← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 95

Sashe 25

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Rafee'ah ta rada ta inda zata bullo ma Rafeeq, don har yanzu bata san damuwar shi ba, da ta matsa ma Zaid sai ya gaya mata, sai yace mata "zaifi kyau ki taya shi da addua, Shi kadai yake bukata, kar ki tsananta Bincike you might end up hurting yourself" haka Rafee'ah ta cigaba da shishige ma Yayan ta ko zata samu ya dawo yanda yake a da, amma shiru ba cigaba, haka zata karashe surutun ta ta barshi, duk yanda yake so ya dan dinga kula Kanwar tasa hakan ya faskara, abun ya zame mishi jiki, Yanzu magana ya zame mishi wani gagarumin Aiki, da Zaid kadai zakaji yana magana, shima be wuce ya bishi da kalma biyu ko uku ba, abun Rafeeq ya wuce Miskilanci, don abun yayi k'amari har ace be iya shiga cikin Gidansu ya ci Abincin da Matar Uban shi ta dafa, kai ko daki aka biyo shi dashi be ci haka zai bar musu shi inda suka aje mishi shi, Be cin abincin Gidan su kwata kwata, sai dai yaje gun me indomie ya sha shayi, da Zaid ya lura da hakan sai ya siyo mishi Cupcakes,Biscuits Shortbread da Drinks kalakala ya ajiye mai a daki tunda yana ganin asaran cin Abincin Gidan su..

Da kyar Maalesh ya sa shi shirin Makaranta, ba don yaso ba, sai dai kawai baya so su tsaya gardama da Maalesh, ya shirya suka wuce School, tunda suka isa Sciences aka zagaye motar Maalesh, Maza da Mata kasancewar R-Lema na kowa ne, Maalesh yace "Guy, dole ka fa sake fuska, mutanen ka na jiran fitowar ka" be kula Maalesh ba sai ma dauko wani Bakin Gilashi irin no respect din nan ya k'wama a fuskar shi, ya bude Kofa ya fita, ji kake ana R-Lema, ko kallo basu ishe shi ba, tafian shi kawai yakeyi, burin shi ya ganshi a Class, duk suka bishi da kallo suna mamakin wanna Shariya na R-Lema, sai duk suka maida kallo ga Maalesh, Maalesh ya shiga raba idanu kamar yayi K'arya, da k'yar yace "kuyi hakuri, R-Lema na da dan damuwa ne, ky tayashi da Addua". Mutanen kam suka jinjina kai, da alamu kam, don ba haka suka saba ganin shi ba, shi mutum ne mai son jamaa, da da ne, da ya fito zai dinga ba mutanen nan hannu suna gaisawa, ya dinga jan tsokanan yan matan nan, ana wasa ana daria, lallai dole suke tayashi da addua Allah ya yaye mishi damuwar shi.

Ai ba Daliban ba, harta Mallamai sun san da Chanjawan R-Lema, yanda kasan hoto haka yake zaune a aji, ba motsi, ba kamar da ba, kafin Lecturer ya gama tambaya har ya bada amsa, amma yanzu ko sun tambaye shi shiru zakaji yayi, bawai be gane abun da ake koyar dashi bane, tsaf yake fahimta kamar kullum, abunda yake ganin asara shine ya bude baki yayi magana ko ya bada amsa, yana jin kuiwar magana, kwanaki da ya ba wani Lecturer haushi koran shi yayi a aji, don ya dinga mishi magana jo tak Rafeeq be ce mar ba, abun ya ba mutumin haushi ya kore shi, sai da Maalesh ya je ya sanar da Level Coordinator dinsu, kasancewar Coordinator abokin Zaid ne, Yazo ya bada hakuri, yace yayi hakuri Rafeeq is Mentally Sick, yayi considering dinshi tunda kowa yasan ba haka yake a da ba. Da haka aka rufe bakin lecturers, ko sunzo ba sa tambayan Rafeeq don sun san ba tanka su zaiyi ba.

Duk nacin da Yanmatan Rafeeq keyi don ya kulasu haka suka gaji suka hakura, don ko sun fi k'uda k'wak'wa iskar da ya debo su Rafeeq be kallo, Cafteria da da ya maida shi Gidan Uba, a rana sai yaje so nawa, yaje ya siya ma yanmata abinci, yanzu kuwa ko kallon hanyan beyi, in ka ganshi cikin Makaranta yana aji, da sun gama lectures be kara ko minti zai bar ajin don be son surutu, Chan bayan Labs inda ba ka ganin kowa yake zuwa ya zauna shi kadai. Haka Rayuwar shi ta cigaba da tafia..

Duk Yanda taso ta kebe ya je gun bokan ta Alhaji Habib ya toshe, be bata damar zuwa ko nan da chan ba, ko ina zaije da ita yake zuwa, be barin ta ita kadai, ta rasa yanda zatayi, haka dai ta hakura har suka karaci kwanakin su a garin Kano.

