← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 95

Sashe 66

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"You cant sleep with them you know?" Cewar Maalesh, "Why cant i?" inji Rafeeq, Daddy yacei "Aa Rafeeq gida zamu tafi, ga Nasiba nan she cant look after her" yace "She's not well too, itama she needs someone to look after her" "Aa Hamma i can, i'm fine ba abunda ke damuna" Rafeeq yace "Shuttup you are not fine" Zaid yace "IkonAllah" Rafeeq be sake magana ba ya zaro wayar shi daga Aljihu ya latsa waya, ringing biyu ta dauka cikin magagin Bacci "Hello Mom" Mom din Maalesh tace "Son ya akayi ne da daren nan?" "sorry na tadaki, Hajjo fah?" ta kalli Agogon gefen gadonta tace for goodness Sake Rafeeq shes Sleeping, baka duba agogon bane kafin ka kira, this is 12:15am, guntun tsaki yayi yace "sorry mom, but you need to wake her up, an sake kwantar da Neh-neh kla Asibiti Maalesh yanzu zaizo daukanta, thanks Mom Love you bye" be jira ta amsa ba ya kashe wayan tare da kallon Maalesh, Maalesh kaje ka dauko Hajjo, Dad Uncle Zai ku tafi gida, I'll be here har sai Hajjo tazo". Kamar Shine Babba duk sukace Okay Maalesh ya fara tafiya, Kafin su Daddy, dama Nene Already tana bacci. A waje Daddy ke cema Uncle Zaid Rafeeq ya damu sosai, damuwar da yayi kan Nene da Seebi ya ban Mamaki, Zaid yace "ba wani abu bane kawai dai ya girgiza da Gobaran nan, na san Mutuwar Rafee'ah ta dawo mai Sabuwa, ya zata zai sake wani rashin ne, don kasan Ya dauki Nasiba kamar 'yaruwarshi, kuma duk da ba sa shiri da Nene, yana sonta Sosai" Daddy ya jinjina kai. A lokacin Zaid ke ba Daddy labarin abun da ya faru tsakanin Saude da Nene, yace " tohh abunda ya faru kenan, dazun naga bakinta ya kumbura da na tambayeta sai cewa tayi a tayi da bango ashe da walakin goro a miya, ta san basu kyauta ba shiyasa bata gaya mim abun da ya faru ba, bakomai Nenen tayi daidia" sukayi daria.
*****
"Ya ki ke jin kanki yanzu, akwai abunda ke miki ciwo, ko yake damunki?" tayi murmushi tana mamakin wannan hali na Rafeeq, lokaci daya zai nuna damuwarshi kan abu, a wani lokacin kuma sai ya nuna shi be da damuwa ko kadan, kamar yanzu ne, yanda yake tambayar ta kamar ance sai ya tambayaeta dole, tace "Ba abunda ke damuna Kar ka damu" a takaice yace "ban damu ba" tayi murmushi tace "Liar, ka tabbata baka damu ba?" ya mata shiru, itama tayi shirun chan sai yace "Naje Kaduna" da sauri ta kalleshi, "da gaske kaje Kaduna?" be amsata ba yace "Anan yace in gaidaki, Murmushi me sauti tayi sannan ta fara hawayen farinciki, yace "Maminki na gaida ki, wai ku maida mata Babynta haka, she's missing her enough" dariyan farinciki ta fara tana Hamdala, tace " Thank you Hamma Rafeeq" a ranshi yace "meyasa take min Godia?" ta sake cewa "I'm proud of you" Murmushin gefen baki yayi ya tashi ya barta zaune ya koma chan kusa da Nene ya zauna, ko wannen su da sak'e sak'en da yakeyi.

