← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 95

Sashe 79

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

nushi, Nene tace "Barawo ne ko dunkum? Ci Uwarshi Wallahi" Alhaji Habib daUncle Zaid suka karaso, "Rafeeq meye haka?" Rafeeq be bashi amsa ba Alhaji Habib ya hada ido da Mak'ale, baki na rawa Ya nuna shi da yatsa "me kakeyi anan?" Mak'ale ya kaima Rafeea Nushi, da sauri Rafeeq ya cikashi shi kuma ya zabura zai gudu, Nene ta hango dan gatarin da kwanaki taso ladabatar da dunkum a gefe da sauri ta dauko ta wurga ma Mak'ale, cikin saa ta sameshi a Bayan kai, Mak'ale ya zube a k'asa, Rafeeq na is gunshi kamar ance ya sa hannu a bayan wandon Makale, yana sawa kuwa sai ga Bindiga. ******* Baba Maigadi yazo da Igiyar Shanya, aka daure Mak'ale tsaf, Rafeeq ya shiga dukkanshi, Alhaji Habib ya kira jamian Tsaro, Rafeeq yayi tsaki yace "we dont have time for this, ya shak'o wuyan Mak'ale, "Uban me kakeyi a dakin Mamina 3/12/2014?" Mak'ale yayi shiru, tare da kawar da kai gefe" Daddy yace "ka bamu amsa kafin police suzo, sukazo ba zakaji da dadi ba" Mak'ale ya ki magana, Nene ta kwala mai wannan gatarin a taakiyar ka, tace kana magana ko sai na rotsa ka?" Mamakin tskhuwar nan yake, anya Mace ce kuwa, wani riko da ta mai dazu ya zata kattai suka kamashi. Akai akai mak'ale yayi magana yayi shiru, Zuciyya taci Rafeeq ya zaro bindigar Mak'ale ya nunashi da ita, yace "Iswear to God, ka fadamin me kake yi ranar a Dakin Mami na kuma waya saka ko in harbeka" a tsorace Zaid yace "Feeq, calmdown hand the gun over" Rafeeq yace "tell me or i shoot" Mak'ale yayi murmushi yace " You cannot shoot me Boy" "İ Am no Boy, i am Rafeeq Freeking Lema" Rafeeq ya saita kafar Mak'ale ya harba ji kake tasssss, İhu Nene ta sake, Mami da ke kitchen tayi salati tare da kashe gas ta sauko, Aneesa a kidime ta firo daga dakinta tayi kasa Gaban Saude ya yanke ya fadi, what the hell just happened? Gabanta na dukan chalugude ta lek'a window abunda idonta ya gane mata ne yasa ta sakin fitsari, shikenan "Asirinta ya tonu, ya zatayi? Mafitar ta daya, ta bar gidan kafin su ankara da ita, Crutches dinta ta hau dogarawa cikin sanda ta hau saukowa, inshaAllah kafin Mak'ale yayi wata magana ta bar gidan. Mami Ta tsure ganin Rafeeq yayi harbin, burinta taje ta kwace bindigar hannushi da yake sake kokarin harbin wani, Daddy ya janyeta ya rungume. Rafeeq ya saita zuciyar Makale "Dont underestimate me,Tell me now or i wont miss your Heart, start talking" cikin jin zafi da Azaba Mak'ale ya fara magana "Sauda ce, Sauda ce, itace ta sa mata magani a drink dinta tayi bacci, ni kuma na shigo dakin nayi acting kamar wani abu ya shiga tsakanin mu, itace ta sani, itace ta sani na kawo mata poison don ta sama yaran mijinta har macen ta mutu, itace ta sa na Kashe Hafiz Lema, itace ta sani na sa ma wani Gida wuta last 2months, itace..... "İnallilahi wa ina ilaihir rajiun kawai kakeji" kuka Mami, Aneesa, Uncle Zaid da Daddy keyi Sosai banda Rafeeq da idonshi ya k'ekashe, "Jaruban chan" cewar Nene. Cikin karaji Rafeeq yace "Saudeeeeee yau zan kasheki da hannuna" murya na rawa Aneesa tace "Yaya Rafeeq, Yaya Rafeeq, ga Saude chan, gata chan zata gudu" dum a tare suka kalli hanyar gate, ashe suna tsaye ta zo ta wuce ta gabansu, gashi har ta bar gidan, da gundulelen kafarta take cilla kafar da crutches tana tafia sauri sauri, Rafeeq ya danna a guje Mami na kwala mai kira ko waigiwa beyi ba, Mami tace Habibi ku tsaidashi kar yayi kisa donAllah, Zaid kuje, Daddy da Uncle Zaid suka bi Rafeeq a baya. Kuka takeyi tana dogara Sandarta tana tafia da sauri, daga gefe taga wani Me Keke Napep na fitsari hango makullan tayi jikin Napep din, da sauri ta k'arasa gun Keke Napep din ta shige, ta tada, tayi ribas ta bar gurin a Sittin, Me Napep ya ji Alamun an tada mai Abun Hawa da gudu ya zira wandon shi, kafin yayi aune sai gani yayi wata mata Me k'afa daya ta sace mai Machine" Jamaa ku taimakeni ta sacen a daidaita sahu" Rafeeq ya karaso ya shiga halbin tayar Napep dinnan amma ina be sameta ba, ya harbi iska da hannunshi, dan Achaba ya tsaida, shima ya janye shi ya wurgar dashi a kasa ya hau kan Machine din ya burka ya bi bayan Saude Mai Keke Napep.(Lols)
Chapter 79 · 0% Book details