← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 95

Sashe 8

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MC ya fara gabatar da shirin Biki, Hajia Aishatu ta bude taro da Addua, Rafeeq ya bada tarihin Ango, biki yayi biki, anci an sha, an gwangwaje, Rafeeq da Rafee'ah sun taka rawar gani, shima Ango ba a barshi a baya ba don sai da Rafeeq ya sashi rawan dole, akayi hotuna, sukayi Family Photo.

Washegari aka daure aure, aka kai Amarya Gidan ta da ke Kaduna U/rimi, da yake chan Zaid yake aiki. Part daya aka ware ma Rafeeq a gidan Zaid don Zaid da Rafeeq kamar abokai suke, ba za ka gansu kace Kawu da dan shi bane.

Rafeeq dan dangi ne,duk inda ya gifta sunan shi kawai zakaji ana kira, yanuwa da abokan azziki, manya da yara, kowa Rafeeq, tabbas Rafeeq yana da farinjini, ba don komai ba don shima he's a simple somebody, ba ruwan shi da zabe, yace ina yi da wannan ba nayi da wannan, aa kowa nashi ne, yana da son mutane, da son wasa, ya ja wannan tsokana, ya ja wannan tsokana, maza da mata, bashi da kyamar talaka. Rafeeq fari ne, bai ciki tsawo ba, bai cika gajerta ba, dan daidai, be da kauri sosai, kyakyawa ne ajin farko, har friends dinshi na mai kirari da ''all ladies eyes on Rafeeq'' duk budurwa mai ji da kanta ta na so a ce da ita budurwar R-Lema, saboda ya hadu, Arzikkin baban shi be sa shi girman kai ba ko kadan, haka fa yake a makaranta, kullum suna Cafteria shi da Abokin shi Mahmud Maalesh, Maalesh abokin Rafeeq ne tun Secondary School, Abotan Maalesh da Rafeeq ne ya sa Iyayensu ke zumunci, idan ka ga Mami da Mummyn Rafeeq zaka zata yanuwan juna ne, Maalesh is his partner in crime, idan sunyi laifi Uncle Zaid ke hukunta su, don ba sa jin magana, duk wani party sai sunje sun sha rawa, ba sa shaye-shaye, ba sa bin mata, amma yanmatan su sunfi 50, don shi Rafeeq kafin yace yana so to an riga cewa ana sonshi, Irin Matashin nan ne wanda be da wata matsala a rayuwa, kowa na shi ne, kar kuyi zaton Rafeeq be mayar da hankali a karatunshi, to ba haka bane, Duk Department din su na BioChemistry, ba kamar Rafeeq, Lecturers kance, "idan akwai abun da yafi 5point, to tabbas Rafeeq zai buge shi" irin su ne ake cewa "Always ahead of the Lecturers" saboda kokari, Allah ya ba Rafeeq k'wak'walwa, both ilimin Addini da na boko, a shekaran shi na 16 ya sauke AlQurani mai Girma ya kuma shiga Jami'a, Yanzu haka yana da shekaru 20 cifcif kuma bana zai gama Jami'a.

Rafee'ah kuma tana karantar Sociology tana aji 2. Ba su fiye shiri da Rafeeq ba don ita shiru shiru ce, shi ko yayi ta tsokanan ta, Rafee'ah kyakyawa ce, bata fiye son magana ba, amma indai Rafeeq na gida dole sai ya sata magana da yawan surutun shi da tsokanam ta da yake yi, tun bata biye mishi har ta fara biye mishi, da ya mata take ramawa, idan kuma abun yafi karfinta, sai taje tana ma Mami kuka, mami kuma ta ma Rafeeq fada, hakan ba zaisa gobe ya kuma tsokanan ta ba.

Gidan Habib Lema, gida ne da aka ginata cikin So, Aminci da yardan juna, suna matuqar son junan su, ba su da Matsalan komai, Mami(Hajia Aisha) ta tsaya tsayin daka wurin tarbiyantar da yaran ta bisa tafarkin Addinin musulun ci, tun suna yara Uncle Zaid ne Discipline Master, idan sunyi laifi shi ke hukunta su, Shiyasa Suka tashi da son junan su (Wannan Kenan).

Daga sama Mami taji ana "Assalam Alaikum" ta bude idanunta a hankali don a gajiye take tun bayan biki, ta dan bude murya ta amsa sallaman tare da cewa "ku hawo saman please" Suka nufa sama, su biyu ne, kana ganin su kasan uwa ce da diyarta, diyar ba za wuce shekara 17 ba, a bakin kofa suka iske Hajia Aisha, tana ganin ta fadada murmushin ta, "Saude kece anan? Sai da muka gama bikin zakizo?" Saude tace "Ayyah madam, wallahi naje gida ne, shiyasa banzo biki ba" "bakomai ai, wannan diyar ki ce? Kafin kace wani abu yarinyar har ta zube kasa tana kwasar gaisuwa, Mami ta dago ta tana kallon ta, wani irin kama taga yarinyar nayi da Rafee'ah, tace what's ur name? Yarinya tayi murmushi tace "Sunana Aneesa" Wow nice name, sannun ku da zuwa, ku shigo" suka shiga ciki, kafin kace meye wannan Mami ta cika musu gaba da kayen ciye-ciye, suna ci suna fira jefi-jefi, Saude tace "bakowa a gidan sai ke?" tace "eh wallahi, ni kadai ce, duk suna kaduna, tunda aka kai Amarya basu dawo ba, Saude tace "Ayyah Allah basu zaman lafia" tace "Amin"