Bayan kwana 3

Cikin 'yan kwanakin nan Uku, Nene ta tabbatar ita *'Yar Gata Ce* (Miemee Babe's Novel) don ko Zaid, Maalesh da Alhaji Habib na kyautata mata, Rafeeq ya rage zuwa Asibitin ya kanzo da daddare, Hajjo na kula da Nasiba da Nene.
Miemee da Usheey sunzo duba su Nene
Tun daren da akayi Gobarar Mak'ale ya kira uwar dakinshi ya sanar da ita ai ya cika aiki, ya cinna ma Gidan Nene wuta, Wutar da Suka kunna da Petir, Saude tayi daria tace "that Old witch, yanzu sai inga iskanci, dama Alkawari na miki cewa zaman katsina sai ta gagareki". Ko da safe sai da suka fita su 3 suka ga gidan Nene a k'one, murna kamar su zuva ruwa a k'asa su sha, Meema ta san aikin Saude ne banda Aneesa da tayi zaton Allah ne ya saka musu.

Zaid ya ji dadin Shiryawar Rafeeq da Maminshi, sai da yayi Azumin Godia ga Allah, dama Alwashi yaci na duk randa Rafeeq ya daidaita tsakanin shi da Maminshi, to zai jera kwana 5 yana Azumi don nuna jin dadinshi.
A safiyar Yau Nene ta sa Darun sai an Sallameta, Nasiba da Hajjo suna ta bata hakuri kan ta bari sai ta k'ara jin Sauk'i, ana haka sai ga Rafeeq da Daddy da Zaid sun shigo da Dr Umar, Yauwa Dafta, yau sai ka sallameni, Dr yace "dama Mama abun da nazo kawo miki kenan, takardar Sallama, tace "yo ni ai ko ba takardar Sallama tafiya ta zanyi" yayi daria yace "balle akwai ba" Alhaji Habib yayi daria yace "Ina kwana Nene? Ya karfin jiki" tace "Ahh Jiki garas ya kuke da iyalin?Rafeeq ya gyatsine fuska a ranshi yace "Neh-nehn nan no getam for kunya, wani Iyali kike tambayar shi? Wanda kika Lafta?" ya amsa mata, Suka gaisa da Zaid da su Nasiba, ta kurawa Rafeeq ido don jin ya gaisheta, ganin ta tsare shi da ido ne ya sashi cewa "Sannu Fah" "Ahau, dama wayace ana chanza wa tuwo suna? Me hali be barin halinshi" duk sukayi daria. Daddy yace "Toh Nene an Sallame ku, Gidanki kuma ba inda zaku fake, na dai sa an kwashe abubuwan da basu ci da wuta ba, sauran kuma an kauda su, ko kuna da inda zakuje ku zauna Kafin a gyara muku gidan?" tace "Muko ke da inda zamu, Kaduna zamu wuce, lokaci yayi da dai da zama zai kaini Bariki Garin Gwamna, Mahammadu bayanda beyi in koma chan ba, har ga Allah bansan garin, amma tunda dalili yasa, dole chan zamu tafi" Daddy ya jinjina kai yace "toh karatun Seebi fa?" tace wani karatu? Ta samu ta ceci rayuwarta da k'yar, ai Gun Iyayenta zan maidata" Nassiba ta bata rai, ai wallahi Nene ba zata datse mata karatu ba, zatayi Magana Zaid yace "Ai Nene tunda dai ta fara karatun a barta ta kammala, ai sun kusa fara Jarabawa, kuma in ta koma chan Abun zai shafi Karatun ta, kuma Semester ya ja da an kama mata hostel" Daddy yace "idan ba Matsala Nene ku na iya zama a gidana Kafin a gama gyara Gidan ku" a tare Rafeeq da Seebi sukace "What?" Daddy ya kallesu yace, eh, saboda kar ayi affecting karatunki" Zaid yace "this is a nice idea" Nene tace shin "Anya zaman mu a gidanka zaiyiwu kuwa?" Zaid yayi saurin cewa "me zai hana?" Rafeeq yace "this is a bad idea, Daddy please dont, dont