← Book details Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 95

Sashe 4

Ke Alheri Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaid yace "ina zuwa, ya fita" tsohuwar ta bishi da ido, motarsa ya shige, bayan mintuna kadan sai gashi da mai gyaran wuta, Zaid ya kalli tsohuwar yace " Toh Iya, ga mai gyara nan, ni zan tafi" baki bude tsohuwar nan take kallon shi, bawan Allah tsaya, Zaid ya tsaya, tace Nagode kaji? Allah ya biyaka, Zaid yayi murmushi. "Amin Nagode Iyah, ni na wuce" tace "donAllah ka tsaya, na kwadanta maka zogale" yace "wallahi, sauri nake, kaduna zan tafi yanzu" tace toh dan jirani da sauri ta shige kitchen, sai ga ta da bakar leda ta mik'a mai, tace gashi ya amsa yana mamakin me ke ciki, tace kayan miya ne irin su daddawa, kuka, kanwa da su kanumfari" ya ce toh ni iyah-- ta katse shi ta hanyar cewa a kai wa Uwargida, idan babu kuma akai ma mahaifiya, Zaid ya sake wani murmushi, farat daya yaji son tsohuwar nan har ranshi, yace "toh nagode Iya" tace bakomai har ya juya tace "nidai, in kace min iyah, ji na ke kamar ka mayar dani wata tsohuwa, zaid yayi daria sosai, yace ai tsohuwar ce" tace "kai bawan Allah, ban wani tsufa ba" yace toh shekarun ki nawa? Tace goma-goma guda shiddada hudu Zaid(10*6+4) ya bude baki yace lalala 64 fa kenan? eh lallai baki tsufa ba" a tare sukayi daria. Yace "toh me zan dinga kiran ki dashi ? Tace "yanda jikoki na ke ce min, NENE"

_Bibilicious biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS
ASSOCIATION(NWA)

Pg6⃣

Zaid ya murmusa yace "toh nene" tace "kai ya sunan ka"? "Sunana Zaid" tace "Zaidu Bawan Allah" yayu dariya yace "toh Nene bari dai in wuce kar nayi rana". tace "Gaskia ne, ince kaduna zaka ko? Ko ka san d'a na? Hafizu Mamman? Fari dan fulani" Daria sosai Zaid yayi yace "Nene kaduna babban gari ne, ba yanda zaa yi na san shi" tace "Allah ka bincika, duk kaduna shi kadai ne" Zaid da ya k'osa ya tafi yace "Toh Nene", Kudi ya ciro ya ba mai gyara suka kara Sallama.

Har bakin motar shi ta rakashi, tana daga mai hannu tana mai addu'oin kariya. Ya tada motarshi yayi ribos,ya dau hanyar barin unguwar, Nene ba ta koma ciki ba har sai da ya kure ganinta kafin ta koma cikin gida, bini-bini sai ta saki murmushi tana tunanin Zaidu bawan Allah.

Asalin Sunan Nene :Amina amma an fi saninta da Aminene, 'ya'yanta 6, dattijuwa ce me kimanin shekaru 65, Mijinta ya rasu shekaru 20 da suka wuce ya barta da 'ya'ya 5, a halin yanzu 2 suke da rai 3 sun rasu. Cikin wanda suke da rai akwai Fatiti, ita ce diyar Nene ta biyu, tana aure a Jihar Jigawa 'ya'yanta 3, Amina,Umar da Muhammad.

Muhammad Bishir Sunan autan Nene, yana zaune da matarsa da 'ya'yansa biyu a Malali cikin jihar Kaduna. Nasiba ce ta farko sai kaninta Anan. Muhammad Yayi aiki a National Trust fund kafin a kulle kamfanin (Company). A hanlin yanzu ba ya aiki amma yana karban pension duk wata.

Nasiba yar kimanin shekaru Sha tara a duniya(19), ba za a sa Nasiba a jerin farare ba, haka kuma ba za a sata a jerin bak'ake ba, wankar tarwada ce, me dara daran idanuwa, idan tayi murmushi kumatun ta sukan lotsa, bata fiye tsayi ba, kuma tana da dan jiki daidai ita, a takaice Nasiba ta kai macen da ake kira da masu kyau.

Tayi karatun ta na Nursery, primary harda Secondary a Kaduna Capital School(KC). Bayan ta gama ne baban ta ya siya mata JAMB, da doki tace Abba ai Katsina zan sa ko? Ya harare ta cikin wasa yace "kina nan, don ko Rigachikun ba za ki wuce ba" ta turo baki tare da bubbuga kafa tace nidai wallahi Abba bana son KASU" tun nursery dina a nan nayi Abba, Shekaru 15 ina karatu a kd, ai change of environment na da dadi, ka ga sai in kular maka da Mamanka tunda tak'i yarda ta dawo gidan nan da zama"

Umma tace "Eh kinyi gaskiya Nasiba, Nene na bukatar wani kusa da ita, tunda anyi anyi ta dawo kaduna ta ki yarda, ya kama ta kije chan kiyi karatun, Mutum ai rahama ne" Abba ya jinjina kai, yace "ko don Nene zan barki kije Katsina karatu" tayi ihun murna tace yauwa "Abban mu"

Anan yace Adda Seebi yanzu kina murna zaki tafi ki barni ko? Sai ya fashe da kuka, da saurin ta rungume tillon kaninta ita ma kukan take yi tace yi shiru Anan, ai zan dingw dawowa hutu kaji?kuma ga Abban mu ga Ummin mu ai ka ga ba kai kadai bane ko? Da kalamai masu dadi ta lallashe shi har yayi bacci, ta dauki form din ta fita don zuwa dakin ta, ta cika 1st&2nd Choice UMYUK, Microbiology course don school din basu fara Medicine ba.

