Sashe 31
Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Zaid ya Zare kamar zautattace, don yana kaunar Matarshi fiye da tunani, yana tausayin su shi da diyar shi Rafee'ah-Ayman, Rafeeq da Baban shi da Maalesh sunzo janaizar, sun sauka masauki, Meema ji take yau Sallah a gunta don ba karamin farinciki mutuwar matar Zaid tayi ba.
Kwana 3suka tafi, banda Rafeeq da yace shi zai tsaya da Zaid don yasan yana bukatar shi, kamar Lokacin suna, Mami bata bari sun ganta ba, sai Bayan da suka tafi ta dawo gidan Zaid tana kula da diyar shi.
Rafeeq ya fito daga mota ya shiga gidan Uncle Zaid, Kai tsaye yayi Parlor, Tsaye ya ga Fuskar da ba zai taba mancewa ba, Fuskar Mahaifiyar shi, tsaye take rungume da jaririya, Jikin Rafeeq ya hau kyarma, idon shi ya rufe da sauri ya je ya fizge Rafeeah-Ayman, daga hannun ta, ya rungume ta, Zaid ya mik'e da sauri yace "Rafeeq" yace "me wannan Matar takeyi a gidan nan? Har ta ke taba min k'anwa? Zaid ya sausauta murya yace "Shes been here for a while" Rafeeq cikin bacin rai yace "and you never bothered to tell me? Zaid yace" coz u never asked, u never wanted to talk about her" Idan har kana so ka kara ganin kafana a gidan ka, This woman has to leave, bana so in sake ganinta, kar kuma ki sake daukar min kanwa don kar ta koyi baki da mugun halinta" Zaid ya kaura mai Mari, ya nuna shi da yatsa" I wont let you disrespect your mother" Baby ta fashe da kuka, Rafeeq ya rungumeta, be damu da marin da ya sha ba yace "yi shiru kinji fee'ah, zan samo miki me raino, mace mai mutunci ba kamar wasu matan ba" Zaid yayi saurin kwace diyar shi daga hannun Rafeeq, yace "bata da wata mai raino da ya wuce Mami, ba ta da Uwa da ta wuce Mami, itace Uwarta, duk me zakayi kayi" Rafeeq ya kalli Mami da fuskarta yayi jazir saboda kuka yace "Ba zaka sake gani na a gidan ka ba" ya fita a fusace, Mami ta bishi da gudu tana "Rafeeq, ko kallonta beyi ba" Zaid ka bishi kar ya dauki hanyar Katsina yanzu, kar wani abu ya same shi" haka Zaid ya bishi a hanya, ya dinga lallashi, da yake Rafeeq din be iya fushi da Zaid, nan da nan ya sauko amma dole ya bar Kaduna a ranar ya wuce Katsina a ganin shi zaman shi be da amfani.
Bayan Shekara Daya (A gurguje)
Abubuwa da dama sun faru a shekarar da ta gabata, Kamar yanda Sauda ta sha k'okarin Kashe Rafeeq ta hanya da dama bata samu nasara ba, har ta hakura ta barshi na wani lokaci, kila yayi amfani, Daga abubuwan da suka faru, ciki kuwa har da Spilling din da Rafeeq yayi a Makaranta, an rasa gane dalilin spilling dinshi, don an binciko takardun shi an ga Yayi passing, an rasa ta ina aka samu tangardan(Ni dai nace Boka na kan tudu), Rafeeq kuwa ko a jikin shi, dama da Uncle Zaid ya koma karatu last year, amma yanzu ko sama zata hade da kasa ba me sashi komawa School, Su Maalesh sun fata bautar kasa.Zaid yayi Mamaki matuka, dole kenan sai ya sake dawowa? Matsalar shi daya yanda zaiyi convincing Rafeeq ya sake wasting shekara daya, Sai da Zaid ya hada da kuka kafin Rafeeq ya amince da zai sake dawowa, da sharadin idan ya sake failing ba shi ba boko har abada, Zaid yayi saurin Amincewa da hakan, a ganin shi Wannan karon akwai nasara.
A wannan karon ne Seebin Nene suka Shiga Jamiar Umaru Musa Yaradua.
*Wacece Alheri?*
Ta yaya ta zama Alheri?
*Shin Sauda zata cigaba da Samun Nasara a duk abunda ta sa gaba?*
*Rafeeq na tava dawowa daidai kuwa?*
Da tambayoyi da dama da kuke son amsoshin su, ku biyoni sannu a hankali.
***********
CIGABAN LABARIN.
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
3⃣3⃣
Wannan Pagen Naki ne *Aunty Sady Yar Mutanen Jegal*, Nagode Da Kaunar da kike nuna min, Allah ya bar Zumunci Amin😘😘.
