← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 95

Sashe 81

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Busy Rafeeq da Nasiba suke, saboda Exams dinsu da ya k'arato, a lokaci guda Kuma wani Son junar su na shiga cikin jinin jikinsu, Rafeeq yace da ranshi if you kee on seeing her, you'll only Love her More and you wont fulfill your only Dream, which is to Make Uncle Zaid Happy, Dole ya daina haduwa da ita ko don Uncle Zaid, ya kagara ya gama Makaranta, da ya gama zai ware ya bar k'asar, don yasan Uncle Zaid he would stop at nothing har sai ya aura mai Nasiba shi kuwa idan har Uncle Zaid be aureta ba shima ba zai aureta ba, saidai suk su rasa. Alk'awarin da ya daukar ma kanshi kenan, haka a fannin Nasiba, ita dai tasan Tana mugun ganin girman Uncle Zaid, tana jinshi a ranta kamar Babanta, kunyar shi takeji, kwarjininshi ya mata yawa, Hallarci, So da k'aunar da ya musu ita Da Nenenta zai sa ba zata ta6a butulce mai ba, duk da ba wani Son Soyayyar da take mishi amma ganin girmanshi zai sa ta Aureshi ta kula mishi da tillon diyarshi, ko tana so ko bata so, dole Ta Auri Uncle Zaid, Dole ta yakice Rafeeq Lema a ranta, bata taba zaton tana ma kanta irin Son da take ma R-lema ba, tana me tausaya ma kanta, ta kasance me Son maso wani koshin wahala. Dole ta nisantar da kanta daga R-Lema, don yawan ganin da take mishi ne ya ke k'ara mata sonshi.
***********
Rayuwa Kenan, Gaskiar Hausawa da sukace Ramin K'arya K'urarre ne, In zaka gina ramin mugunta ka ginashi dan k'arami, kuma komai nisan Jifa kasa zai dawo, Kuma duk wani abu da ba a ginashi ta hanyar Allah ba, to ba a ganin daidai, K'aryar Saude ta k'are, ba ta da saurin gata, Cikin lokacin kalilan Saude ta koma watta halitta, abubuwa sun mata yawa.
Skin Disease har uku, K'azuwa, sankarau da kezbi, hakan ya sa ta koma kamar bushahshen kwado.
Sai Idonta daya ya tsiyaye, mai lafiyan kuma ya kamu da ciwon polio mai kwantsa da Yana.
Ga kuma ciwon ga6obi a guri uku; bayanta, wuyanta da kwankwasonta.
Sai kuma basir mai tsiro gaba da baya.
Shi ya sa ta tsani kanta, duk ta koma wata hallita daban, jinya take tayi, da wannan wuri ya warke sai wani ciwo ya baiyana har Allah Allah take Alk'ali ya yanke mata hukunci, don a halin yanzu tafi son mutuwarta fiye da komai.
Kotu
Kotu ta cika Makil, Iyalan Habib Lema zaune a kujerar gaba don jin hukuncin da zaa yanke ma Saude, a ka fito da ita, da kyar Mami ta shaida ta, duk ta jeme ta kanjame, wasu kuraraji a jikinta ba kyan gani, ga ido daya a makance. Hat tanta ta tausaya mata, Aneesa ma kukan takeyi, Nene ko sai tabe baki.
Bayan Saude da Mak'ale sun Ansa laifin su, Alk'ali ya yanke ma Mak'ale hukunci Kisa ta hany,ar rataya bayan kuma ya tona asirin Abokanshi da suka kashe Hafiz Lema tare, Saude kuwa hukuncin Daurin rai da rai da kuma horo mai tsanani, wato Life Imprisonment with hard labour, Ihu d kururuwa ta dinga yi, tana fadin "Alk'ali, dama ka sa a kasheni, donAllah kunkasheni da me zanji? Da cututukar da ke damuna ko da Wannan hukuncin? Na tuba, ni ko Kisa ta hanyar rataya ne ku min, ko harbi na zakuyi kuyi, donAllah kar ku barni da Rai, ku kasheni, Please end my Suffering, li want to die" haka Saude ta dinga Ihu tana sambatu, da yawa ta ba tausayi a kotun nan, ko da Nene taji wasu mata Na cewa ta basu tausayi tace "don ba ku san abubuwan da tayi ba, haka ta dan basu labari a takaice, matan nan suka tabr baki tace, ya mata daidai, Ai duniya Makaranta, abunda ta shuka ne take girba. Ba na tunanin zata k'ara Sati biyu a raye don Wannan kurarrajin jikinta ba na warkewa bane" Nene tayi daria tace "yauwa yan gari" Mami kuka Seebi kuka Aneesa Kuka, Rafeeq na ganin haka ya tattara su ya maida gida don ko kadan bata bashi tausayi ba, yana ganin hakan ne daidai ita, baya so ta mutu don yasan mutuwa hutu ne a gareta, gwara ta tsaya da ranta bakin ciki ya cinyeta.

Biki Saura Sati Biyu
*Mafarki*

(Afuwan. Abunda ya samu kenan.
Zan cigaba, ina Makaranta☹☹☹
Masu min mgn ta prvt da ban samu nayi replying dinsu ba ba Afuwan.abubuwan da yawa)
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

This page is for all Members of JUST NOVELS, Baby nice and above all Sadeeqah Ummu Sudais, ILY'lls Oceans and Galaxies❤
Pg5⃣9⃣

Biki Saura Sati Biyu
*Mafarki*
Chapter 81 · 0% Book details