← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 95

Sashe 37

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daga gidan su zuwa gidan su Nasiba yayi tsaki yafi dubu, gashi yanzu fi Minti 5 yana tunanin yanda zai shiga gidan, Kamar yayi kuka, Ya ciro wayar shi ya tura ma Zaid text, "i'm there" don be son mishi magana a halin yanzu, Zaid yayi saurin kiran Nasiba, yace "ku fito yana waje" ta shaida mai da yanzu zasu fita. Ya tura ma Rafeeq da cewa "there are coming now, kindly greet the sick person please, Please Rafeeq, for me" tsaki ya buga Wannan Uncle Zaid din yana sani abun da ban yi niyya ba, takaici ya hana shi tsayuwa, ya koma motar shi ya Zauna" ba ayi minti Daya ba Nasiba ta fito rik'e da Nene, ta waiga ta waiga bata ga kowa ba, daga chan taga wata jan mota mai bakin Gilashi, da alamu ba kowa ciki, "to ina wanda Zaidun ya aiko?" "inaga bai karaso ba, mu koma daga ciki" duk wannan lek'e lek'en da sukeyi Rafeeq na kallon su, ganin zasu koma ciki ya sa shi yin horn, Nasiba ta juya inda taji horn, ta ga haske a ta cikin motar nan zuciyar ta ya bata, R-Lema ke cikin motar chan, ta tsinci kanta da murmushi ko ba komai zata samu ta shiga rayuwar shi, tace "Nene, ga motar chan" "wanchan mota kalar jini, ga bak'in windo shi kike nufin mu shiga?" cike da takaici tace "toh, ko Uncle Zaid din ne zai sa a cutar da mu?" da sauri tace "ni ba haka nace ba muje muje kar ki kaini gaba" su ka karasa har inda yayi parking, har yanzu be fito ba, Hannu ta sa ta bude k'ofar baya, Nene ta shiga da Sallama ita ma ta bita ta shiga ta rufo kofar, Nasiba ta kalleshi tace "ina wuni?" be amsa ba, shi dai ya tsinci kanshi da cewa "Ya jiki? Sannu da jiki" Nene ce da fara'arta tace "Naji sauki sosai" be sake magana ba ya ja motar, cikin nutuswa yake tuk'in shi, Nasiba na karantar duk wani abu da yakeyi, tausayin shi take ji sosai, ba tasan lokacin da hawaye suka soma zubo mata ba, tayi saurin sharewa don kar Nene ta gani ta tara mata mutane, be zarce ko ina ba sai Asibitin K-Dara, ya shiga yayi parking, shiru shiru be ce musu komai ba, Nasiba tace "Nene anzo fito mu shiga"suka fito, ga mamakin ta shima ya fito yayi gaba hanyar entrance din, suka bishi a baya, Nene na mata mitar "shi kuma wannan haka yake dunkum?" Seebi dai bata ce komai ba, Rafeeq ya tsaya ya yanki kati, ba layi, ya kira Dr Daran, yace "Baba gamu gaban Office dinka" yace to Rafeeq ku shigo, hannu kawai ya nuna ma Nasiba Office din ya samu guri ya zauna, Nasiba kuwa ta gane me yake nufi, ta sake rik'e Nene suka shiga cikin office din, yace kune Patient din Zaid? Nasiba tace "eh" ai ya kirani ya sanar dani zuwanku" ya shiga yi ma Nene tambayoyi, da gwajegwaje, kusan Minti 45, kafin yace " Inna Zamu baki daki, Hawan jinin ki ya tashi" Nasiba ta zaro ido tace "hawan jini Dr?" meyasa ta samu hawan jini? Yace "Ke kuwa ta tsufa, ai tsufa ce, don ma jikinta me kyau ne kuma tana regulating din shi,amma still zamu bata gado don kar ta kamu da Diabetes, don na fara ganin Symptoms din a tare da ita, kar ki daga hankalin ki, yanzu barin na muku processing gado, Suka fita waje da Dr din, Nasiba ta leleka bata ga Rafeeq ba, a ranta tace "ya ma yi kokari da ya kawo mu" Dr ya rubuta aka basu Gado, A ka kaisu har dakin, Nasiba na tunanin yanda zataje Gida kwaso kaya.
Rafeeq ya shiga Office din Dr, ashe Sallan Maghrib ya je yayi, ya ga basa nan, Dr yace "nayi admitting din su ne,suna room 12, HBP ne da ita, and a minor Diabetes, shine muke so ta samu rest, zan kira Zaid in sanar dashi don yace duk me ake ciki in kira shi, Rafeeq ya danyi gajeren tsaki yace " Me ake so?" Dr yace wannan taje ta dauko musu kayan bukatar su, don zasu kai 3-5days, payment kuma zan tura ma Zaid, Rafeeq yace "a ina zaayi?" yace a gun Cashier, Rafeeq be sake cewa komai ba ya fita, sai da yaje yayi payment kafin ya fita daga Asibitin, Jifatu yaje, ya siyo kayan Amfani, Su kayan Tea ne, fruits, karton din Ruwa, Bargo, Sallaya, da duk wani abun da yasan zasu buk'ata, Rafeeq shine da tsaywa siyan Kaza, ya koma Asibiti, Irin leburori yasa suka kwasan mai kayan, yayi gaba suna binshi a baya, har gaban dakin room 12, umarni ya musu da su shiga da kayan, shi kuma ya juya, daidai nan Nasiba tace Nene barin je in dauko kayan bukatar mu, don ba musan har yaushe zamu tsaya anan ba, Nene tace "toh akwai kudin Nape hannun ki?" eh akwai. Tana bude k'ofa ta gansu tsaitsaye da kaya nik'i nik'i, ta bude baki, sukayi sallama tace wannan kayan kuma fa daga ina? Suka ce wanchan ne yace mu shigo da su nan, Nasiba ta lek'a don tava wasu ke nufi, ga mamakin ta Rafeeq ne yana tafia da sauri, da sauri ta bi bayanshi, gudu gudu amma ta kasa cimma shi, daga nesa take ta kwada mai kira tana "R-Lema, R-Lema dan tsaya don Allah" shi kuwa yaji wannan kiran da ake mai, amma be tsaya juyowa balle ya ga ko waye, a tunanin shi irin mutanen nan ne da suke binshi a school, be juyo ba balle ya tsaya ya cigaba da tafian shi, ita kuwa bata fasa binshi ba, ba ta fasa kiran shi ba, bata damu da yanda ake kallon ta ba, "Rafeeq Please tsaya" wani tunani ya zo mata ta dan daga murya tace *"Hamma Rafeeq"* Chak ya tsaya, gaban shi ya yanke ya fadi, Muryan K'anwar shi yaji, a hankali ya furta "Rafee'ah?"...

