← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 95

Sashe 41

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miemee ta zungure ta, kina jin mu kuwa? Firgigit ta gyada kai, suna mamakin sabon haliayar Seebi, amma dai ba su ce komai ba, haka suka cigaba da lectures har karfe 2.
Da sauri suke tafia amma sun makaro, Buses sun tafi, sai sun jira dawowar su, Usheey, tace da muyi ta Wannan jiran, gwara mu taka bakin gate mu tare su a chan, kafin suzo nan duk mazan nan su shige su bar mu, kunga anyi ba'ayi ba" haka suka dauki hanyar gate suna fira jefijefi, banda Nasiba da ta lula duniyar tunani, kamar daga sama ta ji horn din motar shi, waswasi take anya kuwa shine? Miemee kuwa tuni ta fara gyara zaman rigarta, tana fadin "kunga wata Azababben mota na mana horn?" a tare suka juya ga motar, gaban Nasiba ya fadi ganin motar Rafeeq, bata son su Miemee su san halin da suke ciki, a dabar ce tace "kun ga dai kuzo mu wuce" Miemee tsce wlh idan ba ku shiga ni sai na shiga" Usheey tace "muje Seebi, ba mu san lokacin da za mu bar Makarantar nan ba, muje kawai" Miemee tace daga ganin wannan gayen Ya Azabtu, don ba kowa zaki ga an bar shi ya shigo da Tint makaranta ba, Allah kasa yace ya na sona" Seebi kawai sai taji daria ya zo mata, a ranta tace "Lallai Miemee, indai Rafeeq ne zaice yana sonki to zaki bushe". Usheey tace kun ga dai kuzo mu shige kafin ya chanza raayin shi, Miemee ce tayi gaba suna binta a baya, ta bude k'ofar gaba ta shiga, Seebi tayi murna da hakan fatan ta daya kar ya nuna ya santa, ita da Usheey suka shiga Baya, Waiyo Allah Miemee na ganinshi taji wani irin dadi, tana fari tace "Ina wuni" Usheey ma ta gaida shi, bece komai ba ya kunna motar shi ya bar wurin, suka bar makarantar suna tafia, Miemee ta sake cewa "sannu fa? Ya School?" nan ma ba amsa, daga baya Seebi ta rada ma Usheey a kunne kar ki sake magana, ta dinga zungurar Miemee ta baya don tayi shiru, amma Miemee Zak'al taki yin shiru, wai kai baka magana ne? K'iiii ya taka burkii, ya gangara k'asan titi yayi parking, tsaf Seebi ta gane me yake nufi, yana nufin su fitar mai a mota don Miemee ta dame shi, idan ya bar su a dajin nan ai be kyauta musu ba, Miemee da fi'ili tace "yadai motar ce ta lalace? A hankali yace "Get Out" da mamaki Miemee da Usheey sukace "What?" cikin dan daga murya yace "ku fita nace" a tsorace suka kalle shi, Usheey tace DonAllah BawanAllah kar ka aje mu nan, kaga nan ba inda zamu samu abun hawa, ka taimaka ka kai mu ciki gari, be ce komai ba, be kuma tada motar ba.

Ba tayi niyyar magana ba amma tasan hali nai, ba zai tafi ba har sai sun bar mai motan shi, daidai yanda zai jita tace "kayi hak'uri Hamma" ta mirror ya kalle ta, yayi dan guntun tsaki, ya kalli Miemee yace "kina da hayaniya" da sauri tace "yi hakuri, ba zan sake magana ba" ta bude murfin motar ta fita ta zagaya gun da Seebu ke zaune ta bude, "inshort Seebi koma gaba donAllah ke baki da hayaniya" Daria suka bata su duka, ta bude murfin motar ta fita ta koma gaba, ta na rufe wa kuwa ya ja motar shi ya bar gun, ba wanda ya sake magana har suka shigo cikin gari, a Royal Reataurant yayi parking ya fita, suka tsaya kallon kallo, ko cewa zaiyi su fito, yayi shigewar sa abin shi, Usheey ta tuntsire da daria Seebi ta taya ta, dariar da suke rik'ewa tun Batagarawa, Miemee ta hade girar sama da ta k'asa, sai da sukayi mai isar su, Usheey ta kalli Miemee tace "kina da hayaniya" Seebi ta sa daria, Miemee ta harare su tace its not funny wallahi, Wannan wani irin Guy ne? Kullum cikin k'unci, kun ga fuskar shi murtuk'e?amma fa hakan be hana kyawunshi fitowa fili ba" Seebi ta girgiza kai tace "kina da damuwa" duk suka fashe da daria, suna ganin ta fito duk suka yi shiru kamar sunga wani dodo, dauke yake da ledoji a hannu, ya bude motar ya ajiye wurin kafar Seebi, ya ja mota ya tafi, tafia sukeyi, shi be tambaye su inda zai aje su ba, Miemee ta rada ma Usheey ince mishi ya aje mu nan? Usheey tace baki daddara ba ko? To ba ruwana, duk suka ja baki sukayi shiru, mamaki ya cika Usheey da Miemee da suka gansu a Asibiti, to ko da ma ya san nan zasu zo? To waya gaya mai? Seebi ce ta fara bude motar kafin su Miemee, duk suka mai Godia, be ce komai ba, sauri sauri Seebi ta bar gun suna binta a baya, ya juya ya kalli ledar da ta bar mai a mota ya buga tsaki da k'arfi, ni ta bar ma Abinci?ni me zanyi dashi? Tsaki ya sake bugawa ya kwashi ledojin zai shiga Asibitin kenan ya ga Baba Maigadi, yayi mamaki amma be nuna mamakin sa ba, illa dauke kai da yayi dob be san tambayoyi, da sauri Baba maigadi ya karaso yace "Ahh Rafeeq me kazo yi a Asibiti? Nuna mai ledojin hannun shi kawai yayi, Au abinci ka kawo wa wasu? Ya gyada kai, yace "Nima wata makwabciyar mu nazo duba wa" da sauri Rafeeq yace "Nene?" da mamaki yace "eh ita" ko da yake ba abun mamaki bane tunda Nasiba ta san shi, amma dai Aminene ta ciri tuta tunda har Rafeeq zai zo dubata harda karin ciwo, Rafeeq yace "Baba ka kai musu wannan inji Uncle Zaid" "ya dawo ne?" tsaki Rafeeq yayi yace "baba ka amsa" da sauri ya amsa Rafeeq yace "daki na sha2" don kar ma ya sake sa shi magana ya juya ya tafi, shi ko Baba maigadi ya wuce cikin Asibitin.