*UMYU Katsina*
Kallon wurin da ta ci karo da R-Lema take tayi da suka zo wucewa ita da su Miemee, kamar ance ta waiga ta ganshi Zaune kan dakali, ba Waya, ba littafi ba komai da ke taya shi hira, shi kadai tal, Miemee tace "Lahh, ku kalli Azababben gayen nan na rannan, Usheey ta kallo shi, Seebi dama shi take kallon, Miemee tace " Wallahi sai naje mun gaisa" Nasiba tace "Uhm uhm Miemee ina jiye miki Wulak'anci" Miemee tace "haba Seebi ba kalar mu bane a ke Wulakanta wa, just watch me" ta gyara zaman rigar ta tana karairaya ta nufi R-Lema. Kusa dashi ta zauna tana cewa "Sannu fah" kallo daya ya mata ya dauke kai, Miemee bata damu ba tace na ga kai kadai ke zaune, its seems you are lonely, shiyasa nace barin zo in taya ka fira. Rafeeq ya tashi tsaye ya bar mata gurin a ranshi kuwa cewa yayi "wannan ta cika hayaniya" Me Nasiba da Usheey zasuyi? In banda Daria. Miemee ta k'ulle iyakar k'ullewa, tace to meye abun daria, cewa yayi yana da lecturers, Nasiba tace "kaii Miemee, muna fa kallonku, ko A be ce miki ba" Usheey ta kara tuntsirewa da daria, Miemee da haushi ya kamata ta harare su tace "to sai me?" tayi gaba, suna daria suna binta a baya don abun ya basu laugh.
*Malali Kaduna*
"Waalaikum Salam" Ummi ta amsa Sallamar da taji daga waje tare da fitowa, "Ahhh Mamin Ayman ce da Ayman? Sannun ku da zuwa" da sauri ta koma ciki ta ciro tabarma. Mami dake dauke da Ayman a hannu kuwa tana ta murmushi, Ummi ta fito ta Shimfida tabarma tare da umurtan Mami ta zauna, suka gaisa. Mami tace "wato Ummin Anan, na ganeki, bakya son shiga gurina ko? Gashi Allah ya riga da ya hadamu, ko Anan ba kya turomin yazo tayamu fira, ko ba ki san Hak'k'in Mak'otaka bane? Ummi tayi Murmushi tace " Wallahi ba haka bane, abubuwan ne sai a hankali, kiyi hakuri zamu dinga shigowa" kafin su k'ara magana Wayar Ummi dake kan window tayi ringing, Ummi ta mik'e ta dauko wayar, Seebin Nene ta gani a jikin Screen din, ta dauka da Sallama, daga chan aka amsa, Ummi ina wuni? Ya gida da kowa da kowa? Lafiya Alhamdulilah, ya karatun ki? Muna tayi Alhamdulilah, toh Allah ya bada sa'a, ina Anan?yaje Islamia, ina Nenen? gata nan, Nene ta amsa wayar da cewa "Halo, Dije, ince dai kuna lafiya? "Lafiya lau Nene" Ina Mahammadu? tace "ya fita" Nene tace "to kice mai jiya kiris ya rage muyi gobara, wannan abun chanza layi yayi ta k'auri, ni kadai cikin Gida kamar Mayya, lokacin Nasiba na Makaranta, ina ta bacci kawai naji abu na k'auri, da kunji sak'on mutuwa ta, ko da ka fito wajei neman taimako sai da na share kusan minti 30 waje banga ko akuya yazo wucewa ba, sai ga Zaidu bawan Allah har da mai gyara ya kawon, Na dade ina gaya ma Mahamadu bani son unguwar nan, ba mutane, wai sai yace "Haka Unguwan yan gayu suke" yo ni ina ruwana da wata Unguwan Gayu? Yanzu da ba dan Zaidu bawan Allah ba, da gidan nan ya kone kurmus" Ummi tace "SubhanAllah, Allah shi kyauta gaba ya kuma kare" Nene ta cigaba da mitar ta "daidai da burodi idan zaka saya sai ka taka har bakin titi, k'osai kuwa sai kin ci uwar tafia zaki ga mai k'osai, ni na saba Unguwar mu ta da, duk lungu da sako akwai mai k'osai, ko tari nayi zaa jini a Mak'ota, nidai gaskia ba zan iya ba, a maidani cikin Mutane, ba na son Unguwar nan na masu k'arya". Ummi ta karai da murya tace Nene kiyi hak'uri zan sanar dashi InshaAllah, za'a samu Mafita". Nene cikin tsegumi tace "Ai gwara a samu Mafitan, kuma kice--" Nasiba tayi saurin kwace wayar tace "Laahh, Katin sun K'are" tayi hakan ne don ta san Nenen ta da mita, idan ta kama zance bata san ta tsaya ba, ko bari batayi sun gaisa da Umminta ba da kyau, aiko zata sake kiranta da ta k'ebe.
Ummi ta kalli Mami tace " hakuri Mamin Ayman, ina magana da surukuwa tace, Mami da ta gama jin Zancen Ummi na waya, kasancewar Wayar China Phone ce. Mami tace " Bakomai, najita akwai barkwanci, wani gari take ne? Ummi tace tana Katsina, diyata na chan tare da ita, tana karatu a Jamiar Garin. Mami taji faduwar Gaba don duk yanda taji an ambaci Katsina sai ta jita wani iri, balle wannan da taji wani bak'on almari na ziyarta tace "Allahu, Ayman zo mu tafi Gida" Ayman da ke ta wasa ta gunguro gun Maminta Ummi ta musu Rakiya har bakin kofa.
Bayan Wau 'yan kwanaki.
*Katsina*