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

*Sometimes, its hard for you to figure out what to write when you want to tell someone how much you Appreciate them, but it does'nt matter, i'll say it and write it anyhow. She's more of a Mentor, A Role Model, a Teacher, A Guide, A Respected, Loving and Caring Person, She's one who always wants to share, she's Determined and Confident, Her Support and Advice has helped lotta people, she has touched lives, ofcourse she's touched Mine and lotta people i know, She's Simply Amazing coz She's her, She's AUNTY SIS.*

*This page is for you Aunty Sis*

Pg3⃣7⃣

A hankali ya juyo, suna hada ido da Nasiba, yayi saurin dauke ido yana waige waige, kamar me neman wani abu, a hankali ta sake furta *"Hamma Rafeeq"* Mamaki ya lullube Rafeeq, tabbas ya san shi muryar Rafee'ah yaji, duniya ita kadai ke ce mishi Hamma, a ranshi yace *"to wannan kuma fa? Why is she sounding like my sister?"* a hankali Nasiba ta fara magana *"Mungode Sosai da wannan hidima da kayi damu, Allah shi saka da Alheri, Allah ya biya ka"* ta na kaiwa nan ta juya ta koma cikin Asibitin, shikuma yayi tsaye kamar an dasa shi, ya kasa motsi, shi beyi gaba ba, shi beyi baya ba, mamaki da tsoro ya kama shi, ya shiga tambayan kanshi, *"Meyasa wannan take magana kamar Rafee'ah, there's something about her, i just dont know how to describe it"* da kyar ya shiga mota ya bar Asibitin Jiki a Sanyaye.

Tunanin wannan dawainiyan da Rafeeq ya musu take tayi, komai ya tanadar musu, ashe yana da kirki? ashe Zuciyar shi bata ida macewa ba? Ashe yana da sauran kirki tattare dashi? Toh in ko haka ne, ba zai wuyar tankwaruwa ba, Allah ya bata saa Amin, ta kalli Nene tace *"Zaki ci Kaza?"* Nene ta kalle ta da mamaki tace *"bangane zanci kaza ba, naga dai don ni a ka kawo shi"* Seebi ta girgiza kai tace *"naga dai marasa lafia ba su fiye cin abinci ba, nama ma bai dame su ba"* harararta tayi tace *"ni ya dameni zubo min"* dariya sukayi gaba ki daya.

*Rafeeq* zaune yayi tagumi hannu bibiyu, ya lula duniyar tunani, shi fa be fiye tunani ba, amma tun da ya dawo daga Asibiti ya ke tunanin wannan yarinyar, mamaki yake mesa take abubuwa kamar Rafee'ah? Mesa take kiran shi da sunan da kanwarsa kadai ke kiransa da shi? Ko ta san fee'ah ne? Maganar ta komi na yana mai kama da na Fee'ah, haka kurum yaji a ransa yana son sake ganin ta.

*WasheGari*
Chapter 37 · 0% Book details