← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 95

Sashe 39

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajjo Ta ishe shi da surutu cikin mota, idan ya tanka to wanda ba sa wurin sun tanka, yayi shiru ya maida hankalin shi kan tuk'in sa, har suka iso Asibitin, ya ciro paper da biro yayi rubutu, ya mik'a ma Hajjo, yace *"ki basu, Daki na Goma Sha Biyu"* Hajjo ta san halin shi sai kawai ta kwashi kayanta ta shiga cikin Asibitn, da tambaya aka nuna mata dakin su Nene, ta shiga da Sallama Seebi ta amsa mata tare da gaida ta, ta amsa mata, Nene ta dago tana Kallonta, ta mata ya jiki, da ta lura suna mata kallon rashin sani sai ta ciro takardar da Rafeeq ya bata ta mik'a ma Seebi, ta amsa kallo daya ta ma rubutun ta san nashi ne, don ta yi mastering rubutun shi, duk inda ta gani zata gane, ta fara karantawa *"She'll be staying with Nene Until she's discharged, and you,,,, you are so not skipping classes, Come out now"* ta karanta letter ya fi a kirga, wannan wani irin Letter ne? Ba gabas ba yamma, sai orders din da yake badawa, to ko wannan matar yake nufi da zata zauna da su har sai an sallame ta? Ita kuma ba zata yi missing School ba kuma ta fito waje ta sameshi? Haka yake nufi? Indai haka ne, to it means ya ji me suke cewa da Nene dazun, hakan na nufin ya damu da lamarin su? He cares for them this much? Lallai he's doing more than enough for them, its time ta fara cika Alkawarin da ta daukar ma Rafee'ah, Allah ka taimakeni, nan taji wani kwarin guiwa, tayi saurin fita, Nene tace "ke kuma ina zakije?" ina seebi tayi gaba, Hajjo ta riko hannun Nene tace "Ni zan yi jiyar ki kawata" Nene tayi murmushi kawai.

Inda yayi parking Jiya ta nufa, sai ko gashi zaune kan mota, ya cire rai da zuwan ta, shi kuma ya ki tafiya, sansayar muryar ta yaji tayi Sallama tare da cewa *"Hamma Rafeeq"*da sauri ya diro daga kan motar, yana me kallon ta, Murmushi ta mishi tace "Hamma na ina kwana?" kawai sai ya ga ta chanza ta koma Rafee'ah, da sauri ya lumshe ido ya, chan ya lula duniyar tunani, *"Kai Rafeeq wannan ba Rafee'ah bace, Rafee'ah ta rasu, She's never coming back, dont let this girl mess with your head, you cant let her play with your mind "* ya bude ido tare da yin guntun tsaki, ta gaban ta ya wuce ba tare da ya kalle ta ba yace *" Get In The Car"* ya shige ya barta tsaye, na take wasu tunanin suka zo mata, Anya zata iya? Zata iya da Zafin kan Rafeeq? Anya zata iya da halin shi? anya zata iya jure komai? Ji tayi wani abu ya k'arfafa mata zuciya, taji wani irin Kwarin Guiwa, A baiyane tace *"I Can and I will, I musnt give up, not now not ever, Rafeeq Lema da yardan Allah sai ka dawo daidai"* tana kaiwa nan ta fada motar.

(Please Lovers❤ Ignore all the Typos and Errors👏🏽👏🏽👏🏽)
_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

     NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

This is for you *Maryam AD Bappa(Umm Eeman)* Thanks for Everything ILY❤❤❤
Pg3⃣9⃣

Nasiba ci kukan ta ita kadai, ta share hawayenta, ta kimtsa fuskarta gudun kar nene ta ishe ta da tambayoyi, suka dunguma zuwa dakin tare da Baba mai gadi. Kowa da abun da yake sak'awa a ransa.
Shigar su dakin yayi daidai da fitowar nene daga bandaki, inda ta dauro alwala zatayi sallah, Hajjo kuma na zaune kan darduma tana lazumi.
Nene ta washe baki ganin Baba maigadi suka hau gaisawa, yai mata ya jiki, Seebi kuwa duk yadda taso ta boye damuwarta ta kasa, Nene ta dan gane yar jikallenta na cikin damuwa, ta tambaye ta "ko lafiya?" Seebi tace "Nene ba komai, gajiya ce kawai amma nasan in na dan huta zan ware" Nene ta amsa da to Allah huta gajia.

Bayan tafiyar Baba ne suka zauna suka ci abinci su ukun duka, suna kammalawa Seebi taja gefe ta rusuna tana tunanin ta inda zata fitowa *R-LEMA* don tabbas rayuwarsa na cikin gagarumin hadari.
Kuma He is proving so difficult to deal with.
Haka ta dinga 'yan tunane tunanen ta, ta sak'a wannan ta kunce wancan har bacci ya dauketa ba tare da ta samu mafita ba.

Yau Alhamis kwanan su hudu kenan a Asibiti.
Seebi ta idar da sallar Asubah ta kammala adduoin ta, littafanta ta janyo ta dan dudduba don tana da lectures 9am kuma Malamin ya iya test din bazata.
Bayan ta gama revising ne ta rufe ta maida komai cikin jakarta, ta saka Hijabi kan kayan baccin dake jikinta tare da gyara fuskar ta sama sama don batayi wanka ba,
tayi wa nene da hajjo sallama ta wuce gida don shirin Makaranta saboda sauran kayan da ta da ke Asibitin sun yi Datti.

6:50 ta isa gida, sai da ta share gidan ta ta gyara ko ina kafin ta fada toilet tayi wanka ta shirya ta, ta fito Gida 7.55am. Sauri take ta isa bakin titi don ta samu abun hawan da zai kaita National don kar tayi missing Bus.

