← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 95

Sashe 32

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zaid ya shigo Unguwar su Alhaji Habib Lema da misalin k'arfe 3:30pm, yana tuk'in shi cikin kwanciyar hankali Daidai Gidan Nene ya tsaya ya parka Motar shi, bari ya shiga ya gaida Nene, ya fita ya shiga Soron Gidan da Sallama a bakin sa, "Assalam Alaikum" Wata siririyar murya yaji ta amsa mai Sallamar shi, Hijabi ta jawo kan igiyar shanya, tana me mamakin yau waye a gidan su? Lek'awa tayi ganin Zaid tayi tsaye ya, shima kallon ta yakeyi, ji takeyi kamar ta sanshi wani gurin, shikuma kallo daya ya mata ya gane ta, itace ya taba lift ita da kawayenta kwanaki, Sansayar Murmushi ya mata yace Seebi? Da sauri tace Ina wuni? Ya amsa mata, cikin wasa yace "Me kikeyi a gidan Kakata?" ta zaro ido cikin sanyinta tace "Nenen ce Kakar ka?" Dariya yayi yace "ehmana" daga ciki Nene ta fito, Nasiba ke da waye ke ta dumi a waje? Cikin murna tace "Lahhh, ga Zaidu bawan Allah" da sauri ta rik'o hannun shi har cikin Gida, tace da Nasiba "ke dauko Tabarma ko darduma" da sauri ta dauko ta shimfida mai, "Zaidu Sannu da Zuwa, kazo lafiya?" Nasiba dai ta bisu da kallo, tana ta kallon ikon Allah yanda Zaid da Nene suke ta labartawa, "Nasiba baki san shi ba ko?" ai Shine Zaidu bawan Allahn da bakina ya kasa daina ambaton shi, wanda ya taimaka mana randa muka kusa Gobara, Nasiba tayi murmushi tace "Allah Sarki, Nene ta bani labarin abun da ya faru, Mungode da taimakon da ka mana, Allah ya saka maka da Alheri" har ranshi yaji dadin adduarta gareshi, yace ai Seebi mun taba haduwa kece dai ba ki gane ni ba" tace "ni? A ina?" yace wata rana ba a wuce Sati 2 ba, na dauko daga wajen Umaru Musa, na a je kawarku wurin Motel, ku biyu kuma kukace in sauke ku a Salamah, kin tuna? Nasiba ta zaro ido, Tabbas kaine, na tuna, dama nima ina ta tunanin inda na sanka, nan fira ya barke, idan kaga Nasiba, Zaid, da Nene na fira sai ka rantse sun dade da sanin juna, Nasibar da ta ke da wuyar sabo, bata da saurin sabo, sai gashi nan da nan taji ta sake da Zaid, haka kurum taji Zaid ya samu gurbi babba a zuciyar ta. Sai da Zaid yaci Burabiskon Da Nene tayi kafin ya musu Sallama ya wuce Gidan Yayan shi.

"Assalam Alaikum" bakin shi kadai ya kalla ya san ya amsa Sallamar, da ka kalleshi ka san yaji dadin ganin Zaid, amma ya kasa nunawa, Zaid dai ya Zauna, yace "R-Lema" da k'yar Rafeeq yace "Sannu da Zuwa?"" yauwa Rafeeq ya kake? Ya skul? Sai da ya dauke shi Seconds kafin yace "Alhamdulilah" "Kaci abinci?" kai kawai ya daga mai tare da nuna mai Ledan take away din da yayi a Crispy. Zaid ya jinjina kai yace "akwai wata matsala? Ko akwai abunda kake so?" Rafeeq ya girgiza kai alamun aa, Zaid ya mik'e tare da dafa Rafeeq yace "Good" bari in k'arasa cikin Gidan isowa ta kenan, Rafeeq bece komai ba, har sai da Zaid ya kusa barin dakin ya cire baki yace "Ya Rafeeah-Ayman? Zaid ya juyo da murmushi yace "Shes fine, tana Gaida Yayan ta" Murmushin gefen kumatu Rafeeq yayi, ya dauke duban shi daga Zaid don kar ya mishi wata magana da zai bata mai rai (kun dai san Maganar ko? Maganar Mami).

Meema na ganin Zaid da zuro a guje zata rungume shi, da sauri Zaid ya ja gefe yace lafia? Cikin kissa tace "Uncle Zee, naji dadin ganin ka ne, nayi ta kiranka ba ka dauka ba, na Kuma kace mana zaka zo ba, da kyar yace "i was driving" ya yi saurin hayewa Sama don ya k'i jinin Meema, wani irin warin Man bleaching da gashin doki takey tayi. Meema taje ta barbade jikin ta da turaren da boka ya bata, wanda yace "idan har Zaid ya shak'i kamshin, to sai yanda tayi da shi, Zaid juwa ya shiga ya gauda Yayan shi, Sauda na zaune tace " a kawo maka abinci?" ya danyi murmushin yak'e yace "aa Nagode" ta kalli Mijinya cikin Kissa tace "ka ganshi nan Alhaji, ni bansan me na mishi ba be cin abincina, be taba ci ba, haka zai kamo hanya tunda daga Kaduna, amma ko ruwan Gidanka be sha" Zaid ya dan wayance yace "Wallahi sai na cika ciki na kafin nake k'arasowa nan" Alhaji Habib dai ya murmusa yace "kun fi kusa" yauwa Zaid, ya karatun Rafeeq? Kasan idan be ci Exams din nan ba Spilling na 3kenan zaiyi ko?Mates dinshi daga masu Service sai masu Aiki" Zaid yace " Yaya, Rafeeq zaici Exams dinnan da yardan Ubangiji, this is his last year a School, just have faith" Alhaji Habib yace "Allah shi yarda" Sauda a ranta tace "sai mu gani" Zaid ya musu Sallama ya sauko k'asa.
Meema na ganinshi ta k'araso, Da sauri Zaid ya toshe hancin shi saboda wani irin warin tashina hankali da ya ziyarcin hancin shi, Meema meye ke wari haka kamar Jab'a?" tace "Jaba kuma?" Zaid yace "sai anjima idan na tsaya a nan Kaina zai min ciwo" da sauri ya bar gurin takaici ya hana Meema bincshi, wai ita ke warin Jab'ar ko turaren? Ta fashe da wani kuka mai tsuma rai.