make them live there, please, haba Daddy, do you want our house to turn to a battlefield? Do you have any idea what she did to Aunty Saude and Aneesa? Please that Dont" Nasiba ta kalleshi da mamaki, duk da ba taso su Zauna a gidansu Rafeeq, bata ji dadin yanda yake nuna beso su zauna da su ba, kamar yana k'yamarsu irin an hada su da kashi ko wani abu, Zaid ya wurga mai Harara Nene ta k'ulu sosai duk ds ba ji me yace ba ta san beyi naam da maganar babban shi ba, da bata yi niyyar zama a gidan ba, amma tunda Rafeeq ya kuskure yayi turanci, to sai sun zauna, sai dai ya hadiye zuciya ya mutu, tace "Toh Alhaji zamu zauna, Allah bamu zaman lafia" Amin ya fada cikin jin dadi, yace "da Office zanje amma mu tafi gidan, Rafeeq ka kai Hajjo Gida kace da Mom dinku mungode, Zaid ya ba hajjo 5k tayi godia, Hajjo ta bi bayan Rafeeq da tuni ya bar gurin don bacin rai, Zaid da Seebi suka bishi da ido me yayi zafi haka?.
*********
Fitowar Aneesa ke nan daga cikin gida zata bude mota ta tafi School taga Shigowar Motar Daddy da Uncle Zaid, ta tsaya tana kallon su har suka k'araso, ta nufi Motar Daddy ta Bude
"Daddy kayi mantuwa ne? Yace "Aa Aneesa" ganin Uncle Zaid ya bude booth yana fito da kaya ya sa ta kallonshi, "good Morning Uncle Zee, wadannan kayan fa?" yace "na bak'i ne" Kallon gilashin Motar tayi ta ga Nene zaune a bayan Mota, Wani ihu ta sa kamar mahaukaciya, bata bar ihun ba, Su Saude da Meemah suka fito sun zata wani abun ya sameta, "Anee baby me ya faru" ba ta bar ihun ba, sai dai tana nuna cikin motar da yatsa, Nene tace "Nunani kikeyi kinga dodanniyar cikin mafarkin ki ko?(your worst nightmare) to bari in fito ki ganni da kyau, Nene danAllah ki zauna kar ki fita, ina Nene bata ji rokon da Seebi keyi ba ta fita daga motar. Ai tuni cikin Saude da Meema ya duri ruwa, da sauri ta jufi Mijinta "Alhaji Me zan gani haka? Me sukeyi a gidan nan?" yace "Sunyi Gobara ne, zasu zauna a gidan nan har sai an gyara gidansu" da masifa tace wani Gidan? Ba dai wadannan ba wallahi, ko ni ko si" ran Daddy ya 6aci, yace "Sai dai ke ki bar musu gidan, don Wannan Gida na ne, kuma ina da damar kawo duk wanda na ga dama, a lokacin da nakeso, Nene ku mu shiga ciki" suka shige ciki duk suka bar su tsaye" Gaban Saude kamar ya bude don bugawa, yau ita Alhaji ke mayar ma magana? Yau ita take cewa ga yanda zaayi yana mata musu, har yana mata barazanar ta bar gidan? Ta shiga ukunta Lallai akwai Sakel,
Tana tunanin idan gidan su Nene ya k'one zasu koma k'auye su bar Katsina, su rabu da Family dinta, bata taba tunanin abu zai rikide ya koma mata haka ba, ai da ta sani da bata sa an k'ona gidansu ba, da ta sani tayi maganinsu ta wani hanya,
Tana tunanin ta yada k'wallon mangoro zata huta da k'uda, ta na gudu gara ta fada gidan Zago, wannan shine ta gudu bata tsira ba, gashi ta kwan a ciki, yanzu wa gari ya waya??
(Shin ya kuke ganin Zaman su Nene a gidan Lema).
.👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Chapter 66 · 0% Book details