Kamar kullum, Tuk'in shi yake cikin qasaita, daga nesa ya hangota, kamar ita kamar ba ita ba, kai itace, wannan yarinyar ce, a ransa yace "Wannan kuma me takeyi a nan? (kuji se kace be san nan gidansu yake ba) guntun tsaki yayi yace "Da naje daukan ta a Asibiti da nayi zuwan banza kenan" ya sake wani tsakin kamar yana gabanta. Horn taji da karfi, da sauri ta dode kunnenta tare da juyawa a k'ufule don ganin me neman kashe mata dodon kunne, ita da ba kan hanya take ba, Idonta ya kai ga Motar Rafeeq, haka kurum taji dadin ganin shi duk da ta san ba wai kulata zeyi ba, ko ba komai, ba zatayi latti ba, kuma zata samu daman mishi magana.

Bude motar tayi ta shiga don tasan ba ce mata zaiyi ta shiga motar ba, cikin wata muryar da bata san tana da shi ba tace "Ina Kwana Hamma Rafeeq"
Jan motar shi yayi, ya dau hanyar school yayi kamar be jita ba, har ta cire rai da zai amsata, don sunyi tafiyar kusan 4mins kafin taji yace *"lafiya"* da mamaki ta kalleshi, ta ma manta da ta gaishe shi, a ranta tayi dariya tace *"bakasan waye jikar nene ba sai ka dawo hanya da Yardan Allah"* wani kwarin guiwa taji, ta gyada kao tace "i can do it" Cikin sigar shagwaba tace *"Hamma na please..."* sai kuma tayi shiru tare da duban sa.
Wani uban tsaki ya buga da sai da taji tsoro, ya maida hankalin shi ga tukin sa, don duk yanda ta kirashi da *"Hamma Rafeeq"* sai numfashin sa ya dauke, balle yanzu da ta zak'e wai *"Hamman ta"* "wannan yarinyar ta fara koyon surutu, ta fara zak'ewa"
Kamar ba zai ce komai ba yace " what?" ta ji dadi tare da samun karfin guiwa, tace dama zance ko in munje wancan shagon zaka dan tsaya na sai Ziza Milk, don banci komai ba ina sauri kar nayi latti.

Besan lokacin da murmushi ya subuce masa ba, cikin sakwan da be wuce 2 ba ya daure fuska, a ransa yace "what is funny?" ji yadda take sunne kai kamar mara gaskia, lazy girl she cant even skip breakfast. Be dai ce da ita komai ba

Daidai wani shago ya tsaya, tayi murmushi tace "yawwa Hamma na Nagode" Ta dauki jakarta, tana k'okarin bude kofar taji ya bude tasa kofar ya fita tare da rufowa. Gyada kai tayi cike da tausaya wa, don shi duk abunda yakeyi bata jin haushin, illa ma tausayin da yake bata. Be dauki lokaci ba ya dawo da leda kunshe da soft drink da kuma date bars ya aje mata kan cinya, ta masa godia suka dau hanya.
Ta bude jakarta don saka ledar a sama ta tsinci muryar sa *"EAT NOW"* tace " *to Hamma na*. Ta bude tana ci har suka iso School, har bakin Department dinsu ya kaita, kimtsa bakin ta tayi masa godia ta fice. Shikuma ya ja motarsa ya k'ara gaba.
Yana wucewa ta sauqe wani gauron numfashi tace "Wai Allah nagode maka da ka sa min dauriya, Allah ka kara shige min gaba Ameen"

Zaune take gefen nene tana waya da Uncle Zaid, inda take sanar dashi cewa Nene ta warke, likita yace zuwa magriba zai Sallamesu. Uncle zaid yace "Alhamdulillah, Nene ta ji sauk'i, idan anyi sallamar ki sanar dani" tace "toh"
Ta masa godiya suka yi sallama. Ta miqe ta shirya tace "Nene zan shiga makaranta bani da lecture, amma ina da Assignment din da zanyi submitting kafin lokacin sallahr Juma'a, da an gama sallahr Jumaa'h zan dawo wuraren k'arfe biyu, sai a hada kayan kafin likitan ya zo ya bamu Sallama".
Murna gun Nene kamar me, tace "wlh dama na gaji da Asibitin nan, Mutum da lafiyarsa amma an kawo Asibiti an ajiye, amma fa zanyi kewar 'yar gasasshen Kazar da dunkum ke kawowa" (Dunkum ne sunan da Nene ta sa ma Rafeeq) ba Seebi ba harta Hajjo dake gefe sai da ta dara tace" Kai k'awalliya, jika na ne Dunkum?" Nene tace "yo ehmana, ayi mutum shi he daria, be murmushi be magana? Hajjo tace "lamarin Rafeeq sai du'ai, haka yake" Nene tace "Shiyasa na rik'e furfurata, ba ruwana dashi, don in na mai magana ya share ni, ina iya kulle shi daki karfe ukun dare inci Ubanshi, dan uban mutum" me Hajjo da Nasiba zasuyi in ba daria ba, Nasiba har da kwallah, Hajjo tace "Lallai Nene Lafiya ta samu" Nene tace "dama garas nike, uwayen fiili suka daura man zaman dole a Asibiti, wato Seebi da Zaidu bawanAllah" Nasiba dai ba ta tanka ba.
Dan zaman da sukayi na kwanaki biyar Hajjo da Nene suka Saba don Nene akwai surutu da saurin shiga rai, hajjo kuwa akwai barkwanci..

Ku daga daga k'afa mu isa on time kunga yau Friday, Buses cika zasuyi da wuri. Seebi ce mai maganar nan, Usheey tace "in ba haka ba sai mun ci uwar trekking kafin mu samu naAllahn da zai bamu Lift.
Chapter 39 · 0% Book details