*UMYU KATSINA*

Jugum jugum sukayi suna neman mafita, Awan su 3 a Library, suna neman yanda zasu yi Solving wannan Assignment dinsu na Calculus, gashi 5 ta wuce, gashi da Sassafe karfe 8 zaayi Individual Submission a Office din Course tutor, kuma yace idan suka kwafa na juna zai gane, Ana tsoron Malamin da Course dinshi kasancewar dangin Maths ne, ana samun Carry Over da yawa, hankalin daliban da keyi a tashe, ko wannen su ya dage yana iyakar k'ok'arin shi, gashi 5 har ta wuce, ba yanda Miemee Usheey da Seebi zasuyi illa su wuce Gida don Maghrib ta k'arato, Miemee tace zata ba lesson teacher din k'annenta ya mata Solving, Usheey kuma tace " Zata duba cikin Note book din brother dinta shima yayi Course din lastyear, idan Allah ya sota ta samu, Nasiba da idon ta ya ciko ruwa ta kasa magana, don bata da wata mafita, ta tsani CarryOver amma ta sadakas ta fadi course dinnan, dole sai ya dawo mata Next Year. haka suka wuce Gida.

K'arfe 7 Zaid ya Shigo Gidan, tunda ta gaishe shi bata sake magana ba ta cigaba da Kallon Takardanta kamar ansa zai fito, Zaid ya zauna kusa da Nene, yace "yau Seebi boko ake ta sha? Yau ba a ma Nene Fira?" Nene tace rabu da ita 'yar nema, ka ganta nan tun dazun nake ta magana ta min banza, tunda ta dawo take ta rubuce rubuce tana yaga takarda, ko abincin kirki ta kasa ci, shine kagan mu zugum zugum kamar kurma, ina ta Addua Allah ya kawo mun kai. Yayu daria, yace "Seebi Assignment ne halan?" tace "Wallahi Uncle Zaid, part of our CA test ne, kuma ban iya ba, tun dazun nake ta solving amma na kasa, yace "mugani" da sauri ta mik'a mai ya bude baki "lalala, Calculus, tabdi, ai ko lokacin da mukayi Calculus da k'yar nayi passing course din yanzu ko ko kasheni zaayi ba zan iya cewa ga yanda akeyi ba" hawayen da take makalewa suka gangaro, Zaid kadai ne hope dinta, gashi shima be iya ba, Zaid ya lura da yanayin da ta shiga yace "yaushe zaayi Submitting? ta fashe da kuka, Zaid ya rude yace " Calm down ki kin magana" tace "Gobe da Sassafe before 8, kuma individualy yace don zai gane idan mun kwafa daga junan mu".
Zaid yayi shiru for sometime, wani tunani yazo mai, amma yana gudun abunda zai faru, amma kuma dole ya taimaki Nasiba don tana bukatar taimako shikuma yana da halin taimaka mata, ba tare da tunanin me zai faru ba ya ciro wayar shi ya latso Numbern Rafeeq.

Kamar ba zai daga wayan ba ya dauka ba tare da cewa komai ba, Zaid yace " Hello Son" chan k'asa Rafeeq yace "Yeah" yace "kana Ina?" da kyar yace "gani nan zanje gidan su Maalesh" "donAllah i need your help" Rafeeq yayi saurin cewa "Menene are you ok?"don yaji Uncle sounds so serious, Zaid yace "i'm fine, i need you to come back, daidai kwanar Gida kafin kaje Salamah, Please" be bari yace komai ba ya kashe wayar shi ya na rok'on Allah ya sa yazo" Nasiba ta tsare shi da idanuwa, yace "Nephew dina ne, ina ganin Zai iya miki Solving problem dinki" Dadi ya lullube Nasiba, Mintuna 45 suka shude, ba Rafeeq ba alamun shi, Nasiba ta damu kwarai, Zaid kuwa ya cire rai da zuwan Rafeeq, don har yace ta miko mai ya gani yayi trying solving din. Kirrrrrr Wayar Zaid tayi Ringing, da sauri ya dauka ganin Rafeeq, "Hello" Chan k'asa yace "Nazo kwatacen" da sauri Zaid ya zura takalma yace gani nan fitowa.
Chapter 32 · 0% Book details