nan tayi Ja, idanuwan sa ma sun kada sunyi jazir, Mami bata damu da halin da take ciki ba ta mike ta nufo Rafeeq, yanayin da ta ganshi ya firgita ta matuk'a, ba ta taba ganin Rafeeq a haka ba.

Hannu ta cire zata riko shi don ta zaunar da shi kan gado, da sauri ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu, yace "dont touch me, Kar ki taba ni" cike da mamaki ta kalle shi, tsana da kiyayya taga ni kwance kan fuskar Rafeeq, yace "bana so in sake ganinki" baki na rawa tace "Rafeeee--q" yace "Wallahi na tsane ki" kafin ya sake wani magana yaji wani lafiyayyen mari tassss a fuska, hannu ya sa ya dafe kuncin sa, ya na dagowa ya sake ji a kara sakar mishi da wani marin da ya fi na dazu, duk a zaton shi mamin sa ce ke marin shi, dagowa yayi don sake yab'a mata wasu bak'aken maganganu, sai ya ga akasin haka, Hannun Mami ya gani rik'e da hannun Uncle Zaid da ke niyyar sake marin Rafeeq karo na 3, ta tare shi ta hanyar rike hannun.
Chapter 20 · 0% Book details