Saude Secretary din Hajia Aisha Lema ne a Office, watan ta 6 kenan da fara aiki a office din Matar Habib Lema, tana da kwazo wurin aiki, shiyasa Hajia Aisha ke ji da ita. Six months back ne ta kawo CV dinta da qualification dinta na NCE, office din Madam Lema.
Wurin interview ne suka bata tabbacin ba sa daukar masu NCE sai masu Degree, ta dinga kuka wai a taimake ta, mijin ta ya rasu, ya barta da diya daya, ba halin ciyar da ita suna cikin hali na kuncin rayuwa, yanda take kuka taba interviewer din tausayi, yaje ya sanar da madam din su, madam ta nemi ganawa da Saude, ta bata bayani, itama taji tausayin ta, tace "Madam ki taimake ni, kamar yanda Allah ya taimake ki, you are a mother, kinsan irin son da uwa ke ma diyarta, Miji na ya rasu ya barni da diya daya, dangin shi sun kwashe Gadon, ta tsaya a Secondary, ki taimake ni ki bani aiki da zan kula da diyata" Hajia Aisha ta ja numfashi, sosai Saude ta bata tausayi, tace "can you be my Secretary?" ai ko nan Saude ta zube ta na godia, tace tana so ta gode Sosai harda kukan murnan ta" washegari ta fara aiki as Madam's Secretary, Saude akwai kokarin aiki, da zasu tafi Hajia Aisha ta shiga Dakin Rafee'ah ta tsinto ma Aneesa kwancen kayan Rafee'ah, ta cika su da abun arziki.

Bayan Wata Daya

Gaba ki daya suke zaune a Babban parlorn Habib Lema, Uncle Zaid na fira da Uwar dakin shi Mami, Rafee'ah na kusa da Baban ta tana karanta mishi newspaper, daga gefe kuwa Rafeeq ne ke ba ma Aunty Seema(Matar Zaid Safiyya, sunzo ne) labarin yanmatan shi na makaranta da na Unguwa, tana ta daria, da kagan su kasan Happy Family ne wanda basu da damuwan komai da kowa. Wayan Alhaji Habib Lema yayi ringing, Rafee'ah ta tashi ta dauko mai kan sidestool, ta amsa ta sa ma babanta a kunne, "*Hello* *Yaya*? Dam gaban Alhaji Habib ya buga, ya mik'e tsaye cikin kidima, a hankali yace "Hafiz, kaine? Zaid da Mami suka mik'e tsaye suka nufo Alhaji da jikin shi ke rawa, ya kasa cewa komai, Zaid ya amsa wayan ya sa handsfree yace "Hello?" daga dayan bangaren aka ce "Hello Brother" Zaid yace "Hafeeez, is this you brother, where are you?" karbe wayan akayi daga hannun Hafiz akace "Hello This is Secret Service Agency Lagos, Hafiz Lema's been Jailed 10years ago, he's completed his Sentence, and is fined 500usd, come to the Agency for more details". Dif ya kashe wayan.

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)

Pg1⃣1⃣

Washegari
Habib yayi sallama parlon Alhaji Tijjani da Asuba, duk'a wa yayi har kada yace "Baba Barka da Safiya" Alhaji ya dago kai yace "lafiya lao Habibullah, ya gajiyar jiya? Habib yace "gajia ta bi jiki baba" Alhaji ya tambaye shi game da ayyukan da yajeyi a Cairo ya shaida masa komai na tafiya daidai.

Yace "Jiya sai ku ka ga bak'uwa", Alhaji yace " Aisha ko? Sai da tace min tare kuke na gardama mata, amma daga baya na yarda da na tu a kaima fa jiya ka dawo, amma ya akayi ka shaida kanwar ka, don na san ba ku san juna ba?" Habib ya kwashe komai ya gaya mai, Alhaji ya jinjina kai yace "haka Allah ke abunshi".

A kwana a tashi Habib da Aisha sun yi wata irin shak'uwa da junan su, har so ya shiga tsakanin su, soyayyah mai tsafta sukeyi, Alh. Na sane da su amma yayi shiru, a zahiri kuma yana farin cikin wannan abu don Habib mutumin kirki ne, irin shi yake so aura ma Tilon yarsa, amma tunda sun hada kansu tun wuri toh falillahil hamd.

Wata rana Habib ya shigo gidan don zuwa kiran Baba tijjani, ya aika a kirashi, Bayan gaisuwa Alhj ya muskuta yace " Habib dalilin kiran ka shine in shaida maka yau za muje mu kai kayan sa bikin Aisha, tunda kai kadai ne yayan ta, ina so ka hallara wurin zuwa, idon Habib ya rufe, be san sanda yace "baba, wace Aishar? Ban gane ba? Yace " Aisha kanwarka ko? Aishan Misra" Habib ya zabura yace "what?, Baba kar ka min haka, wallahi nike son Aisha, kuma tana sona baba kar ka rabu mu don darajan Allah, cikin fushi yace kuma ai a aladance zuwa ake gidansu yarinya a daidaita tsakani, ba wai da ga gidansu yarinya zaaje gurin Namijin ba, hala dan sarki ne" ya fada a fusace.

Sosai Alhaji Tijjani yayi daria, sai da ya tsagaita yace " Habib in banda abinka, ya zaayi dangi mata suje kai kayan biki? Ai ko a masarauta ba a haka, kwantar da hankalin ka d'a na, Kayan Biki zamu kwasa ni da kai muje chan gidan k'anena kuma waliyyin Aisha, in nema maka aurenta gun shi. Kunyar duniya ta lullube Habib, a take ya bar parlorn don kunyan baban da yakeji yana murmushi.

Aisha tsallen murna takeyi da Habib ya gaya mata abunda ya faru tsakanin shi da baba dazun, tayi daria sosai tace "wato kai loverboy ko?, ka mance baba kana ta sakin layi" yayi daria shima yace "sanki ne ya jawo hakan" tace ni ba "ruwana".
Chapter 8 · 0% Book details