Abba ya kalli matarsa yace Ummin yara, gidan nan na layout(Gidan gadon shi), ina ganin zan tada mutanen ciki Nene ta koma can, Gidan Kofa Uku ya tsufa,nan aka haifi marigayi Yaya Shehu fa, Umma ta kada kai tace lallai ya tsufa kam, kinga kuwa sai ta koma gidana na layout din, Ummi tace "toh Allah ya sa ta yarda, don yanda take son Unguwar nan, raba ta dashi sai Allah, saboda mutane da Abokan arzikkin ta ya sa ta hana a dauko mata wacce zasu dinga zama tare saboda kadaici," Abba yace ai Nene in ta kafe ba me tankwara ta, amma bakomi na san yanda zan bullo wa lamarin" Ummi tace Gidan fa? Yace "sai in gyara a zuba yan haya ciki"

Cikin Ikon Allah, Watannin da basu rufe 10 ba, Nasiba ta samu Admission a Jami'ar Umaru Musa, course din da ta zaba suka bata, Gaba ki dayan su suka zo Katsina don rako Seebi, don daga Registeration ba za ta dawo Kaduna ba.

Nene tayi murnan dawowan Seebi gunta, don ta na son jikokin ta sosai, bayan sun huta, Abba ya kebe da mahaifiyar shi, Nene tace "Ya akayi ne Mahammadu? Cikin ladabi yake maganan, yace " Nene, gidan nan ya tsufa, katangar kamar zata fado, shine nace ko zaki koma chan gidana na layout, tayi saurin katse shi "kai tsaya, ni da gidan nan mutu ka raba, shekaru sama da 30 ina zaune da yan unguwan nan lami lafia, kawai sai kace na tashi? Too don naki Garin Gwamna (Kaduna) shine kazo da wannan salon? Toh ba zan tashi ba, ina nan ni da gidan nan mutu ka raba, idan katangar ya tashi fadowa ya fado kaina, kaga nayi mutuwar shahada kenan". Abba ya ja numfashi ya san a rina. Ya sadda kansa kasa yace " Nene, ba wai gaba ki daya za ki koma chan ba, gyara zaayi, idan an gama daga katangar sai ki dawo, tace kai yaro ni zaka yi wa wayau? Ko da nake kauye ba a riga na zauna ba, ka fita idona. Abba ya girgiza kansa ya ciro waya ya kira yayar sa Fatiti, ringing biyu ta dauka, ya mata bayanin kudirinsa kan Nene, tayi na'am da maganar, ya mik'a mata wayar itama tayi tayi amma Nene tace aa. Ummi ma ta sa baki, Sai da aka kai ruwa rana kafin ta yarda, tace ni abunda ke batan rai shine unguwar nan shiru kamar ta mayyu baka ganin kowa awaje don bakin hali. Daga Abban har Ummin ba su tanka ba don kar ta chanza raayinta. A ranan Abba ya kira masu mota suka kwashe kayan Nene na bukata suka kai Gidan layout, A rannan Nene batayi kwanan Kofa Ukku ba".

Abba ke raka Nasiba Registeration. A gurin reg. Ne ta hadu da Ushee da Miemee. Hussaina Umar(Ushee) Aisha Saliz (Miemee) kawayen juna ne, tun JS1 suke tare, Ushee da Miemee suna da kirki sosai, suna son junan su, Miemee ta fiye surutu da kaudi, Ushee kam akwai jan mutane a jiki.
Wurin signing course form suka hadu, Inda Nasiba ta tambayi Miemee da ke bayanta a layi Biro, tace "donAllah ara min biro na rubuta mat.no dina nawa ya tsaya, Miemee da murmushin ta ta ciro ta bata, Miemee na son kyawawa, tace keme MCB kike? Tace "eh" Sunana Miemee, wannan kawata ce Ushee" Seebi tayi murmushi ta mika musu hannu sukayi musabaha tace"its nice meeting u all" nan suka dinke da labari har ya kai su da exchanging numbers, a nan ne suka gano gidan su Ushee be da nisa da gidan Nene. Haka Abotar su ta samo Asali.
Wannan Kenan..

_Bibilicious Biebee_
👧🏽KE ALHERI CE 🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

® NAGARTA WRITERS
ASSOCIATION(NWA)

Pg7⃣

"Kinsan jiya sai da nayi mafarkin Azababben Guy din nan?" Miemee ce ke maganar nan, Ushee da Seebi suka yi daria, Ushee tace ai ya hadu ne ba karya, Seebi tace ku ma kuka ga fuskar shi, ni jiyan nan ai a tsoroce nake, Miemee tayi tsaki, "ai wlh kina bada mu, kiyi ta wani nok'e nok'e kamar wacce tayi karya". Seebi tace banyi karya ba amma ai KUNYA ADON MACE (Na feedon biebee). Miemee ta kada idanuwa tace "story for the gods" Ushee tayi daria tace "ya isa, ku tashi muje Library mu fara Assignment din Wagini, Seebi tace "wallahi yunwa nakeji, daure wa kawai nayi aka gama first lecture" Ushee tace kinsan dai gobe za'ayi submitting, kuma gwara mu yi mu dawo before 12 kafin Mr Ola ya shigo, kin dai san rules dinshi ba a shiga idan ya shiga" Seebi tace "ba zaki gane yunwa Da nake ji bane, ku je ku mana Assignment din, Miemee tace "aa muje dai tare, sai mu fito mu ci abincin sha biyu saura minti talatin (11:30) Seebi tace "i can manage har time din muje".
Chapter 4 · 0% Book details