Bayan Sati Uku
Sauda ta kalli Boka cikin kunan rai tace "ya zaka ce min hakan ba zaiyiwu ba? Meye ba zaiyiwu ba? Kaine fa kake share min hawaye na, kai ke biya min buk'atu na"(Waiyazubillah, ya mu Mata, mu kula, mu lura, aikin Boka na tasiri ne da Yardar Ubangiji, Boka be Isa Ya biya mana Bukattun mu ba. Allah sa mu dace). Ta yaya zan ce maka ga abun da nake so kace min ba zaiyuwu ba? Kasan taya na bar Katsina na zo nan? Ni yanda nake so haka zaayi, Kawai Rafeeq nake so ya fyade kanwarsa". Boka yace "Saude kar fa ki manta, duk aikin da kike samu muna miki shi yanda kika buk'ace shi, tunda kikaji nace wannan bazaiyuwu ba toh ki hakura da wannan, amma na riga na biya miki dayan bukatar hana Yaron Gama Makaranta" Sauda ta katse shi ta hanyar cewa "yo ni raba ni da wata makaranta, yo ya gama ina ruwana, ni buk'ata ta shine Alhaji ya tsine musu duka, kai ni ban k'i su mutu ba" Boka yace "Ke Saude saurareni kiji, jijsan aiki na kamar yankan wuk'a yake, ba wanda ya kaini aiki me kyau, na hango miki gaba ne, duk wanda zai ce miki ki bashi kudi ya miki Aiki kan Mijinki akan 'ya'yansa, to nayi imani kudinki kawai zasu ci, ba wani mugu a doren k'asar nan da zai iya hada Mijinki da Yaransa ba, wai shin baki san so da ke tsakanin d'a da mahaifi ba? Kar ki ga kinci nasara kan Matar shi, kice suma zaki ci nasara, Saude shawara zan baki, idan kika matsa kan hakan, to Asirin ki na Gaf da tonuwa..

Sauda ta k'ule matuka, ta mik'e cike da Masifa, tace" kai na kan tudu, kar ka cika ni da wannan soki burutsun, ai baka gaya min Imani ya fara shigan ka ba, idan ka tsufa baka iya biya min buk'ata ta sai ka sanar dani, bawai ka dinga ce min hakan bazaiyiu ba? Ba ka k'ara gani na nan, zanje in samo wanda zai iya min abun da nake so" ba ta jira amsar shi ba ta fice daga Bukkar.

Cikin Kwanaki 20 Saude ta zabure sosai, duk inda ta san zata samu bokaye ta bi, burinta Rafeeq ya lalata ma Rafee'ah Rayuwa, sun san aikin da ta ke so a mata ba me yiwuwa bane amma sunk'i gaya mata sai dai su ce mata taje Gida zata ga aiki da cikawa, haka zata dawo gida tayi ta jiran tsammani, shiru takeji, sai ma wani Gatan da Alhaji yake k'ara ma yaran sa, haka zata chanxa wani boka, Bokaye kuwa sai cin kudinta suke yi, da ta gano su dai tayi watsi da dukkan su ta zauna gaban Madubi ta na kallon kanta tace "Haba Saude, sai kace ba mace ba, idan Plan A yak'i ci, sai a gwada Plan B, Wato K'issa" ba Bokan da zai k'ara cin kudina, cikin ruwan Sanyi zanyi maganin ku Rafeeq da Rafee'ah..

Bayan Wata Daya

Karatu suke kain da nain, Rafeeq ya dage da Project dinshi, be kula kowa yake abubuwan shi, kwanaki kadan ya rage su fara Final Exams, Rafee'ah har ta saba da Shariyar Rafeeq, itama tana ta karatun ta cikin kwanciyar Hankali, Babban Tashin hankalin ta Mamin ta, ta fara gano akwai wata makarkashiya, duk wanda ta tara da maganar mahaifiyar ta sai yayi shiru, har takanas taje gidan Kakanin ta don tambayo idan Mahaifiyar ta take, amma bata samu amsa daya k'wak'wara ba, sai hanya hanya suke mata.

Yau tace InshaAllah dole sai ta gano gaskiar inda Mahaifiyar ta take, Bayan ta dawo School ta nufa dakin Aunty Saude, ta tura kofar da Sallama, Sauda daga ciki tana waya da Meema da Aneesa tayi saurin latse wayar tana addua Allah ya sa Rafee'ah bata ji me take fada ba. Ta amsa mata sallamarta, "Rafee'ah sannu da zuwa kin dawo?" "eh Aunty ya Gida?, kina da lokaci? Akwai maganan da nake so muyi" Sauda tace ohh Rafee'ah, barin yi Sallah sai inzo muyi magana ko? Rafee'ah tace toh, nima barin shiga in watsa ruwa".
Chapter 25 · 0% Book details