← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 95

Sashe 50

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"Nasiba, kin taba ganin uwar da tayi fushi da danta? ko tayi fushi dashi na wasu lokaci ne, ko me ya ke mata ba za ta tab'a fadin Mummuna kalami a kanshi ba, tsakanin d'a da Mahaifi sai Allah, balle ni da ban taba ganin Laifin Rafeeq ba illa Laifina, nice na sakashi a halin da yake ciki yanzu". Nasiba ta kamo hannun Mami tace "karkiyi Blaming kanki, k'addara ce ta riga Fata, nidai DonAllah kice kawai ki yafe mishi duk da kince be miki komai ba" Mami tayi Murmushi tace "Toh Nasiba, na Yafe ma Rafeeq Duniya da Lahira, na yafe mishi, Ubangiji Allah ya sa ya gama da Duniya lafiya, Allah ya bashi saar karatu, Allah ya ma Rayuwar shi Albarka" da sauri ta Rungume Mami dadi kamar ya kasheta, ita a ganinta zataji Saukin komai tunda Rafeeq na tare da Adduar Mahaifiya, tace "Ameen Mami, ki Cigaba da mishi addua kullum, InshaAllah ba zai tab'a tab'ewa ba" Mami ta tsura wa Nasiba ido cike da k'auna tace "Bless you Daughter, you have an Amazing Heart, Ke Alheri Ce" Murmushi kawai Nasiba tayi, don bata son tayi magana Mami ta cigaba da kukan da takeyi, tace "Mami yaushe zakizo Katsina? Katsina na missing dinki" Murmushi tayi tace "i have no Bussiness left in katsina, Duk Wata Baba na da Mama na su na zuwa duba ni" Nasiba ta sigar zolaya tace " are you sure you have no Bussiness in Katsina? Mahaifarki ce fa, besides, your One and Only Love is there, nasan he still inside that pure heart of yours" Mami ta daburce tana unconditional Murmushi, tace "ke Nasiba maganar me kikeyi haka? Shuttup ni ba kowa a zuciya na, na tsufa" Nasiba tayi dariya tace "Is that so? Then why are you blushing?" Murmushi Mami tayi tace "How i wish zan sake ganin Habibullah" "Awwwn Mami ta tuna da tsohuwar Zuma" tace "Kinsan ana cewa Zaid me kyau ne, Hafiz Me kyau ne, amma Wallahi duk Habib ya fi su kyau, harta Rafeeq da ke kama dashi be kamo k'afar shi ba" Sosai Nasiba tayi daria tace "zai k'ara kyau idan kika koma dakin ki" Mami tace "Hmm nagaji da tsammanin Ranar nan" Nasiba tace "Dont worry Mami,Akwai Allah, gaskiya zata baiyana, zai gano gaskia da na rashin bincike ne ya sa shi daukar mataki take yanke, amma kar ki damu, Have faith" Mami tace "dadi na dake you give me Hope" Sukayi Murmushi, kuma chan sai Mami ta fara matsar k'wallah, Nasiba tace bari in kira miki Nene ki sha dariya.

*Washegari*
Ina Nasibar ne? Sai mun rasa Motar K'arfe 10? Ummi tace "wai ta shiga yi ma Mamin Ayman Sallama yanzu zaka ga ta taho" Abii yace ai gwara tazo mu ta tafiya.
Mami tace "Yanzu ba zaki k'ara mana hutun ba? Kin bari mun saba sosai sai kice zaki wani koma?" tace "Ayyah Mami, nima na saba dake Sosai, idan mun tafi ba zamu dade ba zamu dawo, trust me zan dawo" Mami tace "to shikenan, ga wannan kiyi using as Pocket Money" "Nooo Mami i cant accept your Money" Mami ta tsura mata ido, tace "ni na dauke ki ne a matsayin Rafee'ah, and i can do anything for you, don break my heart" "Mami kudin sunyi yawa ne ki raba biyu" " Haba Nasiba dubu Goma ne fa, ba yawa, inshort why dont you be like Rafee'ah? Be like Mami kudin sun min kadan, i need more" daria Nasiba tayi tace "Okay, I'll accept this Nagode" "Yauwa diyata" tace "One more thing" ta zaro dan karamin Zoben da ke k'aramin yatsar ta ta sa ma Nasiba a yatsa tace "this is my love for you" Nasiba ta bi zoben da kallo, tana so ta tuno inda ta san Zoben, Zoben me kyau ne sosai, kuma Azurfa. Mami tace "kinsan waya bani Zoben Nan?" ta girgiza kai, Mami tace "Rafeeq ya bani shi on my 40th Birthday, Daga Dubai ya sa akayi su Guda 2, ran Birthday na ya sa min a yatsa yace "Mamina, this is my love for you" ya bani gudan yace in sa mishi a, yace "this is the twin of your ring, even if we are far from eachother, this Ring is linked to Our hearts" daria kawai nayi nace dashi"he's Crazy" amna Nasiba yanzu Rafeeq ya tsane ni, nasan Ya dade da wurgar da Zoben shi" Nasiba tace "Aa Mami, wallahi be wurgar dashi ba, yana nan a yatsar shi, ni na san na san Zoben nan a wani wuri, a Yatsar Rafeeq na sanshi" Mami tayi dariya tace"Nasiba kenan, you want me to feel better, shikenan naji, its yours now" Nasiba tace "Aa Mami, wannan naki ne, ki ansa" Mami tace "bansan gardama tashi muje, ni ma zan kai ku tasha, kar ku rasa motan hawa" suka fita tare, a ranta tace "with this Ring Rafeeq, you'll be your Mother's Son Again". Da sauka shiga gida ne ta nuna ma Ummi kudin da Mami ta bata, Ummi ta mata fadan meyasa ta amsa, Mami tace don na ba diyyata kudi shine nayi laifi? Ko iko zaki nuna min kanta ki nuna min diyarki ce, tace "laaaah Mamin Ayman be kai nan ba, ai an fi so diyarki taji tausayinki" Mami tace kya dai ji dashi, gabaki daya sukayi daria.

*4:00pm*
*Layout, Katsina*
Chapter 50 · 0% Book details