Miemee da Usheey suka ma Nene Sallama, Seebi ta fito rakasu, a bakin k'ofa suka hadu da Baba Maigadi, ta gaida shi, tace "baba barin raka k'awaye na, yauwa 'yar baba je ki dawo ina nan" sai da ta rakasu bakin gate din Asibitin ta dawo, yana nan inda ta barshi, yace "ya jikin Aminene? tace "da sauk'i" yace "gashi inji mutumin ki Rafeeq, wai inji Zaid" ya mik'a mata ledar, ta bi ledojin da ido, ohh dama na su ne? Lallai Rafeeq a gaishe shi, tace "Yanzu muka rabu, be ce min namu bane" ai na mayi mamakin ganin shi anan, bayan abun da ya faru yau da safe a gida" da sauri tace "Baba Me ya faru yau?" Ya kwashe komai da ya faru tsakanin Rafeeq da Baban shi da su Aneesa, harda abunda Saude tace da martanin da Aneesa ta mayar, Nasiba ta tsorata, tace *"Baba kar suyi mishi wani mugun abu, Dole Rafeeq ya dage da Adduo'i, zan tambayi baba na ya rubuto min adduoin tsari"* Baba Maigadi yayi murmushi yace "lallai Nasiba, baki san waye Rafeeq ba, Yo Allah na tuba Sallah kadai Rafeeq keyi don ya zama dole yayi shi, to tsaya kiji, Rafeeq be Sallah a Massalaci baya jam'i, sai a daki, kuma da ya idar yake tashi, baya addua a ganin shi be da bukatar wani abu da zai rok'a, be da saurin jin dadi, shifa yanzu be k'i ace ya mutu ba, a takaice dai Rafeeq baya Addua" Nasiba ta fashe da wani irin kukan da bata san lokacin da ta fara shi ba, cikin kuka tace *"Waiyazubillahi, wani irin Masifa ce wannan? Wane irin mugun hali yake son jefa kanshi ? In banda abun shi wa ke cire rai daga rahamar Allah? Waye baya da bukkata gun Ubagijin shi?"* cikin Masifa da dacin rai kamar tana gaban shi tace *"R-Lema kana cikin 6ata Wallahi, kuma ko ka k'i ko ka so sai ka dawo hanya"*

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg4⃣0⃣

A tsorace ta dan kalleshi, ko bi ta kanta beyi ba ya hau titi kanshi a tsaye, Maimakon suyi hanyar Asibiti, sai bani tayi ya dauki hanyar *Sally's Cuisine* ba tace da shi komai ba har ya iso yayi parking, fita yayi ya shiga, nan ta samu damar amsa Wayar Usheey da tun da suja aje su take ta faman kiran ta, "Hello Seebi ina zai kaiki?" tayi daria tace "Asibiti" "haba har hankalin mu ya kwanta" tana ganin ya fito tayi saurin katse wayar, Hannun shu dauke da ledoji 4 ya aje mata 3, dayan kuma ya aje a seat din baya yaja mota sukayi Asibiti.

Ko da suka isa Asibtin, har ta bude murfin mota zata fita, Zuciyar ta ta bata shawara, ko bazai amsa ba, ki masa godiar dawainiyar da yake tayi daku, Abinci lunch da dinner baya fashin kawo muku, ga kai ki makaranta da dawo dake duk da ba kullum ba.

Ta juyo ta gyara zama yanda tana fuskantar sa tace *"Hamma Rafeeq, Yau Dr ke sa ran Sallamar mu, mun gode kwarai da dawainiyar da kakeyi da mu, Allah ya biya ka, Allah ya saka da Alheri ya, Allah ya ji kan Magabata, Albarkaci Rayuwar ka, Allah ya kuma Saka maka duk Zalincin da aka taba maka, wanda ba za ka iya yafe su ba"* tana kaiwa nan ta fice daga motar, bata tsaya sauraren abun da zai ce ba, Yanda kuka san Hoto, haka Rafeeq ke zaune a gun, ko yatsar shi ya kasa dagawa, be san lokacin da ya furta *"Ameen*" ba.
Haka kurum yaji dadin Adduointa, Shi be san meyasa ba, amma yana jinta a jikin shi, kawai yaji ya bata babban matsayi a ran shi, jinta kamar FEE'AH.
Chapter 41 · 0% Book details